← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 27

Sashe 1

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*AZAAD JUNAID*
The young Billionaire
Na
Jeeddah Aliyu

*Haske Writers Association*

*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare duk wnd yy using set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali😘just start placing ur orders dearies DNT be left behind
Available product👇
Herbal whitening black soap:3k
Beauty kit:11k
Blacksoap/molato whitening soap: 3500
Bridal kit:20k
Muna maraba da masu siyan daya ko sari
Chat
08062991549
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀️

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee

Sannan munada frames masu kyau shima siyan daya ko sari 07046881166
08062991549

Sannan gamai bukatan abinci, cakes,meatpie,samosa nd spring rolls, traditional juices nabiki shima yy hanzari yy mgn 08062991549
Mungode🤝

Free Page
1....

"Wai ke Salima wacce irin mace ce sau nawa zan faɗa miki ban amince da wannan tafiyar taki ba?"

Ta cikin mirror da take zaune a gabanshi tana gyara daurin d'an kwalin dank'areren lace da ke jikinta ta aika mishi Kallon uku saura kwa6o tare da ta6e bakinta. Kana ta mik'e ta nufi wata k'atuwar show glass mai d'auke da tarin designers shoes & handbags tsaye tai ta k'urawa show glass ɗin idanu tana nazari wanda ya dace tasa
Ta d'auki half cover golden in colour na company lamis elwan tare da handbag ɗinsu. Ta ra6a gefenshi ta wuce abinta sosai hakan ya k'ara linka masa 6acin rai da yake ciki, ya dunkule hannunshi na dama ya nushi bango d'akin ba tun yau ba yake nukurkusa bakin cikin matarshi Salima wacce shi kanshi a yanzu ya fara yarda da tafi k'arfin shi. Bai isa ya faɗa ta ji ba tabbas a wannan karon zai tabbatar mata da shi ke iko da ita ba ita ke iko dashi ba.
Cikin zafin nama ya bi bayanta da k'arfi yake taka steps hakan ne yasa yai nasarar cin mata a downstairs parlor.

"Salima!

Yadda ya kira sunanta da k'arfi yasa housemaid ɗin da ke cikin parlor suka fice da sauri ba tare da sun bari ya had'a idanu dasu ba. Nanny Lacey da ke zaune a dinning room tana ba wa k'aramar 'yar su Ahlam abinci tai sauri daukarta ta nufi d'akin yara da ita.

"Wannan wane irin wulak'anci ne ina magana za ki fita ki bar ni wato ga mahaukaci ko?"

Ya k'arasa magana yana huci.

"Look Azaad Kar ka nemi tashin hankali dani domin karshenta za ka dawo kana regretting.

Ta faɗa ba tare da ta juyo ta dube shi ba ta ci gaba da tafiya.

"Da gaske nake yi ban amince ba asalima inaso ki rubuta resigning letter, lokaci ya yi da za ki zama full housewife ki kula da tarbiyyar 'ya'yanki domin gaba d'aya tarbiyyar su a gur6ace take. Kina kallon abin da ya faru yau a school ɗinsu yaushe aka haifi Anisa da har za tai dambe da schoolteacher ɗinsu.....

"Enough is enough Azaad!

Ta katse shi cikin tsawa da tada murya tuni sautin muryar ta ya kere nashi kana ta ci gaba da faɗin

"Na fahimce dukan da aka yiwa Anisa kai ko a jikinka asalima so kake yi ka d'auki laifi kachokan! Ka dora min. Idan har kana jin ba za ka iya sauya mata school ba, to ni zan iya domin sani kanka ne ban dogara da abin hannunka ba....

"Ya ishe ki Salima! Nace ya isa! Har sau nawa kike so a sauyawa Anisa makaranta sa'o'inta suna aji huɗu a secondary amma ita tana jss three shin hakan Kaɗai bai isa ya haska miki lalaci 'yar ki ya yi yawa ba?"

"Yar ta Azaad kace 'yar ta wato ni Kaɗai Allah ya ɗorawa tarbiyya yara kai ubansu ba da kai ba ko?"

"Kwarai kuwa domin kece uwa ke ya dace ki zauna gida cikin 'ya'yanki ki kula dasu ba ni ba. Abin da ya rataya akaina shine hakkin ci da sha kuma dai-dai gwargwado na tsare muku su. sannan ki tuna ina da hakki akanki sai mu share watani uku Salima ban had'a shinfid'a dake ba. Angaya miki ni dutse ne ko waliyi da bana buk'atar mace?"

"Yanzu kan na fahimce inda ka dosa Azaad kawai ka fito fili ka faɗa min ba ka so ci gabana. Allah ya rufa min asiri na dogara da kaina bana tsayawa jiran sai kayi min, shine kake so ka tauye ni to bari ka ji inaso aikina domin bana ko tantama da banida kud'i ko na fito gidan babu da ba yadda za a yi kai ɗin ka aure ni.

Cike da takaici yake K'are mata kallo ko wane furunci dake fitowa daga bakinta k'ara mishi 6acin rai yake yi, shi mutum ne da bayaso hayaniya yana da matuk'ar sanyi hali shiyasa a koda yaushe Salima take zantar da hukunci kuma dole ya bi koda hakan bai masa dad'i ba. Amma tsabar sanyi halinsa ba zai ta6a bari ta fahimci hakan ba, ita kuma anata 6acewar basira take gani kamar tsoronta yake yi.

"Ki sani Salima furuncin nan kin sha faɗa min shi ba sau daya ba, ba sau biyu ba. Kin faɗa min shi bila'adadin, kuma yana cikin kalamin ki da ke matuk'ar sosan rai

"ka ga Azaad ka bar ni haka nagaji da saurare tsofaffin maganganun ka, domin duk ciki abin da ka faɗa babu sabon abu a wurina kana bata lokaci ne kawai.
Chapter 1 · 0% Book details