Sashe 10
Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna shiga dakin Mukhy ya maida kofar ya rufe, sannan ya dau jakar kayan sa ya wuce ciki batare da ya kara bi ta kan Amani ba. Don yunwa yake ji sosai, in yana jin yunwa kuma (at times) zuciyar sa a kusa take. Da ta gaji da tsayuwa dole ta nemi kujerar falon ta zauna, tana maida numfashi, so ta ke ta yi wanka ko ta ji dadi a ran ta da jikin ta, sabida yadda jikin ta ke mata danko danko na gajiyar tafiya, amma ta daure don tana jin nauyin shiga toilet alhalin yana dakin. A ran ta tana jira ya zo ya ce ta shiga ciki ita ta hau gadon, kada ta yi ciwon baya in ta kwana akan kujera, in ya so shi ya kwana a falon, amma gogan nata sai ji ta yi yana kakkabe gadon, da alama kwanciyar sa zai yi. Ita kuwa ko oho. Amani ta dauki kayan wankan ta a jakar ta ta shiga toilet ta kulle da key ta ciki, sannan ta yi wankan ta a hanzarce kuma a darare, don ji take kamar zai bude ta a toilet din, ta samu ta ji dadin jikin ta, sai ta dauro alwallah ta zo ta bada faralin sallar azahar ta wuce su a hanya. Mukhtar tunda ya canza kayan jikin sa zuwa na barci yayi sallah sai ya kishingida yana hutawa a kan sofa-bed na dakin cike da gajiya, ko ci kan ki bai ce mata ba. Daga bisani yunwar cikin sa ta dame shi, sai ya janyo kan telfon din hotel din ya kira restaurant din su, ya bada odar abinda yake so ya ci wato pounded-yam and egusi soup, sai ya tuna Amani bai san favourite food din ta ba tun sanin sa da ita, do haka ya fito ya tadda ita, da kan telfon din a hannun sa ya fito falon da ya bar ta a zaune, ya samu ta yi wankan ta har ta shafa mai, tana sallah lokacin, daidai ta sallame sallar ta ta mike kenan tana nade mayafin ta, ya dube ta ya ce. Hajjaju may I know what you want to eat? Amani tayi banza da shi kamar ba ta ji shi ba, wai ita ce Hajjaju, irin ya maida ita tsohuwa din nan, ko me yake nufi da wannan sunan? Ko duk cikin ire-iren wulakancin sa ne zai dubi yarinya yar kwalisa kamar ta ya ce mata Hajjaju? Ganin ta yi kicin-kicin da fuska kuma bata amsa shi ba, yayi kasa da murya ya ce ba da matar dakin nan nake magana bane? Ko Hajjaju bata ji na? A fusace ta juyo, ta watsa masa manyan idanun ta da ke cike da tsana, raini da fushi mai yawa, ta ce idan na ji, ka kuma ban ga damar amsawa bane sai me? Sai a ka ce dole sai na amsa? To bana cin komai, ko dole ne sai na kula ka? Ina ruwan ka da cin abinci na ko rashin sa? Hanya ce kawai ta hada mu, zuwa Saliyo, kuma da sannu zata raba mu, so ka tsaya iya matsayin ka na abokin kan hanyar Saliyo Mukhtar ya ce ni kuma na yi rantsuwa sai kin bani amsar me zaki ci, kin yi kadan in yi miki magana ki mayar min da zancen banza, ni zaki gayawa hanya ce ta hada mu alhalin kina matsayin matar aure na dana biya sadaki dagumi na ba na wani ne ya biya min ba? Ya soma takowa zuwa gare ta kafin tayi aune ya saki kan telfon din hannun sa ya yi wuf! Ya kama tsinin karan hancin ta da bakin rashin kunyar ya murde su tare, sai da Amani ta saki kara don azaba, tana son kiran ka cece ni Daddy! Amma Mukhy ya murde bakin da hancin ya hana sauti fita sai da wasu hawayen azaba suka feso mata. Sannan ya sake ta yana fadin this is last warning! Kika kara yi min rashin kunya wanda ya fi shi zan miki. Kuma duk abinda nasa a ka kawo sai kin ci wallahi ba zan yi asara ba Ya zauna a kujera ya kira kitchen, ya ce su kawo masa tuwon dawa miyar shuwaka. Shi kuma pounded-yam with egusi soup. Ba jimawa aka kawo, tana tsaye inda ya murde mata baki tana hawaye dafe da bakin nata wanda take ji kamar Mukhtar ya tsinke shi daga jikin ta, ya ce zauna mu cinye shi tas tace Allah ya sauwake in ci abinci da kai, abincin ma tuwon dawa, nayi maka kama da yar talaka ne? Ko aka ce maka kowa ma faqiri ne irin ka? Maganganun ta sun tsorata Mukhtar don rashin tarbiyyar magana da ke cikin su ya isa, ya ce sannu yar Qaruna, wato bakin naki har yanzu bai mutu ba ko? Yana bukatar sabon garambawul ya mike ya doshe ta tayi maza ta haura bayan kujera kamar wata yar wrestling. Mukhy ya ce mara kunyar karya, ki tsaya mana in ba tsoro ba? Ki gani in ban yi reshaping bakin ba ta hanyar kara miki girman sa? In the way and manner da gobe da kudi aka ce ki yi min rashin kunya da gorin arziki wallahi baza ki yi ba ta ce ba tsoron ka nake ba, bana son ganin ka kusa da ni ne, balle kodaddiyar fatar ka ta gogi tawa, don ban sani ba wannan farin naka ko ka hada dangi da zabiyu (albinos) Mukhtar ya hadiye zafin da maganar ta yi masa ya ce Allah ko? Su zabiyu ba mutane bane kenan? Zaki ga zabiyu ganin idon ki, ranar da kike shayar min da fararen ya na masu kama da zabiyu, na lura fata ta ta tsole miki ido, don tafi taki haske, idan ke mayya ce ki ci kan ki, ni kurwa ta kur! Amani ta soma hawayen bakin cikin kalaman sa ta ce Kada Allah ya nuna min wannan ranar, ko makamanciyar ta ko a cikin mafarki! Wato ranar da zan haihu da kai Aka kwankwasa kofa ya je ya karbo abincin ya dawo. Ya zauna ya fara cin abincin sa cikin nutsuwa da dadin rai ya manta da ita a tsaye, Amani na nan tsaye har zuwa lokacin kamar soja ta ki zama, don ta fara tsorata da irin kalaman sa kamar ba Mukhtar ba, ya ce ki zauna ki ci tuwon nan ki kuma cinye shi tas, ba zan yarda ki kwana da yunwa ba saboa hakkin ciyarwa, kin ji ko yar Qaruna? Idan kuma kika ki, wallahi mai raba ni da ke a dakin nan Allah ne kadai, Amani bata san sanda ta zauna gaban tuwo tana kuka ba, bakin ta har yanzu bai daina radadin murdar da ya sha ba, bata so a kuma, ta ce fisabilillahi ka takura min, ka na son matsanta min, ni bana ta ammali da tuwon dawa, sai ka saiwa kan ka sakwara ni ka saya min bakin tuwo? Saboda Allah amanar da Daddy ya baka kenan? Mukhtar ya hadiye dariyar da ta bashi ya ce to naji mu yi musanye, na gan ki babu kumari ne, fingi fingi kamar kazar mayu, ina so kashin ki yayi kwari ne kafin ranar amarcin mu, wato ranar saka kwallo a raga, ranar da zan yaye duk wani hijabin raini dake tsakani na da ke, kafin zuwan ranar nake so ki yi kwari, ki yi kumari, yadda zan ji dadin hutawa sosai a kan kowacce gaba babu fargabar zan iya ballaki, ko kasusuwa su zo suna suka na, shi yasa nake son ki fara ta ammali da tuwon dawa tun yanzu, don ki samu sinadarin carbohydrate sosai a jikin ki Ai jin abinda Mukhtar ke cewa sai bakin Amani ya mutu bakidaya daga nan, bata taba zaton yana magana haka ba, balle kuma a ce ita yake gayawa, ta san dai tsakanin su babu ragayya, amma bata san akwai sabo irin wannan ba ba da har zai iya furta mata wadannan maganganu masu nauyi haka, ko kuwa su maza daga ranar da aka daura musu aure shikenan kunyar su da bakunta ga diya mace ya tafi shikenan? Amani ta tambayi kan ta, amma bata iya ta baiwa kan ta amsa ba, sabida kallon da Mukhy ke mata A rude ta zauna ta hau jefa loma bayan loma bayan wata hararar bakin ciki da ta zabga masa, sai ta cigaba da jefa lomar tuwon dawa babu kakkautawa, bata ma bi ta kan sakwarar da ya ce ya yarda su yi musanye ba, ba don komai ba sai don yadda maganganun nasa suka kidima ta suka gigita ta, suka rikita ta duk a lokaci guda, don bata taba zaton su daga bakin mutum kamamme irin Mukhtar ba. Duk da a yawan shekarun ta ta san cewa sha ani na aure ya fi gaban nan. Sannan babu babba babu yaro when it comes to marital affair. Amma bata taba zaton Mukhtar zai iya furta mata su ba, in aka yi la akari da irin personality din sa na kamewa, fadin rai, girman kai da rike girma, da yadda ta dauka cewa kwatakwata ya tsaneta ba ya son ta. Ba ta yi tunanin zai taba wannan hasashen na samuwar ya a tsakanin su ba, wanda ke nufin yana hasaso physical relationship (bodily contact) watarana a tsakanin su. Gara ta cinye tuwon dawa komai yawan sa a kan dai Mukhy ya kara yi mata wannan sabon da kunnen ta ba zai iya jure ji ba, sabida nauyin da maganar ta yi mata a kwanya, don ji ta yi tamkar Mukhtar yayi babban sabo, yo sabo mana! Tana kara maimaitawa a zuciyar ta .... kada Allah ya nuna mata wannan ranar da yake hasashen zuwan ta! Sai da ya tabbatar ta cinye tuwon sannan ya kyale ta, kuma ya yi mamakin ganin yadda ta cinye shi kamar kiftawar ido, bai san tsabar rudewar da kalaman sa suka saka ta bane yasa ta cinyewa cikin rashin sani, ya mike ya wanko hannun sa sannan ya fita zuwa reception don ya yi waya da Alhaji, yayi wayar wajen tsayin awa guda kafin ya dawo dakin, nan ya ga Amani a kan doguwar kujera tayi wata irin takurarriyar kwanciya, ta kuma kankame jikin ta cikin rawar dari sabida sanyin