← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 27

Sashe 22

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nanny Lacey ta faɗa tana kallon Miyya wacce fuskarta ta baiyyanar da rashin walwalarta a fili ta ce.

"Ki yi hak'uri Nanny bai kamata na shiga flat ɗinshi ba, gara na tsaya matsayina na mai kula da yaranshi"

Cikin kwantar da murya Nanny Lacey haɗi da rarrashi ta ce.

"Haba pretty miyasa za ki faɗi haka ne? Shi fa mijinki ne mallakinki idan har kika ce za ki dinga nisanta kanki dashi babu amfani auren naku kenan.

"Ba laifina bane Nanny Lacey sai nake gani kamar shi ma ya fiso hakan"

"Ba haka bane Pretty yalla6ai yana da sauk'i kai ta wani 6angare zan iya cewa yana da wuyar sha'ani. Amma ba za ki fahimce hakan ba har kin bai wa aurenku muhimmanci.

"Nanny ba za ki gane bane shi ma fa yana da manufar da yasa ya aureni"

"Ke yarinya ce k'arama pretty ba za ki yi saurin fahimtar wasu abubuwa cikin sauk'i ba. Ki sani na dauke ki tamkar jikata shiyasa nakeso ki sami rayuwa mai inganci. Rayuwar Yalla6ai Azaad tana tsanani buk'atar mai tallafa mata, Kuma kece za ki kawo wannan tallafi ki d'aure ki yi min biyayya bisa ko wane umarni da zan dinga ba ki, wallahi ba zan ta6a yi abin da zai cutarda ke ba.

Shiru Miyya tayi tana nazari maganganu Nanny Lacey d'aya bayan d'aya hakan ne ya bai wa Nanny damar ci gaba da fayyace mata, yana yi rayuwar Azaad Junaid da ta iyalinsa. Kana ta zarce da rarrashinta da kalaman kwantarda hankali da haifar da natsuwa. Sosai jikin Miyya ya yi sanyi ta tsinci kanta da tausayawa su Amrah ko Kaɗan ba ta ji tausayi Azaad ba ganinta shi ya siyawa kanshi saboda shine miji madam Salima mata duk dokar da ya kafa mata dole ta bi koda ace ranta bayaso. Nanny Lacey ta d'an buge kafad'arta ta dawo natsuwarta ta sauke ajiyar zuciya.

"Naga Ahlam ta sami barci ki kwanta kawai zan faɗa mishi kun yi barci amma dan Allah pretty da safe ki yi k'ok'ari ki kai mishi ita kinga shi ba girmanshi bane ya dinga zuwa d'aki nan ba kinji yarinyar kirki?"

Miyya ta jinjina kanta amma a k'asan zuciyarta tana ji kamar ba za ta iya ba ta amsawa Nanny Lacey ne kawai don ta shafa mata lafiya. Nanny tai mata sai da safe ta fice kana Miyya ta maida kanta bisa pillow tare da rungume Ahlam cikin jikinta daga haka barci mai dad'i ya yi awon gaba da ita. Da fitar Nanny Lacey ta kira Azaad a waya ta faɗa mishi Ahlam tayi barci, duk sai ya ji ba dad'i saboda yana so yaga yanayi jikinta tun safe rabonshi da ita ya fi tsawon minti goma yana safa da marwa daga wannan kusrwa zuwa wannan, daga k'arshe yasaka flip flops a k'afarshi ya fito cikin takonshi na k'asaita d'akin Ahlam ya nufa duk da ba shi da tabbacin ko zai tararda ita, ko Kuma k'ofar d'akin tana a buɗe. A natse ya turo k'ofar luckily ta buɗe ya yi amfani da wayarshi ya haska d'akin idanuwanshi suka hasko masa kan gado Miyya rungume tsam....da Ahlam tamkar ita ce ta haifeta bai san adadin mintocin da ya d'auka yana kallonsu cike da sha'awa wani irin girma da matsayi ya ji zuciyarshi ta bai wa Miyya ya k'arasa daff dasu ya harde hannuwanshi yana mai ci gaba da kallonsu ji yake ko zai shekara a tsaye ba zai gaji da kallonsu ba. Irin kulawar da yake so ya ga Madam Salima tana bai wa yaranshi kenan saidai kashh...Salima bata da lokacinsu business ɗinta yafi mata muhimmanci fiyye da kula da yaranta sai gashi Allah ya kawo k'aramar yarinya mai k'anana shekaru ta magance masa wannan matsalar wacce bai ta6a tsanmani magance ta cikin sauk'i ba.
Ya girgiza kanshi tare da hamdallah, kana ya fice daga d'akin yana shiga d'akinshi ya zarce bathroom ya yi alwala ya shiga zuba nafilfili tare da rokon ubangiji ya k'ara wanzar da farin ciki a rayuwarshi da ta iyalinsa.
**** ****** ******
Washe gari da wuri Miyya ta tashi kamar yadda ta sabawa kanta, ta taimakawa Nanny Lacey suka had'a breakfast bayan Aneesah da Airah sun wuce school ta dawo d'aki tayi wanka ta shirya cikin tsadaddiyar material gown irin dinki ready made wanda ake zuwa dashi daga Dubai. Yana d'aya daga cikin kayan da Hakeem ya siya mata a yanzu kan hutu ya zauna a jikinta fatar jikinta ta k'ara haske sai shek'i take.
Miyya 'yar duma-duma ce bata da tsayi sosai za a iya sakata a jerin gajeru, tana da doguwar fuska tana da hanci dai-dai gwargwado tana da yalwatatce gashin kai da na gira k'irjinta cike yake fam...ga Kuma manyan hips tubarakallah Ma-sha-Allah!
Bata cika so d'an kwali ba shiyasa ta yane kanta da k'aramin veil da ya dace da kayan jikinta tana cikin fesa turare, Ahlam ta falka daga barci ta d'auke ta nufi bathroom da ita tai mata wanka, ta shiryata cikin red gown ta d'aure mata gashinta da red band, tayi matuk'ar kyau duk da ta d'an yi rama cikin hukunci na ubangiji yau da tashi babu zazza6i a jikinta.
Ta d'auke ta suka fito downstairs parlor kaitsaye kitchen ta nufa ta tararda Nanny Lacey tana goge gas cooker yayin da Linda ke wanke plates ɗin da su Aneesah suka yi amfani dasu.
zaunar da Ahlam tayi akan kitchen cabinets saboda tasan halinta ba yarda za ta yi wani ya d'auke ta ba. Ta kammala had'a madara a fida sake daukarta tayi suka fito zuwa parlor tana cikin bata ta shak'i k'amshinsa take ta ji faɗuwar gaba haɗi da tsoro ya ratsata, batasan lokaci da tayi wata 'yar shassheka kamar mai jin sanyi. Ta ɗago idanuwanta a hankali kamar wacce aka yi wa dole karaff... idanuwanta suka sark'e da nashi yana sanye da ash colour suit ya ɗora green colour necktie ya yi mishi balthus Knott style sosai kayan suka k'ara fitowa da shahararren kyawonshi. Da sauri ta janye idanuwanta daga gareshi, saboda Sam bata iya jure kallon cikin fitinannu idanuwanshi sosai suke rud'ata tare da cika mata nata idanuwa. Ya yi kamar bai gannta ba ya nufi dining room, da sauri Nanny Lacey ta fito daga kitchen ta kalli Miyya tai k'asa da murya kamar mai rada ta ce.

"Pretty tashi ki je ki yi wa Yalla6ai Azaad serving tun da kina nan babu amfani na ci gaba da yi mishi.

Wani iri kallo Miyya take mata baki buɗe kafin ita ma cikin rad'a ta ce.

"Ni kuma Nanny haba Dan Allah miyasa kike so ki dinga jefani hurumin da ba nawa ba?"

"Saboda ke matarsa ce pretty saboda irin wannan sakaci ya jawo wa Madam Salima zuwanki gidanan, har kika kafa fada mai girma ban kuma san me zai faru anan gaba ba.

Miyya tai shiru tana wasa da fida da ke rik'e a hannunta, yayin da gabanta ke ci gaba da dukan tara-tara.

"Tashi mana kada ki 6ata masa lokaci yana da kyau ki kiyaye wannan Yalla6ai bayaso wasa da lokaci.

Batare da ta ce uffan ba ta tashi d'auke da Ahlam Nanny Lacey bata yi yunk'uri kar6a Ahlam ba, saboda tasan yana da buk'atar ganinta. Ta bi bayan Miyya da kallo tana tuna girman wannan aikin da Hakeem ya sakata tun tafiya ta yi nisa ta fara gani haske.
Cikin tafiyarta ta natsuwa mai kama da yanga ta ratso cikin dining room ɗin, hankalinshi yana kan wayarshi yana duba sak'oni{messages} sallama ta fara yi cikin sanyi murya, kafin ta gaida shi.
Can k'asan mak'oshi ya amsa mata lips ɗinshi haɗi da adams apples ɗinshi taga sun motsa ya shine ya bata tabbaci ya amsa mata.
Ya ajiye wayarshi akan dining table ya mik'o mata santala-santala hannuwanshi tuni ta gano abin da yake nufi ta matsa kusa dashi tare da mik'a masa Ahlam, wacce taso tak'i zuwa ya fizgota da k'arfi ya shiga yi mata wasa.
A fakace Miyya ta galla masa harara saboda ya bata haushi ta yadda ya fizge Ahlam ɗin. Batasan cewa duk abin da take yana ganinta ba. Haka zalika duk abin da ya faru tsakaninta da Nanny Lacey ya ji su sarai.
Ta zari plate ta zuba masa soyayar doya da haɗin source na kidney & liver ta zuba masa kunu gyada a mug. Sannan ta kar6i Ahlam har ta juya kamar daga sama taji sautin muryarshi.

"Nagode Sosai da irin kulawar da kike bai wa Ahlam idan buk'atar wani abu ta taso ki zo kaitsaye ki faɗa min.

Miyya ta ja dogon numfashi tare da saukewa abin ya zo mata wani iri tarasa amsar da za ta bashi sai kawai tayi murmushi tare da juyawa ta fice daga dining room ɗin. Cike da natsuwa ya shiga cin abincinsa har ya kammala yana jin kansa kamar ba shi ba. Ya bi ta flat ɗin Jadda ya duba lafiyarta kana ya wuce office, yana shiga office ɗinshi Hakeem na danno kai dama tun d'azu yake dakon zuwanshi, shaking hands suka yi kafin ko wane su ya nemi matsugunni.

"Ya ake ciki Aj mijin kwaila ya ka baro kwailar taka?"

Hakeem ya faɗa yana k'unshe dariyar shek'inyaci. Azaad ya bata rai cike da miskilancinsa ya ce

"Ban kira ka office ɗinan ba don ka karanta min iskaci ba. Na kira ne domin nasan menene matakin karatunta tana da buk'atar komawa makaranta, kasancewarta mai karancin shekaru bai kamata a tauye mata wannan damar ba.

Hakeem ya saki murmushi yana kallon Azaad Junaid da girar ido a ɗage, shi Kaɗai yasan abin da yake karanta akan fuskarshi kafin ya ce.

"Karatunta ya tsaya ne a matakin k'aramar sakandire {junior secondary School}

Azaad ya ta6e baki cikin izza ya ce. "Sai abu na gaba gargadi ne ina fatar za ka natsu ka bani aron hankalinka saboda banaso ace sai na sake mai-maita gargadin nawa.......

*AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004

19.....

Hakeem ya k'ure shi da kallon mamaki kafin ya ta6e baki ya ce.
Chapter 22 · 0% Book details