← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 27

Sashe 5

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita ma hannu ya ɗaga mata kamar yadda ya yi wa Nanny Lacey, kaitsaye ya wuce bedroom ɗinshi dake upstairs. Wanka ya yi ya shirya cikin dark blue ɗin jallabiya ya wuce masallaci sai da ya sallaci sallar isha sannan ya dawo gida ya shiga 6angaren Jadda koda ya mai aikinta Mero ya tarar a falo, Jadda tana bedroom ɗinta. Direct d'akin ya nufa tana zaune akan sallaya da casbi a hannunta, ya nemi gefen gadonta ya zauna. Cikin natsatsiyar muryarshi ya gaidata ta amsa mishi cikin kulawa.
Kana suka zarce da fira sai ga Mero ta shigo da k'aton tray mai d'auke da tsadaddin warmers ta sauke a gabanshi, tasake fita ta dauko mishi lemo da ruwa. Jadda da kanta tai mishi serving tuwon semovita da miyar agusi taji tantakwashi da tsokar busasshe kifi. Sosai ya ci tuwon saboda shi mutum ne mai matuk'ar son abincin mu na gargajiya sai dai kashh! Allah bai had'a shi da wacce ta iya ba. Madam Salima ko ruwan zafi na shan tea bata da lokaci dafawa. Duk wata kulawa da ya dace ta ba wa mijinta housemaids ke yi mishi ga Azaad da shegen kyamkyami. Kuma gaba d'aya 'yan aikinta Christan ne ba Musulma ko d'aya, shiyasa Azaad ya k'auracewa abincin 6angarenshi sai dai ya zo na Jadda ya cika cikinshi.
Bayan ya kammala cin tuwonshi hadda su taune k'ashi Jadda ta tsare shi da kallon tausayi, har sai yaushe Azaad zai zama cikakken mutum?"
Domin a ganinta bai cika mutum ba rabin mutum ne, tayi iya k'ok'arinta akan ya k'ara aure abin yaci turo dole tana ji tana gani ta zuba mishi ido, duk da al'amarin iyalinsa yana ci mata tuwo a kwarya kullum cikin masa addu'a take Allah ya kawo mishi sauya.

"Anya kuwa Datti wannan rayuwa da ka za6awa kanka za ta fishe ka kuwa?"

"Jadda in-sha-Allah nesa ta zo kusa domin na sanar da Salima ta ajiye aikinta....

"Dallah..! Rufe min baki sakaran banza nusari kullum cikin faɗar haka kake yi har yau ka sa aiwatar da komi. Saboda haka na ba ka nan da wata uku ko ta ajiye aikinta ta cikakkiyar matar aure ta amshi ragamar kula da gidanta hannun arna. Ko kuma ni na nemo maka wacce za ta kula min kai da yaranka"

"Ki yi hak'uri Jadda in-sha-Allahu ba ma zai kai mu da haka ba .

"Sai ta Kai mu domin ba ajiye aikinta za ta yi ba ni kuma idan har ba mutuwa tai min sauri ba sai na auro ma 'yar mutunci mai nagartattaciya tarbiyya.

"Ni dai ina k'ara ba ki hak'uri Jadda"

"Hak'urin ka na banza da wofi, ka dai ji na faɗa ma wata uku na ba ka, idan ba haka ba k'arin aure ya zame maka dole. Ba kuma shawartarka nake ba ko jin ra'ayinka.

"Jadda rigima Keɗai sam bakyaso a zauna lafiya mu ajiye wannan zance ki sha maganinki"

Ya k'arasa magana tare da dauko mata ledar maganinta da ke aje akan bedside drawer, bayan tasha magani ya shafa mata na ciwon k'afa sannan ya koma 6angareshi. Har zuwa lokaci madam Salima bata dawo gida ba, Kuma tun fitar ta da safe.
Dama haka take yi in tafita sai baba ta gani take dawowa dabi'unta sam ba su yi kama dana musu aure ba, tafi Kama da masu zaman kansu.
D'akin yara ya wuce ya tarar da Airah tana game a laptop princess Aneesa, tana aikin nata na chat ganinshi yasa ko wace ta dakatar da abin da take yi.

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.

*AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Wattpad:-jeedddahaliyu

Haske writers Association.

Top Ten Takun Haske Batch:A

Free page

4....

Zaune suke a katafare falon farmhouse da ya kasance mallakin Alhaji Yusuf Junaid su taru ne kamar yadda suka saba taruwa a can baya. Domin gudanar da secret meeting ɗinsu. su 8 ne maza 6 mata biyu kowa ne fuskarshi a turbune da ka dube su za ka hango tsananin 6aci rai da suke ciki. Hakan ya samo asali ne da har yanzu sun kasa cimma dad'en burinsu akan d'an uwansu Azaad Junaid.
D'aya daga cikinsu ne ya fara magana wanda da ganinshi yafi sauran mugunta da zafin rai, zuciyarsa na tafarfasa yace.

"Tsakani da Allah nagaji da jiran gawon shanu, zuwa yanzu yaci ace mun shafe babin Azaad a ɗora k'asa kuna kallo dai yadda kullum k'ara daukaka yake yi dukiyarshi sai habbaka take yi kamar shuka ana zuba mata fertilizer mun kasa yi komai. Idan har dukanku kwakwalenku sun daina aiki ni zan sa ayi masa mai gaba d'aya haihuwa da hanji...

"Dakata Ahmadu!

Hajiya kubra ta katse shi a tsawace dama can kawarsu bata gamo ba, duk lokaci da suka haɗu sai sun yi uwar watsi. Ta ci gaba da faɗin

"Kai miyasa ka cika fushi da daukar zafi?" Garin bak'ar zuciyar taka za ka iya kai mu ka baro kai mana shiru mu ji dalilin kiran gaggawa da muka samu daga babban yaya.

"Ke Kubra ki shiga taitayinki dani nafi ki rashin mutunci wallahi...

"Dallah ya isa haka ku kenan da zarar kun haɗu ba za ku ta6a rabuwa lafiya ba. Sai kun sai da hali.

Alhaji Yusuf Junaid ne ya kawo k'arshen musayar yawun nasu. Ya ci gaba da faɗin.

"Dalilin da yasa na me ganinku da gaggawa jiya ne Alhaji Buba ya zo min da labari wani shararren boka sha yanzu magani take. Aikinsa yana ci domin ya yi masa aiki cikin kwana uku buk'atarsa ta biya. Shine naga dacewar mu kai masa ziyara watakil adace ya kawar mana da Azaad.

"Haba Yaya har yaushe za ku gano aikin bokaye nan duk k'arya da yaudara ne?" Kawai ku bar min wuka da nama ku ka aiki da cikawa 'yan ta'adda za nemo su yi mishi yanka rago.

Hasheem ne ya yi magana yana hura hanci duk cikinsu shine mai k'anana shekaru.

Alhaji Abdallah ne ya kar6e zance ta hanyar faɗin.

"Kai dallah rufe mana baki idan har kai ba ka da hankali mu ba sakakkaru bane irinka, muddin muka sa aka kashe Azaad ta wannan hanya jami'an tsaro ba za su yi shiru ba, za su tsananta bincike kasancewar Azaad babban mai kud'i. Nan take za a gano mu. Saboda haka mu gwada zuwa wajen bokan ya kashe mana shi."

"Shikenan Babban Yaya gaba ɗayan mu, mun amince gobe da sassafe sai mu shirya mu tafe k'auye da boka yake.

Da wannan shawara suka kawo k'arshen secret meeting ɗin nasu.
**********************
"Aneesa ina so ki bani aron kunnenki, ki saurare abin da zan faɗa.

Azaad ya yi magana fuskarshi a daure tamau..

"Tam Daddy!

Aneesa ta faɗa tare sadda kai k'asa tana wasa da wayar hannunta.

"Daga yau mai kama da rana ta yau Kar ki sake bari na kama ki da laifi rashin ɗa'a a school ke ba iya school ba ko a gidanan naji labari kin ma wani daga cikin housemaids rashin kunya, za ki sha mamaki irin hukunci da zan zantar akanki. A dalili abin da kike yi aikatawa ga Airah nan ta fara koyi da halinki. Haka ku ke so rayuwarku ta dinga tafiya a baud'e?" Idan har ita mahaifiyarku bata damu tarbiyyarku ba, ni hakke ne da ya rayata a wuyana, da izzini ubangiji sai inda k'arfina ya k'are."

Tun daga lokaci da ya fara magana har ya dasa aya bata ɗago ba jikinta sai rawa yake yi, saboda duk iya shegenta tana bala'in tsoran mahaifinta. Ta ɗago kanta da kyar bakinta na rawa tace.

"Kayi hak'uri Dadda in-sha-Allahu na daina ba zan k'ara ba.

"Da yafi miki.

Ya faɗa a takaice kana ya juyo kan Airah wacce tuni tsoro ya gama bai-bayeta, dama tasan za a yi haka daga zarar ya gama da Aneesa kanta zai dawo.

"Ke kuma da kike koyi da Aneesa miye abin burgewa a cikin halayenta da har za ki koya?" To bari ki ji duk irin hukunci da zan zantarwa da Aneesa kema irinshi zan maki.

A matuk'ar tsorace Airah take kallon shi, har idanuwanta sun fara kawo ruwan hawaye.

"Daddy Don Allah ka yi hak'uri ka yafe min sharrin shaidan ne.
Chapter 5 · 0% Book details