← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 27

Sashe 25

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Karka yi haka kk ka dawo min da kudina tun da kun kasa aiwatar da contract ɗin, na k'ara muku two days nan ma kun kasa komai kuma a gabanku Azaad Junaid zai wuce ba ku yi masa komai ba. Ko jiya ina la6e ina kallonku naga lokaci da ya fito daga gidanshi ya wuce ku amma ba ku yi masa komai ba. Hakan ke nuni da cewa ba za ku iya ba.....

"Rufemin baki kafin na sauke dukkan fushina akanka Hasheem. Kana tsanmani kisan Azaad Junaid sauk'i ne dashi?" Kaine kake yi wa Azaad kallon sakarai amma shi yasan abin da ya taka. Shu'umancinsa ya zarce naka, zai fi maka alkhairi da ka hak'ura da son ganin bayansa. A cikin kwanaki biyu da ka k'ara mana kasan irin bala'o'in da muka dinga cin karo dasu a duk lokaci da muka yi yunk'uri sheke shi?" Jiya har dare muna la6e a jikin katangar kamfaninsa, a maimakon na kashe shi ni ne na kusa mutuwa saboda haka ka nemo wani yai maka wannan aiki, Amma inaso kasani
duk yadda kake tunani Azaad Junaid ya zarcewa tunaninka. Kud'inka kuma k'arfi yaci idan ka matsa sai na dawo dasu to kasani komai zai iya faruwa daga ciki har da rasa rayuwarka. Saboda haka ka za6a ranka ko kud'inka?"

"Ba zai yu ba kk kud'inan su na da yawa fa.....

Kafin ya k'arasa magana kk ya buge tsakiyar kanshi da bindigar hannunshi, zafi da radadin azaba suka ratsa kwakwalwar Hasheem ya kurma ihun neman taimako tare da sulelewa k'asa yana dafe da fasashe kanshi da ke zubda jini, duk da haka kk bai kyaleshi ba saida ya har6eshi a k'afarshi ta dama yana k'ok'ari sake saki mashi wani harsashe a k'irji Tajo ya dakatar dashi ta hanyar jan shi da k'arfi suka fice daga falon. Kasancewar a gidan gona suke, gate yana da nisa da inda suke shiyasa duk ihu da kururuwar da Hasheem ke yi maigadi bai ji ba.
Har jini ya buge shi ya some.
***** **** ******
A hankali take saukowa daga matattak'alar jirgi yayin da k'awarta Hafsat Shinkafi ke biye da ita kamar jela. Tun kafin su k'araso direbanta mr Michael ya buɗe musu k'ofufin mota duk lokaci da tai tafiya Mr Michael ne Kaɗai ke sani dawowarta.
Duk gaisuwa da yake mata ko kallo bai isheta ba, sai Hajiya Hafsat ce ta amsa mishi. Sai da suka fara sauke Hafsat Shinkafi gidanta koda ta iso gidanta ana kiran sallar magarib.

Cike da izza ta fito daga mota da azama mr Michael ya nufi k'ofar main parlor ya buɗe mata, jin k'arar takon takalminta ya sanya Nanny Lacey ɗagowa daga tattara toys ɗin da Ahlam da ta gama wasa dasu, gabanta ya yi mummunan faɗuwa sakamakon gani madam Salima. Jikinta na rawa ta gaidata tsabar girman kanta da izzarta basu bari ta amsa ba sai yatsunta guda biyu ta ɗagawa Nanny Lacey, ta haura staircase ta nufi 6angarenta.
Nanny ta bi ta da kallo inda sabo ta saba da ɗagawa da izzar madam Salima.

Yanzu duk tsawon shekaru da ta d'auka tana mata hidima da yaranta ace bata kallonta da gashin arziki, kusan watani biyu har da sati uku kenan da tayi tafiya ko a waya bata ta6a kiranta ta ji lafiyar yaranta ba.
Hakazalika ta dawo ko ba za ta tayi lafiyarta ai ta tambaye na yaranta.
Shigowar mr Michael janye da luggage ɗinta ya katsewa Nanny zance zuci da take. Ta kar6i trolley ɗin daga hannunshi ta kai mata d'akinta koda ta shigo tana cire kayan jikinta a hankali ta ajiye mata luggage ɗin har Nanny ta buɗe k'ofa za ta fita ta ji ta kira sunanta.

"Nanny!

"Yes madam!

"Ki sanarda Azaad na dawo amma karki faɗawa yara ki bari sai zuwa gobe, saboda ina da buk'atar cikakken hutu.

Tsabar takaicinta da ya lullu6e Nanny Lacey kasa magana tayi sai jinjina kanta tayi, har ta koma d'akinta tana yaba rashin k'awa zuci irin na madam Salima.
Miyya ta fito daga wanka a gaugauce ta tsane raguwar ruwan jikinta ta zura doguwar riga da hijab tayi sallar magarib bata tashi ba har saida tayi sallar isha.

Samun kanta tayi da yi simple makeup ta sanya wide legs trouser haɗi da pink bias top ta yane kanta da scarf jikinta na fitarda sanyayye kamshi.
D'akin Aneesah ta shiga domin ta k'ara mata haske akan assignment ɗin da aka basu bayan su kammala assignment ɗin.
Su kayi dinner sannan ta dawo d'akinta.

Nanny Lacey na cikin goge dining table Azaad ya shigo cikin girmamawa suka gaisa, kana ta sanarda shi madam ta dawo nan take annurin kan fuskarshi ya d'auke cakk... kamar an yi ruwan sama an dauke, ita kanta Nanny ta lura da sauyawa tashi faratt d'aya. Bai ce da ita uffan ba ya nufi 6angarenshi.

Har Miyya ta kwanta ta tuna da bata bai wa Daddy abinci ba ta tashi zubur, ta d'auki scarf ɗinta da ta cire ta fito downstairs parlor. Ta nemi cushion ta zauna tana jiran fitowarshi har 11:00pm ta buga bai fito ba. Batasan cewa yau a 6angaren Jadda ya yi dinner ba. Da taga ji da zama sai kawai ta yanke shawara ta kai mishi coffee.
Tana sanda kamar 6arauniya haka take tattaka matattak'alar bene da zai sadata da 6angarenshi, tana zuwa k'ofar falo bata tsaya neman izzini ba ta buɗe ta shiga kanta tsaye ta wuce falonshi na biyu.

Yana zaune da system a gabanshi yana gudanar da online meeting, sallamarta ce tasa shi ɗagowa, har ta k'araso inda yake zaune bai d'auke idanuwanshi daga kanta ba. A k'asan zuciyarshi yake yaba tsin-tsan kyau da tayi a cikin kwanaki nan completely ta sauya wa sanin da ya yi mata, gashi ta hanawa zuciya da gangar jikinsa natsuwa bashida aiki sai na tunaninta, idan har bai yi da gaske ba yarinya k'arama za ta zauta shi saboda haka zai taka mata birki, kada ta kai shi da aikata abin kunya.
Ta sauke tray hannunta akan center table cikin sanyayya murya ta ce.

"Daddy yau lafiya ba ka fito dinner ba?"

Ya kalleta cikin d'aure fuska gudun kada taga damarshi, ya ce.

"Naci a 6angaren Jadda.

"Iyeee....ashe yau Daddy dad'i kaci.

Ta faɗa tana dariya mai ban sha'awa......

*AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004

22....

Baisan lokaci ya da ya saki mata murmushi ba, a k'asan zuciyarshi so yake ya taka mata birki ta daina shigowa mishi part amma ya kasa furta mata sai kawai ya tsincin kanshi da faɗin.

"Kema za ki iya zuwa ki ci dad'in.

Ya k'arasa magana yana zuba mata idanuwanshi, masu rikita ta a duk lokaci da ya kalleta dasu.
Ta rausayar da kai tana ci gaba da murmusawa cikin sigar shagwa6ar da murya ta ce.

"Ba wani nan Daddy da kaso naci dad'in da ka zo min da nawa ko kuma lokaci da za ka je 6angarenta da ka aiko min da katin gayyata"

Yadda take magana tai masifar tafiya da ruhi da gangar jikinsa, ya gama fahimta muddin bai da gaske ba tsaf k'aramar yarinya nan za ta zuzuta shi a hankali ya ɗago idanuwashi ya sauke su akan fuskarta wacce ke ta glowing cikin haske bulb ya saki murmushi tare da furta.

"Wai ke bakya ji barci ne?"

"Uhm..bana ji"

Ta faɗa tana turo d'an k'aramin bakinta, hakan ya k'ara kunna wutar abin da yake ji akanta da sauri ya kauda fuskarshi yayin da gabanshi ke wani iri bugawa da k'arfi. Ya sauke numfashi kana ya nuna cushion ɗin da ke facing ɗinshi da hannunshi batare da ya yi magana ba. Da kanta ta fahimci abin da yake nufi cikin salon tafiyarta mai jan hankali ta nufi kujerar ta zauna, ta ɗago idanuwanta suka sark'e da nashi bugun zuciyarsu ya tsananta. Tai sauri runtse idanuwanta tana jan wahalallen numfashi.
Ta sadda kanta k'asa.
Shiru ya biyo baya shi bai tanka ta ita kuma bata sake yi magana ba ko wane su yana faman da bugun zuciya, Azaad ya kasa samun wadatatciyar natsuwa da zai ci gaba da gudanar da meeting ɗinshi lokaci zuwa lokaci take ɗagowa ta saci kallonshi kuma duk sanda ta ɗago idanuwashi na kafe akanta tamkar yana karanta wani abu, akanta ne.
Rashin natsuwa da yake ji yasa sai faman shafar sajenshi yake yi can kuma cikin rikitatciyar murya ya ce.

"Pretty ki je ki kwanta please kinsan gobe kina da school ko kinaso ki yi latti tashi ne?"

Kamar jira take yi ya bata umarnin tashi ta mik'e zubur ta nufi k'ofar fita saida ta rik'e handle ta juya tare da faɗin.

"Goodnight Daddy!

"Goodnight"

Ya faɗa kamar mai ciwo hak'ora. Ta k'arasa ficewa kamar yadda ta shiga part ɗin nashi cikin sand'a haka ta fito tana sand'a tana isa k'ofar d'akinta tai wuff....ta shige tare da rufu k'ofa. A tsorace take gudun kada tsautsayi ya gitta Aneesah ko Airah wani daga cikinsu ya gannta ta fito part ɗin Daddynsu, dole su tambaye me ta je yi a halin yanzu batasan amsar da za ta basu wacce za ta zama kariya agareta.
Da wuri Miyya ta tashi kamar yadda ta saba ta shirya cikin school uniform ɗinta sosai uniform ɗin suka k'ara fidda kyawonta.
Side by side suke tafiya ita da Aneesah zuwa parking lot kasancewar Airah tariga su fita tuni take zaune a mota tana zaman jiransu sai faman zabga tsaki da duba agogo take yi, saboda tana da presentation gashi suna so 6ata mata lokaci.
Chapter 25 · 0% Book details