← Book details Amani Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 22

Sashe 9

Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

dabi un sa. A dalilin shi mutum ne mai charismatic personality da duk inda yaje sai an so shi. Ta fahimci kamar ita kadai ke kin Mukhy a duniyar subhana, kuma kamar shi din ya zame mata dole a yanzu, aure ba wasa bane duk da bata da ilmin sa, abinda ta sani akan aure shine mijin da igiyoyin auren ta ke hannun sa, sai yadda ya ga damar yi da rayuwar ta da gangar jikin ta har wani lokacin, da zuciyar ta. Ya Rabbal Alamin . Wane irin bala I ne ya tunkaro ta haka? Saukar ta daga motar nan na nufin yau zata kwana daki daya da Mukhtar Diffa! Matsayin miji da mata na Sunnah. Wannan wace irin bakar rana ce da bata san kaddarar da ta yi mata sanadin ta ba? Ai ko Mukhtar bai sayar da kan nata ba kamar yadda ya ce cikin gatse, ta tabbata sai ta gwammace bata san wani mai suna Mukhtar ba, daga irin halayen sa da ta fuskanta na son girma da rashin daukar raini, muddin bazata sauke kai ta yi masa irin girmamawar da yake so, ya kuma taso ya ga ana yi masa ba, ya ga mace (wato mahaifiyar sa) na yi wa mijin ta (mahaifin sa) a gidan su ba, wani zubin tamkar ta yi masa sujjada, to kuwa zata sha wahalar sa. Ya riga ya san babu wannan tarbiyyar a tare da ita, to daga yau zata fara daukan ta bisa dole, in ba haka ba bai da wani courage na kai ta gaban iyayen sa a matsayin matar sa uwar da ya zabawa yan sa. Tunanin ta ya gama bata cewa Mukhtar ya tsayar da su a Lagos ne don ya samu damar da ya dade yana neman samu a kan ta, wato damar da zai wulakantata son ran sa, a inda bata da mai ceton ta sai Allah, shine dalilin da yasa ya shirya musu kwana wuri guda da sunan transit, bata yi tunanin cewa Mukhtar mijin ta ne da shari ah ta halarta zaman nasu waje guda ba a yanzu. Har Mukhy ya je ya kama masu daki ya dawo Amani na zaune cikin mota bata ko motsa ba tana ta tunanin da bai bata mafita ko guda daya ba. Ya dauki kayan su a booth ya kai ya dawo tana nan yadda ya bar ta; ihu ne kawai bata kurma ba. Damuwar duniya da bacin ran da take ciki ya gama bayyana kan sa a kan kyakkyawar fuskar ta, wadda yanzu ta hade tayi jazur idanun ma suka yi jazur abin ki da farar mace. Mai taxi ya kunna mota ya ce ta fita shi zai wuce, sai ta juya kai ta dubi inda Mukhtar ke tsaye, ya harde hannuwan sa a kirji yana kallon ta, yana jira ta gama sake-saken wadda zata fishsheta, kafin ya gaya mata cewa shima bai shirya kwana daki daya da mace ba, don bai taba ba, kuma bai shiryawa rayuwar sa hakan a nan kusa ba, don bai shirya sallama samartakar sa ga macen da bata san darajar shi ba. Da a ce zai iya, da ya gaya mata hakan ko don hankalin ta ya kwanta, cewa daki ciki da falo ya kama musu; shi ciki ita falon, don ma ta daina kissima abinda take kissimawa wanda shi bai taba kawowa ran sa ba. Mai taxi sai ya koma masifa yana fadin ta fitar masa a mota zai tafi, haka dole kanwar na ki, Amani ta ja dogayen kafafun ta ta fito masa daga mota, rataye da yar farar hand bag din ta mai matukar kyau samfurin (Louis Vuitton), da cokalelen takalmin ta kamar zai huda kasa, sai Mukhtar ya saki ajiyar zuciya ba tare da ya san ya yi ba. Ya juya, ita kuma ta bi shi a baya, a haka suka isa har cikin lifter , inda suka shiga ya tashi da su ya sauke su a kofar dakin da ya shigar da kayan su. Bata da zabi banda na bin sa ciki, tana tafiya tamkar ba ita ba, sabida yadda tayi cooling. Kan ta yayi down, bata ko iya dago kan ta. Duk da haka ba wai ta rasa komai bane daga izzar ta da takamar ta na halitta ba. Wadanda da su Allah Subhana ya halicce ta. Kuma dai an ce hali zanen dutse ne amma tabbas a wannan lokacin bakin ta kanwa yayi la asar. Sai dai da yake an ce aure yakin mata , ni TAKORI na yarda da wannan zaurancen, domin kuwa hakika yau naga tasirin sa a tare da jarumar mu mai kasaita da izza wato Amina (Amani) domin tasirin sa ya kurda cikin jikin ta yana yaqar ta ta ko ina ba tare da ta sani ba, dalilin da yasa tayi dan sanyi kenan, a lokacin da Mukhtar ya sanya mukulli ya bude kofar dakin nasu, ya bata hanya ta fara shiga, sannan ya wuce ciki ta bishi a baya, sai dai a wannan lokacin idan ka lura da kyau zaka fahimci gab take da fashewa da kuka wanda ta san idan ta yi shi babu mai taimakon ta!!! **** **** ****
Chapter 9 · 0% Book details