← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 27

Sashe 24

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa furtawa Nanny uffan tayi cikin yana yi na takaici ta juya ta buɗe k'ofa ta fita, zuciyarta tana wani iri tuk'uk'i duk k'ok'arinta na ta hanawa kanta zubda hawaye hakan bai samu ba sai da zafafan hawaye suka wanke kuncinta. Kitchen ta wuce tana haɗa mishi coffee tana shar6a hawaye ko Kaɗan bata k'aunar abin da zai haɗata da Azaad domin ita Kaɗai tasan hali da take shiga a duk lokaci tayi arba dashi. Ta kammala haɗa coffee ta daura mug ɗin aKan k'aramin tray, cikin tsoro take taka matattak'alar benen da zai sada ta da 6angarenshi da ta iso k'ofar falonshi na farko zuciya ta k'ara sautin bugawa fiyye da farko tahowarta, sai ta kai hannunta za ta turo k'ofa sai ta janye, da kyar ta rinjaye zuciyarta ta turo k'ofar ta wangale bugun zuciyarta ya k'ara tsananta cikin tako d'addaya ta fara takawa zuwa cikin ainihin falon. Bata tararda shi cikin falon ba hakan yasa ta sauke k'arfaffiyar ajiyar zuciya, ta dire tray ɗin kan center table ɗin da tagani a tsikyar falon. Ta juya abinta har ta rik'e handle ta tuna da Nanny ta ce da ita ba a falon farko za ta kai ba a falonshi na biyu ji tayi kamar ta ɗora hannu akai ta kurma ihu. Dawowa tayi dole ta sunkuce tray, ta nufi k'ofar glass ta tura batare da ta tsaya shawara ba kamar yadda tayi a farkon shigowarta, Yadda ya ɗago da sauri kalleta yasa ta daskare a tsaye ita bata k'arasa ba bata kuma koma inda tafito ba.
Mamaki ganinta yake a dai-dai wannan lokaci a kuma falonshi da ko yaranshi basu ta6a shigar shi ba. Iyakacinsu su tsaya a falonshi na farko.
Siririyar sallamarta ce ta katse mishi mamakin da yake.
Ya amsa mata cikin taushin murya, sadda kai k'asa tayi ta kasa k'arasawa duk da ya amsa mata sallama.
Ya maida ganinshi akan screen ɗin laptop da ke gabanshi, shiru-shiru bai ji ta k'araso ba ya ɗago kanshi ya ganta tsaye kamar an dasa ta ya kira ta ta hanyar ɗaga mata yatsanshi.
Tafiya take ta doshi wajenshi yayin da kafafuwanta ke neman hard'ewa waje guda. Da taimakon Allah ta iso gabanshi.
k'aramin center table ɗin da ke girke a gabanshi, ta ture tulin files ɗin da ta gani a gefe kana ta aje tray ɗin. Cikin sanyi murya ta ce.

"Barka da hutawa Daddy"

A natse ya ɗago idanuwanshi ya sauke su akan kyakkyawar fuskarta, sunan da ta kira shi dashi ne ya ji shi wani iri duk da ba yau ne karo na farko da aka kira shi sunan ba. Ya d'an waro idanu waje tare da shafo sajenshi.

"Yauwa Sannu"

Ya faɗa cikin izza da k'asaita.

"Nanny ce ta ce na kawo maka coffee"

"Uhmm... thanks!

Ya faɗa a takaice yadda yake furta magana cikin izza da k'asaita yai masifar burgeta, har batasan lokaci da murmushi ya subuce mata ba.
Har ta kai k'ofar fita ta waiwaya ta kalleshi sai kawai ta tsinci kanta da faɗar.

"Daddy iya coffee kake buk'ata Koda akwai wani abu da za ai maka?"

Jin muryarta ya sanya shi sake ɗagowa ya cire medical eyes glass, dake lullu6e da kwayar idanunshi hakan ya bashi damar k'are mata kallo from head to toe, ya lefe jikin resting chair da yake zaune tare da lumsashe idanuwanshi. Sai kawai Miyya ta harde hannuwanta a k'irjinta itama ta shiga kare mishi kallo, tana yaba kyawon halittarshi ganinshi take tamkar saurayi d'an shekara 25 idan ba farin sani kai mishi ba. Ba za ka ce shine ya haifi su Aneesah ba. Duk yadda taso ta dauke idanuwanta daga kanshi kafin ya buɗe nashi idanu hakan ya ga-gareta yana ɗago idanuwanshi shima samun kanshi ya yi da kallon cikin idanuwanta, take wani maganadisu ya tsarga musu a jiki tamkar an jona musu wutar lantarki, da sauri ta runtse idanuwanta da baya-baya ta isa ga bango falon ta jinginar da bayanta gudu kada ta faɗi. Wannan shine karo na farko da ta ta6a samun kanta cikin yanayi irin wannan.

"Daddy in tafi?"

Ta tambaye shi cikin lafazinta mai kama da na mai koyon magana.
Samun kanshi ya yi da girgiza mata kai, a hankali ta baro jikin bango ta tunk'aro shi duk takonta d'aya sai ya ji faɗuwar gaba wanda ya rasa na menene.
Ta kalleshi tana murmushi wanda ya k'ara jefashi cikin rud'ani.

"Daddy me kake so ai maka ne?"

Shiru kawai ya yi yana aikin kallonta turo d'an k'aramin bakinta, tayi wanda bata masan tayi ba muryarta cike da shagwa6a ta ce.

"Daddy kayi magana mana"

Sauri Kiriss numfashi Azaad ya fita daga gangar jikinsa da kyar ya iya dai-daita natsuwarsa, ya zuba mata idanuwanshi wanda suka soma sauya launi.

"Za ki iya gyara min gado?"

Ya faɗa cikin taushin murya.

"Zan iya mana"

Tayi magana tana k'ara k'awata fuskarta da yalwatatce murmushi, da hannunshi ya nuna mata Master bedroom ɗinshi wanda tsawon rayuwarshi madam Salima ce Kaɗai ke shigarshi sai kuma yau da shi da kanshi ya lamuncewa yarinyar da ya yi kirari da ba abin da zai yi da ita.
D'akin ta nufa tana wani iri cat walks wanda za ka zaci da gangan take yi shi, alhali kuwa halitta ta ce a haka. Bai d'auke idanuwanshi daga kanta ba har saida ta shige d'akin ya daina ganinta kana ya yi ajiyar zuciya.
Tana shigar bedroom ɗin ta ja tayi tsaye tana kallon haɗuwa da tsarin d'akin nashi ba k'aramin burgeta d'akin ya yi ba.
Komai na d'akin very neat gado ba wani ya lalacewa da ya yi, sai kawai ta canza mishi bedsheet ta wanke bathroom.
Koda ta dawo falo ya mik'ar da bayanshi ga jikin resting chair, ya ɗora kafafuwanshi akan center table idanuwanshi suna rufe, saida ta kalle mishi fuska iya son ranta kafin ta dai-daita muryarta ta furta.

"Daddy na gama har bathroom na wanke maka"

"Thank you!

Ya faɗa cikin muryarshi da bata fita sosai saboda k'arfin izza da k'asaita, da kuma bakon al'amari dake yawo cikin jini da bargonsa.

"Goodnight Daddy"

"Goodnight!

Ya furta can k'asan mak'oshi still idanuwanshi a rufe, ta taka a hankali ta nufi k'ofar fita tana daff da ficewa ta waiwaya ta kalleshi idanuwanshi fess...akanta tasaki mishi murmushi mai tsayawa a rai tare da rufu k'ofar. Tana ya fita ya ja k'arfaffiyar ajiyar zuciya gaba ɗaya jikinshi ya saki kasala ta lullu6eshi. Ya kasa ci gaba da aiki da yake yi sai tsallake tulin files ya yi ko ta kanta coffee da ta kawo mishi bai bi ba, ya shige bedroom, ya tsaya tsakk.....yana kallon yadda ta gyara mishi gado karo na farko a tsawon rayuwarshi da mace ta gyara mishi gado kasancewar bai yarda housemaids su shiga mishi d'akin kwana ba.
Madam Salima kuma ko lokaci kanta bata da balle na gyara wani abu wai shi gado. Numfashi ya sake saukewa kana ya bi lafiyar gado.
Da fitar Miyya ta zarce kitchen ta dauko rubar ruwa a dalili wani irin bushewa da mak'oshinta ya yi d'akin Ahlam da yanzu ya kasance nata ta nufa gefen gado ta zauna ta sha fiyye da rabin ruwan, ta ajiye raguwar bisa bedside kana ta nemi kusa da Ahlam ta kwanta tana runtse idanuwanta kyakkyawar fuskarshi ma'abociya kyau da kwarjini ta bayyana gareta da sauri ta buɗe idanun nata duk yadda taso barci ya d'auke ta hakan ya kasa samuwa.
Ta 6angare Azaad shima hakan ce ta faru dashi sai misali karfe uku na dare barci ya d'auke shi, saidai wani abin mamaki gaba ɗaya barcin nashi ya raya shi ne cike da mafalkan Miyya, cikin tsananin firgita ya falka ya tashi zaune kana jinginar da jikinsa ga kan gado, yasa hannunshi yana shafar kwatattce sajenshi cikin yanayi na mamaki da Kuma al'ajabi yake backwards ɗin mafalkin nashi a hankali yabi jikin wando pajamas ɗin jikinsa da kallo, ba ko shakka wanka janabba ya Kama shi. Tun a farkon balagarshi rabon shi da ya yi mafalkin yana saduwa da mace sai yau ko yau ɗin da Miyya da yake yi wa kallon 'yar cikinsa. A gareshi wannan babban abin kunya ne wannan wacce irin masifa ce takeso kunnuwa rayuwarsa?"
Ya sauk'o daga gado ya shiga bathroom zuciyarsa fal.....damuwa a haka ya tsaftace jikinsa wani abin mamaki wata irin natsuwa da gansuwa yake ji tamkar a fili ne ya rage mararshi ba a mafalki ba. Yadda ya sami wannan gansuwar a mafalki a wurinta, ya tabbata a bayyane zai sami fiyye da yadda ya samu a mafalki.
Praymat ya shinfid'a ya shiga zuba nafilfili yana kai wa ubangiji mai kowa mai komai buk'atunsa.
Misali karfe 7:15am Miyya ta fito downstairs parlor sanye da school uniform, tea kawai tasha saboda daren jiya bata samu wadatatce barci ba. A dalili tunanin Azaad Junaid da ya hanata sakatt.....

*AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004

21.....

Sai kai da komo Hasheem ya ke yi ya kasa zaune ya kasa tsaye, idanuwanshi sun kad'a sun yi jajir lokaci zuwa lokaci yake fesar da zazzafar iska daga bakinsa. Can kuma ya dunk'ule hannunshi na dama ya nushi tafin hannunshi na hagu ya yi hakan yafi a kirga. Tajo ya buɗe k'ofa saida KK ya fara wucewa sannan shi kuma ya biyo shi a baya, tun kafin su k'araso tsakiyar falon Hasheem ya nufe su da gaggawa 6acin ranshi ya kai koluluwa shiyasa yana zuwa ya chafko wuyan Tajo.

"Ni za ku yaudara ni za ku cinyewa kud'i batare da kun min aiki da nasaku ba sannan har kai Tajo kake min barazana a waya?"

Kafin Tajo ya yi yunk'uri kwatar kanshi Kk ya fito da pistol daga aljihun black leather jacket ɗin jikinsa, ya nuna Hasheem da ita cikin kakkausar muryar ya ce.

"Sake shi ko na tashi kokon kanka da wannan.

Da mugun sauri Hasheem ya saki Tajo jikinsa ya shiga kakkarwa.
Chapter 24 · 0% Book details