Sashe 5
Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sha Allah, zan canza booking din da nayi mana ya zama daga Bauchi zamu wuce Lagos, inda zamu hau jirgin Freetown Hamidah ji tayi farin ciki ya lullube ta kamar ita ce Amanin, burin kawar ta at last zai cika. Zata ga Innar ta! Ta san kowacce irin damuwa Amani ta saka kanta a ciki a kan auren ta da Mukhtar zata zo da sauki muddin zata ga mahaifiyar nan tata data kallafawa rai. In ta ga dama ma tace bazata dawo ba, hakan zai fiye mata kwanciyar hankali in har Amani tana tare da Maman ta, fiye da in ita Hamidan ta ki bata goyon bayan bijirewa Daddy ta bar gidan su ta nausa wani wajen da baza a gan ta ba, don ta san halin aminiyar ta sarai ba tun yau ba, bata saba in tana son abu ko ta saka kanta abu a hana ta ta karfi ba, tunda ta taso ya riga ya saba da yi mata komai take so komai tsaurin sa, shi yasa yanzu Daddyn ke shan wahalar ta da ya zo yana son tankwara ta ta karfi, bayan tun tasowar ta ba haka ya sabar mata ba. Sun yi sallama da Mukhy a kan in ya sauka a Bauchi goben zai kira ta, ta bashi lambar wayar ta, har rokon sa ta yi da kada ya kama hotel in ya iso, tace akwai gidan saukar baki a nan cikin gidan su, tunda dole sai sun kara kwana a Bauchi kan su wuce Lagos din. Bayan sun gama wayada Hamidah ya gayawa Alhaji ashe wajen kawar ta ta tafi a Bauchi. Nan dai hankalin su ya kwanta suka soma shirin komawa Katsina washegari. Baba Idi ya ce wallahi idon sa idon Amani sai ya zane ta. Sai da suka tsaya a Funtuwa Sahura ta yi sallama da yanta ta dauki kayan ta sannan suka wuce Katsina, har da Kamilu, wanda Mukhtar ya ce ya dinga kula da Alhaji har ya dawo tunda zai yi tafiya gobe. Duk irin kulawar da yake masa ya nunawa Kamilu, ta ci da sha da shan magani da tsaftace masa jikin sa, kuma Kamilu yayi alkawarin kwatantawa. Alhaji ya sa Rakiya ta kai Sahura dakin Haj. Rabi ya ce ta zauna a nan, Kamilu ma aka bashi daki a cikin gidan daura da na Alhaji. Mukhtar ya gaya masa sai ya dawo daga tafiyar da zaiyi zai kai su kamfani da Boutique din Amani, in yaso su zabi in da zasu yi aiki tsakanin shop da kamfani. Sauran kannen na kamilu da Alhaji ya baiwa aiki ba a gidan sa zasu zauna ba, duk ya basu gidan zama ne can kusa da kamfani. Kamilu ne kawai zai zauna da su saboda kula da Alhaji da tafiyar da Mukhy zai yi wadda shi kan sa bai san tsayin kwanaki nawa zata dauke su ba shi da Amani, idan har ta yarda sun tafi taren kenan. Sai ko Baba Sahura da dake dakin Haj. Rabi. Su kenan a gidan sai Rakiya mai girki. Da maigadi Malam Tajuddeen da sauran ma aikatan waje Sai dai Mukhtar ya san mawuyaci ne duk bacin ran da Amani take ciki, da halin kuncin da ta saka kan ta a ciki na babu gaira babu dalili sai kiyayyar auren sa a ce mata ga ido tace doyi yake. Wato bazata iya tankwabe zuwa gun Innar ta ba, iyakaci in aka je din ta ce ba zata dawo ba, ya riga ya san hakan ce zata faru, kuma ya shiryawa hakan. Karfe sha biyu na ranar washegari Mukhtar Diffa ya sauka a filin jirgin saman Sir Abubakar Tafawa Balewa. Sanye yake da farar shadda kal Wagambari babbar, ya aza hula zanna bukar a kan sa mai ruwan kasa-kasa ta zauna daram a cikin tarin sumar kan sa, kamar yadda takalmin kafar sa na fata kirar Italy shima ruwan kasar ne, haka fatar agogon rolex da ke daure a damtsen hannun sa na hagu wanda bakin lallausar gashi ya kwanta a hannun itama brown ce. Yana takun sa cikin nutsuwa da haiba yadda ya saba yana tura matsakaiciyar jakar matafiya. Hamidah da kan ta ta tuko motar ta ta zo daukar sa, ta baro Amani ta shiga wanka bayan ta tashi barci ta more ta sau nutsuwa. Ba yadda Hamida bata yi da ita kan ta karya kumallo ba amma Amani ta ki, ta ce daga ranar yau ta daina cin komai, ta daina shan komai, ta fi son yunwa ta yi mata illar da har har sai ta mutu, in ya so Hamidah ta kai wa Mukhtar da Alhaji gawar ta, tunda Hamidan ta ce abinda suka yi mata din ba laifi bane, kauna ce. Hamida sai ta kada kai ta fita tana dan murmushi. Har falon Haj. Muna Ha mida ta yi wa Mukhtar iso, ta gaya mata angon Amani kenan. Jiya aka daura auren, shine Amani ta taho basu sani ba. Yanzu Daddy ya ce Mukhtar ya zo ya tafi da ita zasu wuce wajen Maman ta a Freetown. Haj. Muna tace ikon Allah, masha Allah tabarakarrahman, dalilin tahowar ta a motar haya babu sanin ku ranar daurin auren ta nake son sani, ko bata son auren ne da wannan miji sardidi haka son kowa? Kunya ta kama Mukhtar ya kara dukar da kai kasa. Shi kansa yasan Allah ya kyautata halittar sa ko mutane basu fad aba, amma baya so ana fada sai yaji wani iri, Hajiya ta cigaba da fada tana cewa. Da sabon aure haka a kan ta tayi wannan kasassabar, tahowa har Bauchi babu iznin mijin ko na Baban ta? Maza kirawo min Amanin, in wanke ta tatas, haka ta zo tana langabe min jiya kamar mutuniyar kirkin da ke cikin matsala, ashe ashe gudun nata na aure ne Hamida da Mukhtar babu wanda ya tanka, amma sun ji dadi da Hajiya zata wanke musu Amani wankin babban bargo, illa yayi kasa da kan sa da ke duke yana danna wayar hannun sa. Zaune yake bisa kilishi kafafun sa a tankwashe, yana fuskantar Haj. Muna, wadda ke kan kujera tana masa nasihar yayi hakuri da Amani irin hakurin da zai yi da kanwar sa, kasancewar bata tashi tare da mahaifiya ba wani abun sai ana mata uzurin sa. Don dabi un ta ba irin na wadanda suka tashi da uwa da dangi bane. Goyon namiji ce. Shi kam Mukhtar har ya gaji da cewa da ake yayi hakuri da Amani, wai wane irin hakuri? Ita tafi kowa shafuwa da mai ko yaya ne? A wurin sa ai saidai duk su yi hakuri da juna don shima ba kanwar lasa bane, in ta so a zauna lafiya a zauna, in ta zabi tsiya a tsiyace, shi duk wanda ta zaba daidai ne a gun sa. Babu diya macen da zata daga masa hankali, don in dubu yake so a rana zai samu, bai yi ra ayi bane. Koko ya ce lokaci bai zo ba. Amani yana jin ta da matsayi na dabam ne saboda karamcin mahaifin ta gareshi da irin kauna da yardar da ya yi masa, da tausayin halin da yake ciki na rashin lafiya, sannan kuma yana da son rama alkhairi da alkhairi. Ba don haka ba Amani ta yi kadan ta wahalar da shi irin haka, ko ta saka shi yawon da bai shirya ba irin haka, yana bin ta gari-gari kamar wani jelan ta. Yana cikin wannan mitar a ran sa ya ji kamshin turaren Amani a falon. Ko kusa bata kawo a ran ta wanda ke duke gaban Haj. Muna Mukhtar ne ba, ta ina ma zata yi tunanin ya san inda take? Ko ya sani tunanin ta bai taba bata zai iya ajiye girman kan sa ya biyo ta har nan ba, balle kuma tayi tunanin Balewa zata iya tona mata asiri ta fadawa Mukhy tana gidan su a Bauchi. Har ta zauna a kujerar da ke fuskantar Hajiya bata gane Mukhtar ba, sabida keyar sa ce kawai a duke, duk da hasken fatar sa daban ne dana mutane da ke saurin fallasa shi hankalin ta bai kai kan sa ba, watakila kuma don bata taba kawowa ran ta ganin nasa anan bane. Mukhtar ya dago fusatattun idanun sa ya dubi Amani da su a lokacin da take zama a kujerar kusa da shi, bayan ga Hajiyar ma na kan kujera, wato rashin tarbiyyar nata a ko ina ma yin sa take yi har a bakon wuri, tunda dai gashi tana ganin daga shi har Hamida sun zauna a kan carpet Haj. Ce kadai a kan kujera amma ta dare kan kujera tana fuskantar Haj. Muna. Haj. Gani, Balewa tace kina kira na Haj. Muna ta jefa mata harara sannan ta dunkule hannu ta mika mata ta ce ungo naki (dakuwa) sannan ta nuna mata Mukhy da ke zaune yana hararar ta shima wata irin sassanyar harara. Ga mai kiran naki nan, ba ni bace, dauko mayafin ki kafin in kyafta ido na, sawun ki a likkafa ki bi shi duk inda ya sanya kafa bisa umarnin mahaifin ki, ina maki kallon mai wayo ashe Amani sakarai ce ke? Ki sa kafa ki taho ke kadai tun daga Faskari ba da iznin mijin ki da sanin mahaifin ki ba? Shin kina son albarka Amani ko kuwa kin fi mahaifin ki sanin abinda yake daidai a gare ki? Sai a lokacin Amani ta gane Mukhtar ne, da kuma ainahin fadan da Hajiya ke yi. A firgice ta juya ta kalle shi suka kuma hada ido, saura kadan fitsari ya kwace mata da irin zazzafan kallon da Mukhtar ke mata. Hankalin ta in ya yi dubu to ya tashi tsaye, nan take ta hau yi wa Haj. Kuka mara sauti tana fadin Hajiya ki yi hakuri ni ba zan koma Katsina ba, idan kin kore ni ma gaba zan nausa Hajiya tace ki wuce birnin Sin, amma tare da mijin ki ba da ni ba, maza Hamidah dauko mata kayan ta kisa a bude musu guest house yanzu, su kwana gobe sai su yi sammako tunda dare ya riga yayi yanzu Amani ta wuce dakin Hamida tana kuka wiwi tana tattara kayan ta. Hamidah ta shigo dakin tana fadin da gaske Sahibah ba wanda ya isa ya gaya