← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 27

Sashe 21

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya jinjina kanshi.
Doc Jannat ta mik'a mishi prescription ta tare da furta.

"Kafin na dawo ayi k'ok'ari a siyo wad'annan magunguna.

Nan ma sake jinjina kanshi ya yi bayan doc Jannat ta tafi, ya nufi 6angaren Jadda ya nufa zuciyarshi a cakude bayan ya gaisa da Jadda mero ta kawo mishi Karin kumallo ya d'an tsakura Kaɗan saboda damuwar da yake ciki, zance na gaskiya idan har hasashen shi ya hasaso masa gaskiya wannan tatsutsuwar yarinya da ya gani sa'ar Aneesah matashi to kuwa akwai matsala babba. Wannan ai abin kunya ne gotai-gotai dashi ya aure sa'ar 'yar cikinsa. Ai sai girma da k'imarshi su zube a idanu mutane duniya.
Wayarshi ya dauko ya kira Hakeem ya zo yana so ganinshi gara ya zo su yi ta manya-manya daga tushe, kafin Hakeem ya iso ya kalli Jadda da ke mishi zance Aslamiyya kamar tasan abin da ke nukurkusar zuciyarsa. Rai 6ace ya fara magana.

"Wai Jadda kina nufi wannan 'yar k'ank'anuwa yarinya da nagani ita ce matar tawa?"

"Kwarai kuwa ita ce ai nice nace da Hakeem ya 6oye kada ya yi saurin baiyana maka da ita gudun kada kace tayi maka k'ank'anta, ka fasa auren ni kuma a duniya nan ta maliki yaumidini bana da buri da ya wuce ka k'ara aure kai da yaranka za ku sami kyakkyawar kulawa da gantalalliyar matarka ta kasa ba ku.

Ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauke tare da shafa kwantattace sajenshi wanda hakan ya zame masa dabi'a. Kafin ya tattaro natsuwashi wuri guda ya ce.

"Jadda idan kina min hasashen kulawa to kin tafka kuskure domin wannan kwaila ba abinda za ta iya, azahirin gaskiya ni an cuceni tare da linkeni bai-bai saboda Hakeem ce min ya yi bazawara ce har da yara biyu. Ashe duk k'arya ce da yaudara saboda haka yadda yadda kawota haka zai dawo ya d'auki abarshi don ni ba mutumin banza bane balle araina min hankali"

Hakeem da ya turo k'ofa zai shigo karaf furuncin Azaad na k'arshe ya sauka a kunnenshi, cikin mutuwar jiki yai sallama Jadda ce Kaɗai ta amsa Azaad kuma ya amsa a cikin zuciyarsa. Muryar Hakeem Kaɗai da ya ji saida ya k'ara linka masa 6acin rai da takaicinsa.
Hakeem ya mik'a masa hannu da nufi su yi musabaha, ya kwada masa katuwar harara, ya kauda fuska.
Hakeem ya mak'e kafad'a tare ta6e baki ya nemi cushion dake facing ɗinshi ya zauna, ya gaida Jadda ta amsa kana ya zarce da faɗin.

"Jadda ki shiga cikin lamari nan saboda Aj ya dau zafi dani, ni kuma shawara da kika ɗorani akai na bi. Don haka kar ya sake ya ga laifina.

"Wannan haka yake Hakeem tun kafin ka zo na faɗa na Kuma k'ara jadaddawa Aslamiyya tayi min d'ari bisa d'ari....

"Haba Jadda ya za ki faɗi haka gaskiya ni dai ba ai min adalci ba?" Kuma inaso kasani Hakeem saboda yarda da nayi maka yasa na ba ka ragamar rayuwata da ta iyalina sai gashi ka rusa wannan yarda.

"Karka faɗi haka Aj domin wallahi-tallahi ban zantar da hukunci ba saida amincewar Jadda, aganina ko mayya Jadda ta nuna tanaso ka aura za ka amince da gaggawa ba tare da tambayar ba'asi ba. Balle yarinya mai cike da nagarta iri Aslamiyya wacce samun irinta a wannan zamani sai an sha matuk'ar wuya. Duk wani qualities da kakeso a jikin mace Aslamiyya tana dashi, ita ce mace da za ka faɗa ta ji, ka kafa doka ta bi ba tare da tayi fatali da ita ba. Ita ce za ta girmamaka ta mutunta igiyar aurenka ta kuma zame maka ma'adanar sirrinka, ta so ka ta k'aunace 'ya'yanka Aj kada ka bi rudin zuciya ka daure Dan Allah da manzonsa ka kar6i, Aslamiyya a matsayin matarka. Yarinya nan rayuwarta cike take da k'alubali a tunanina kaine za ka kawo mata sauyi a rayuwarta kamar yadda nake da yak'ini za ta kawo babban sauyi a rayuwar gidanka"

Azaad ya dafe kokon kanshi saboda Hakeem da Jadda sun ri ga da sun gama daure shi da kalamansu. Yana matuk'ar k'aunar Jadda domin ita Kaɗai ta rage mishi ita ce yake kallo a matsayin mahaifiyarshi yayin da Hakeem yake da babban matsayi agareshi, abokinshi ne tun na yarinta duk wata gwagwarmayar rayuwa a tare suka yi shima maraye ne kamar shi saidai Hakeem yana da K'anwa daya kachal Zainab sa6ani shi da Jadda ce Kaɗai yake da sai shirgin 'yan uba da kullum burinsu su ga bayanshi. Kasa magana ya yi hakan ya bai wa Hakeem damar zayyane masa tarihin Miyya bai 6oye masa komai ba. Sosai ya ji ya tausaya musu ya kuma kudurta aranshi zai kula da ita a matsayi 'ya ba mata ba, har sai zuwa lokaci da za ta mallaki hankalin kanta ta yadda za ta iya 6ance-6ance tsakani abin da takeso da wanda bataso.
Ya yi shiru bai sake magana ba sai ma jinginar da gadon bayanshi ya yi a jikinta ya lumshe idanuwanshi gani haka yasa Hakeem ya yi hamdallah domin shiru da ya yi shine amincewarsa da bai amince ba tashi kawai zai yi ya bar musu falon.
**** ****** *****
Miyya tana rik'e da hannu Ahlam ko nan da can bata gusa ba, yanzu haka fitsari take ji amma ba za ta iya shiga bathroom ta barta Kaɗai ba.
Sai da drip ya k'ara ta fita kiran Nanny Lacey ta zo ta cire mata sai lokaci ta faɗa bathroom ta rage nauyi tare da d'aura alwala saboda lokaci sallar Azhar ya yi har kuma zuwa lokaci Ahlam tana sharar barci abinta.
Hatta da abinci Nanny Lacey ce ta kawowa Miyya a d'aki sai misali k'arfe uku Aneesah da Airah suka dawo daga school, sai lokaci su ka san Daddynsu ya dawo sosai suka shiga murna ganinshi.
Yini daya kacal har Ahlam tayi rama tun tana mamaki rashin dawowar Azaad ya duba Ahlam har ta dawo tana zance zuci.

"Wannan wane irin uba ne?" Fissibillahi 'yarka bata da lafiya ka kasa nuna kulawarka akai.

Wani 6angare na zuciyarta ya ce.

"Daina ganin laifinsa Miyya mahaifiyarta ta fi shi laifi kasancewar mace Kuma uwa amma ta iya tsallakewa uwar duniya ta bar 'yarta mai watani goma.

Abin da ke d'aure mata Kai ya Kuma k'ara dumulmula mata tunani tare da hargitsa mata kwakwalwa, bai wuce tun zuwanta gida dai-dai da rana d'aya bata ta6a gani Madam Salima ta kira waya domin ta ji lafiyar yaranta. Dama Azaad kafin ya dawo kusan kullum sai yai waya dasu which means Azaad ya fi damu dasu fiyye da Madam Salima. Idan kuwa hasashenta ya kasance gaskiya tabbas Madam Salima batasan ciwon kanta ba, ta kuma san darajar 'ya'ya ba.
Ta 6angaren Azaad Junaid yana damu sosai da son sani hali da Ahlam take ciki, ya tambayi Nanny Lacey ya kai sau uku ya jikinta sai ta ce dashi tana barci duk da haka hankalinshi bai kwanta ba, yana so ya je d'akinta ya gannta sai kuma ya tuna da Miyya tana d'akin baya so duk wani abu da zai danganta shi da ita. Gudun kada ta rena shi. misali k'arfe biyar na yamma ya Kira Doc Jannat ta zo ta k'ara duba Ahlam ta ji sauk'i sai da zafin jikinta da har yanzu bai rage ba. Amma ta daina amai duk da haka sai ta sake sa mata wani drip.
Gani yadda Ahlam ta jigata ya k'ara linka masa haushi da tsanar Madam Salima, ya kuma jefa shi cikin nadama haɗi da danasani aurenta.
Misali karfe 8:30pm ya 6aro flat ɗin Jadda ya kira Nanny Lacey ta kawo mishi Ahlam ya gannta yana part ɗinshi.
Koda Nanny Lacey ta shigo d'akin Miyya har tayi shirin kwanciya barci saboda throughout bata huta ba tana ta fama da Ahlam.

"Pretty har kin kwanta ne?"

Cewar Nanny Lacey lokaci da takai dubata wurin da Miyya take kwance sanye da sleeping gown yayin da Ahlam take kwance akan cikinta, sai da tayi k'ok'ari tashi zaune kana ta amsa da cewa.

"Eh! Nanny nagaji ne sosai ga Kuma barci da nake ji.

"Ayya sannu pretty ai kina k'ok'ari sosai ba Kaɗan ba, dama Yalla6ai ne ya ce akawo mishi Ahlam ya gannta"

Jin abin da ta faɗa yasa Miyya ta6e baki wato sai yanzu ya yi lokaci Ahlam ɗin, fuskarta babu wal-wala ta shiga k'ok'arin mik'awa Nanny Lacey Ahlam, yayin da Ahlam ta fasa ihu da sauri Miyya ta dawo da ita jikinta ta rungumeta tana shafar gadon bayanta.

"Nanny ki faɗa mishi wallahi yau gaba ɗaya yarinya nan k'iyya take ji bata yarda da kowa ai dai kin ga yadda nake fama da ita ko bathroom ban isa na shiga na barta ba.

"Nasani pretty daurewa za ki yi ki kai mishi ita tun da ni bata yarda dani.

Da sauri Miyya ta kalli Nanny Lacey fuskarta cike da zallan mamakin furuncinta.........

*Not Edited!!*

*AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004

18....

Cikin tsananin fusata Hasheem ya cakume collar rigar king Kevin yana k'ok'ari kai masa nushi gani haka yasa Tajo ya taso da sauri ya rik'e masa hannu domin ya tabbata idan har ya kuskura hannunshi ya sauka a jikin KK tabbas da wuya ya kai gobe.
Yayin da KK yake kallonshi hankali kwance jira yake yi ya aikata abin da yake nufin aikatawa ya tashi kokon kanshi da alburushi.
Tajo ya ja shi gefe yana bashi baki da kyar ya shawo kanshi ya k'ara musu two days idan har kwana biyu ya cika basu kashe masa Azaad Junaid ba, dole su dawo masa da kud'insa.
Wanda daga Tajo har KK suke gani ba abu mai yuwa bane dawo da kud'i koda kuwa ba su sami nasarar cimma manufarsu ba.
6ata musu lokaci da baro garinsu da suka yi ba za su yi shi a banza ba. Idan har Hasheem ya kafe lallai sai sun dawo mishi kud'insa to kuwa haka yana nufin numfashinsa za bar gangar jikinsa.
***** **** *****

"Ya naga kin 6ata rai?"
Chapter 21 · 0% Book details