← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 27

Sashe 18

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka Airah bata sake magana ba sai kawai ta bi umarninta.
A kwana a tashi lokaci yana ta tafiya Miyya har tayi cika two weeks a gidan, sosai shak'uwa da k'auna mai k'arfi ta shiga tsakaninta da Airah da Ahlam har ta kai a yanzu a d'akinta suke kwana.
A koda yaushe idan taga Nanny Lacey a kitchen ta kan je ta tayata girki, sosai ta sami kar6uwa a wajen housemaids ɗin gida kowa k'aunarta yake yi saboda Miyya mutum ce mai saurin shiga rai. A two weeks da tayi da yana yi mu'amalarta da mutane gidan za ka zaci ta shekara da saninsu.
Miyya tana da hak'uri uwa-uba sanyi hali gata shiru-shiru magana ma wahala take mata ga yawan murmushi saidai akwai saurin yin kuka.
Rashin kulata da Aneesah ke yi ba k'aramin damunta yake yi ba. Har cikin ranta take ji k'aunarta shiyasa a duk lokaci da ta ga Aneesah ta sauk'o k'asa sai ta gaidata, burinta su sami kyakkyawar mu'amala.
Tun Aneesah bata amsawa har ta zo yanzu tana amsawa saidai a gajarce.
Yau ma dukansu suna zaune a downstairs parlor, suna cin pancake da Miyya tai musu Aneesah ta sauk'o cike da yanga wacce ta zame mata jiki ta kalle su ta d'auke kai, ta nemi kujera da ke nesa dasu ta zauna tare da crossing legs ɗinta.
Miyya ta dubeta tana murmushi ta ce.

"Barka da fitowa Aneey"

Sai da ta yatsine fuska tukun kafin ta amsa da

"Sannu!

Miyya ta d'auki plate ta zuba mata pancake ta sauke Ahlam daga jikinta, ta nufi wajenta ta mik'a mata.

"Aneey ga pancake nai mana ci ki ji ko ya yi dad'i?"

Ta faɗa da yalwatattace murmushi akan innocent face ɗinta, shiru Aneesah tayi tana tattance irin kalar wulak'anci da za ta yi mata. Sai kawai ta buge plate ya faɗi pancake ɗin ya zube akan tiles, cikin tsawa ta ce.

"How dare you to bring me this trash ban faɗa miki ba ki daina shiga harkana ba?" Ko dole ne sai na kula ki what kind heartless you're?"

Tuni idanuwan Miyya suka kawo ruwa sai k'ok'ari hana su zubowa take yi, Airah ta taso cikin fushi ba k'aramin haushi take ji ba a duk lokaci da Aneesah ta yiwa Miyya wulak'anci.

"Wai miye haka ne Aneey ke ko Kaɗan ba a miki abin kirki ne sai kin ma mutum wulak'anci, wallahi da nice pretty da tuni na tattara ki na zubar a bola.

A fusace Aneesah ta mik'e ta nuna Airah da yatsa tana faɗi

"Hey...watch your tongue

"An k'i ɗin sai ki zo ki dakeni.

Airah ta faɗa tana galla mata harara. Sosai hakan ya k'ara harzuk'ata ta soma zazzaga masifa.

"Tuni nagano Airah kin fiso stranger akan ni 'yar uwarki ta jini, kwatata kin daina kulani saboda ita amma ba komai ki jira mommy ta dawo wallahi sai tabar gidanan.
Ta k'arasa magana muryarta yana rawa kamar za ta fashe da kuka.

"Tun kafin mommy ta dawo ki zo ki fitar da ita ai kema kin isa ko?"

Airah ta faɗa a fusace kuma cikin shouting. Da sauri Miyya ta jawo hannunta.

"Miye haka Airah yayarki ce fa?" Bai dai-dai bane ki faɗa mata irin wannan magana.

Kafin Airah tai magana Aneesah ta rigata ta hanyar furta.

"Ba wani nan duk ke ce kika janyo kafin zuwanki gidanan Airah bata isa na faɗa ta faɗa ba, saboda haka dole ki bar gidanan.

"Ba isa ki ba wallahi Aneey you're not a Daddy saboda shi keda iko zantarda hukunci Kuma shine silar zuwanta gidanan.

Ita ma Airah ta faɗa a fusace.

"Airah please ya isa haka tun farko laifina ne da na kasa daina shiga sabgarta.

Miyya ta faɗa cikin sanyi murya kana ta kalli Aneesah ta haɗe hannuwanta alamar rok'o.

"Ki yi hak'uri Aneey tun da bakyaso ba zan k'ara ba kinji?"

"Haba pretty miye na bata hak'uri ita ya dace ta ba ki hak'uri ba ke ki ba.

Airah tayi magana cike da jin haushi hak'uri da Miyya take bata.

"A'a Airah laifina ne dole na bata hak'uri. Ina k'ara ba ki hak'uri Aneey.

"Go to hell!!!

Aneesah ta faɗa cikin ihu wanda ya janyo hankali Nanny Lacey ta fito da gudu daga d'akinta, tana tambayar meke faruwa. Aneesah bata bi ta kanta ba ranta a mugun 6ace ta juya da gudu ta haura staircase ta shige d'akinta.
Airah ce tai mata bayani Miyya kuma ta duk'a ta shiga tsince pancake ɗin da Aneesah ta zubar. Hak'uri Nanny Lacey ta bata.

"Its ok Nanny.

Ta faɗa a gajarce tare da nufar kitchen ta kai plate, za ta fito dai-dai Airah ta shigo tana zuwa ta rungumeta cikin taushin murya ta ce.

"I'm sorry pretty karki damu da abin da Aneesah take miki, bata da halin kirki she's very bad girl...

Da sauri Miyya tasaki wa Airah duddu a gadon bayanta tare da faɗin.

"Za mu 6ata Airah idan kina faɗawa yayarki kalaman rashin ɗa'a.

"Ouchh.... pretty da zafi fa.

Ta faɗa cikin shagwa6a tana shafa gun da Miyya da buga.

"Sorry....

Cewar Miyya tana dariya kana suka fito daga kitchen ɗin, Airah ta kalli Miyya with serious face ta ce.

"Ni fa pretty na ganoki kin fi so wannan arrogant Aneey akaina"

Murmushi kawai Miyya tayi ta d'an ture Airah, ta wuce d'akinta.
Miyya bata daddara ba da yamma ta ga Aneesah bata fito ba sai kawai ta sulelewa Airah ta nufi d'akinta, sai tayi niyyar knocking sai kuma ta fasa tayi haka kusan sau uku sai a na huɗu tayi knocking on.

"Yes come in the door is open"

Ta tsikayo muryar Aneesah daga ciki, ta danne zuciyarta ta tura k'ofa wannan shine karo na farko da ta fara shiga d'akinta. Tana bibiyar Aneesah ne saboda ta fahimci saboda su Azaad Junaid ya aure ta. Don haka ta k'udurta aranta za ta yi hak'uri ta bi ko wace hanya da za su sami jituwa a tsakaninsu.

"Assalamu Alaikum!

Da sauri Aneesah ta ɗago idanuwanta taga game ɗin da take yi a wayarta, fuskarta ta kasa 6oye mamaki gani Miyya a d'akinta nan take ta daure fuska.

"Aneey cewa nayi amincin Allah ya tabbata agareki amma kuma kin kauda fuska addini musulunci babu kyau ai ma mutum sallama ya kasa amsawa"

Miyya ta faɗa cikin tattausan lafazi jikin Aneesah ya yi sanyi ta juyo amma bata bari ta had'a ido da miyya ba ta ce

"Wa'alaikum salaam! Shikenan ko?"

Ta faɗa tana yatsine fuska.

"Dama na zo ne na duba ki naga tun safe ba ki k'ara saukowa falon k'asa ba?"

Shiru Aneesah tayi tana k'ara mamakin Miyya wacce irin zuciya ce a k'irjinta da take jure wulak'anci.

"Aneey kin yi shiru ba ki ce komai ba, Ko dai har yanzu fushi kike yi dani?"

"Bana fushi da mutane da basu da muhimmanci a gareni.

Yadda tai magana bai ma Miyya dad'i ba don har hakan ya nuna akan fuskarta, amma sai ta daure ta sake cewa.

"Na sani Aneey banida muhimmanci agareki amma ni kina da a wurina saboda muhimmancinki yasa har na dako k'afata a dakinki.

Furuncinta ba k'aramin rikita tunani Aneesah ya yi ba, duk ta ji wani iri sai ta hana hakan tasiri akanta cikin muryar reni hankali da gatsali ta ce.

"To naji za ki iya tafiya Ina buk'ata huta banaso damuwa.

Ta k'arashe magana haɗi da pointing k'ofar fita da yatsanta, jikin a sanyyaye Miyya ta buɗe k'ofa ta fito karaf idanuwanta suka faɗa cikin na Airah da ke tsaye tayi folding hannuwanta a k'irji tana facing k'ofa. Ta ɗage girar ido tana kallonta kafin ta girgiza, ta ra6a ta gefenta ta shiga d'akin na Aneesah, jin k'arar buɗe k'ofa yasa Aneesah ta taso a fusace a tunanina ko Miyya ce ta sake dawowa sai idanuwanta suka sark'e da na Airah, ta galla mata harara kana ta koma ta kwanta ta bata baya. Airah tayi murmushi tare da zaunawa kusa da kafafuwanta cikin tattausa murya ta ce.

"Aneey please wake up we have to talks.

"About what??"

Ta tambaye ta batare da tashi ba, balle ta kalleta.

"Pretty!

Airah ta faɗa a gajarce.
Sai da Aneesah ta 6ata lokaci kafin ta tashi zaune tana mai k'ara tanke fuskarta.

"Aneey zuwan pretty gidanan ta miki wani laifi ne da yasa kika tsane ta har haka?"

"Banaso silly questions Airah.

"Babu zance silly questions Aneey abin da kike yi kwatata bai dace ba, nasani haka kawai kika tsaneta alhali bata miki laifin komai ba.

"Ni nace dake na tsaneta?"

"Ba sai kin faɗa min ba Aneey ga alamomi nan a bayane, ko magana tai miki a lalace kike amsawa Ina laifin wanda ya damu da kai.

"Wai ke Airah meke damunki ne huh?" zuwan wannan Miyya gaba daya kin canza, ba ki da zance sai nata wato ta zo ban bata fuska ba shine ta turo ki, da yake bakida kunya shine za ki zo ki cika min kunne Dan Allah tashi ki fita min daga d'aki banaso tak'ura.

Haushinta ne ya turnuk'e Airah ta juya a fusace ta buɗe k'ofa da k'arfi, ta fita. A falon k'asa ta tararda da Miyya tana zaune Ahlam tana kwance akan cinyoyinta taso tai mata korafi akan zuwanta d'akin Aneesah sai kuma ta fasa, ta kalleta a natse ta ce.

" Pretty ko za ki tashi mu tafi flat ɗin Jadda kwana biyu ba mu lek'a ta ba.?"
Chapter 18 · 0% Book details