← Book details Amani Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 22

Sashe 16

Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nade Ta fashe da kuka tana cewa ko sadakin su ban karba ba, don haka babu wani auren sa a kai na ni. Baba Idin ma ya san ban karba ba shi na barwa abin sa, sai dai in Baba Idin ya aura an tayi ta awizi. Tun ba a je ko ina ba Mama Jal an ta gama karantar wacece Amani, halayen ta da dabi un ta marassa kyau na girman kai, alfahari da dukiyar uban ta, fariya da izzah na rashin sanin darajar da Allah yayi wa dan adam. Yawan alfahari da rashin kunya na rashin mafadi ko tarbiyya mai inganci. Tausayi mai tsanani ya kamata sai ta kasa ce mata komai. Sabida ita ta ko ina Mukhtar yayi mata, har tsoron kwarjinin sa da ilhamar sa ta ji, don kwarjinin sa da kasaitar sa cika mata ido da falo suka yi, ta yi duba don gano makusa a tare da shi da ta sa Amani fadin abubuwan da take fada a kan sa ta rasa. Sai kawai ta gane cewa Amani wawuya ce, doluwa, gaula kuma goyon namiji. Mai halin yan fari, kuma wadda gata da kudi ya jika har ya yiwa yawa har ya taba hankali da nutsuwar ta. Bata samu tarbiyyar uwa da wadatar ilmin addini ba sai na zamani. Sanan bata samu religious background na musulunci sosai ba. A yanayin da take magana ma ga kowa, gatsau ba respect ba taunawa tana gatsine baki na raini ga Mukhy ya tsorata Jal Kamar Mukhtar itama nan take ta gayawa ranta cewa jan aiki ne a gaban ta jawur, don haka zata roki Mukhy ya bar mata Amani zuwa nan da watanni biyu haka. In hakan ba zai cutar da shi ba. Yo Allah ta tuba ina wani kwanciyar hankali da miji zai samu a tare da Amani mai abubuwa irin na zararru? Ai gara ma ya bar ta aga abinda za a iya a kan ta ko kadan ne, tunda ba a bari a kwashe daidai, kuma icce tun yana danye a ke tankwara shi. A halin yanzu tana so ta karance ta ciki da bai, don ta san ta inda zata bullo mata, da yadda zata gyara gurbatattun dabi un ta da halayen ta ko da ba duka ba, kafin ta shiga dakin miji ya zama ko manner of speaking ta gyara mata. Tunda an riga an baro kari tun ran tubani. Duk da haka zata yi iya yin ta cikin yan watannin da zasu yi tare, sauran sai ta barwa Allah mai kowa mai komaia, ta kuma hada da addu a da rokon Allah ya baiwa Mukhtar zuciyar dauka da soyayyar da zata rufe masa ido daga ganin aibun munanan halaye da dabi yar ta. Sai bata ce mata komai a kan Mukhtar ba a wannan daren, ta barwa ran ta, don so take ta gano root causes na matsalolin sangartar Amani da rashin good upbringing din data samu, sannan ta yi tunanin hanyoyin magance su a ilmance. Duk da ita ma din ba wai ta samu zurfin ilmin zamani bane amma tayi sakandire kuma tana da ilmin addini sosai, sannan ga shekaru ga kyakkyawan hankali. Amani ta nemi ta bata nata labarin. Bayan rabuwar ta da mahaifin ta. Nan ta gyara zama ta soma bata labari ta gaya mata cewa bayan Daddy ya sake ta a gadon asibiti basu taho ba sai da ta warke tas, suka dawo Saliyo tare da iyayen ta. Maman ta tayi mata jego, har ta warke. Mahaifin ta yayi fushi da ita fushi mai tsanani a kan rashin biyayyar data yi masa na kin zama da Alhaji. Ta hana shi samun makudan kudaden da yake samu a hannun Alhaji Usman. Yace yanzu gashi ta janyo ya raba ta da diyar data haifa kuma babu tabbacin yarinyar zata rayu ko a ah, ko zasu sake haduwa, tunda babu wanda zai shayar da ita. Ni kuma kullum na yi sallah sai na roki Allah ya raya abinda na haifa koda bamu sake ganawa ba, yasa rayayye ne kuma ya amfani musulunci da al umma. Daga baya bayan wasu watanni, Luqman tsohon saurayi na dana ke so ya dawo neman aure na. Da kyar na samu mahaifi na ya yafe mini, yace Yaya ta Aisata tayi mishi biyayyar da ni ban yi mishi ba, don ita kam sayar da ita ma yayi a Nijar ga wanda bai ko sani ba, don haka kada in taba tsammanin zai barni in zauna a gidan sa, in kawo miji kawai talakan dana ke so yayi min aure ya huta. To dama ni da Luqman mun dade tare kuma a kan sa ne naki zama da Alhaji Usman, da kuma nasa halayen wadanda na san ba sai na fada miki ba, tunda baban ki ne ya kamata ace kema kin san su. Muka yi auren kauna da soyayya ni da Luqman, wanda shine mahaifin su Fajur, ma aikacin kamfanin Tama da karafa ne (Steel Rolling Company), wannan gidan, shine gidan da muka rayu a cikin sa tsayin shekaru goma sha tara ni da Luqman, cikin rayuwar aure ta soyayya da fahimtar juna wadda mahaifin ki bai iya ko daya ba, shi dai ya yarda kudin sa ne zai samo masa duk irin matar da yake so a duniya. Shekara na zagayowa na haifi Safwan, sai bayan shekaru biyar da haihuwar sa har mun fidda rai sannan daga baya na haifi Fajur, a shekaru ukun baya ne Allah yayi masa rasuwa bayan gajeruwar rashin lafiya. Iyayen mu kuwa sun jima basa raye, Aisata ya sayar da ita a kasar Nijar ko zuwa Saliyo bata kara yi ba tun karbar ta da aka yi aka tafi da ita aka bashi Rakuma masu yawa, wato shi mahaifin namu a matsayin sadakin ta, lokacin rasuwar mahaifin namu ne ban san ya akayi ta samu labari ba ta aiko min wasika ta taaziyya ta gaya min watarana zata aiko a kaini inda take aure a Nijar, kuma tun daga wannan lokacin ne ta soma yi min aiken kudi lokaci-lokaci duk da bana cikin bukatar komai, ina tare da miji na cikin kwanciyar hankali da rufin asiri lokacin, bayan rasuwar Baban su Fajur na aika mata ta hanyar dan aiken da ke kawo wasika a tsakanin mu wanda dan kasar nan ne mai kasuwancin Rakuma a Nijar, shine fa ta bude min asusu, wanda kai tsaye duk wata take turomin kudade na Saifa masu kauri, wadanda da su ne na cigaba da daukar nauyin karatun yaran nan, muke kuma cin abinci, na kuma soma sana ar kiwo, ga abinda mahaifin su ya mutu ya bar mana muna juyawa a gona, muna samun amfani daga noma da kiwon kaji da kiwon shanu. A takaice kin ji wannan itace rayuwar da muke yi a halin yanzu. Safwan yana rubuta jarrabawar kammala sakandire yanzu a nan makwabtan mu wato Gambia, ya zo hutu ne, Fajur tana karatu anan wata karamar sakandire ta kudi a bayan gidan nan, kullum da kanta take zuwa ta dawo ta huta ta wuce Islamiyya **** **** **** MOTHERHOOD uwa washegarin ranar, hatta makwabtan Jal an bakidaya sun san da zuwan yar ta dake Najeriya aka shigo ana yi mata barka, wasu na aiko abinciccikan kwadayi wa Amani, kasancewar Jal an ta mutane ce mai yawan kyauta da kyautatawa ga makwabtan ta, anata mamakin kamannin su ita da Amani in ka dauke cewa Jal an mai jiki ce Amani siririya. Duk abokan arzikin iyayen su dake raye sai da ta kai Amani a washegari suka gan ta. Basu dawo gidan ba sai da yamma lis. Shima Mukhatr baya gidan tun safe Faytoory ya zo ya dauke shi, sun shiga gari yana nuna masa wurare masu tsohon tarihi na Kenema, da inda ake Mining din Diamond. Daga can suka wuce gidan Faytoory suka ci abinci da iyalin sa sai lokacin suka dawo gidan su Amani. Faytoory ya ajiye Mukhtar kenan suna sallama da cewa gobe in sha Allah da wuri zai zo ya tafi dashi Freetown, inda daga can zai hau jirgin Lagos. Mama Jal an ta aiko Safwan ya kira shi su ci abincin dare yadda suke yi kullum, a lokacin yana hada kayan sa a jaka yana tunanin tunda su ka zo rabon sa da kebewa da Amani ko da da sunan su gaisa, wato ya gama mata amfanin da zai mata, tunda ta dafe uwar ta a gefen ta shikenan. Sai ya shiga tambayar kan sa na me zai yi wannan tunanin ma? Amani ce fa! Wadda ya sani ba tun yanzu ba. Ai ya dade da sanin Amani ba yar goyo bace shakiyya ce ya sani dama, kuma ta fada ta kara haduwar su ta kan hanya ce da zarar ta ga uwar ta babu ita babu shi. Ya tuna cin mutuncin data yi masa sa Freetown da zagin fitar hankali na sheganta shi, sai ya ji zuciyar sa na kara tafarfasa, Amani na kara fita a ran sa. Amma mutuncin iyayen ta a zuciyar sa na kara ninkuwa. A ladabce Safwan ya shigo ya gaida shi, sannan ya gaya masa sakon Mamma na ya fito su ci dinner tare. Ba tare da ya dago ya dubi yaron ba don baya so ya ga idanun sa, a dai yanayin da suke ciki yanzu na tsananin bacin ran Amani. Ya ce ya je ya gayawa Mamma cewa a koshe yake, ya ci abinci a gidan Faytoory kuma yana so zai shigo yayi mata sallama don gobe in sha Allah zai koma Katsina. Safwan ya je ya dawo ya ce Mamma ta ce ya shigo, a gaskiya a lokacin baya son shiga cikin gidan a yanayin da fuskar sa ta koma yanzu, wato boyayyen yanayin nan nasa da ba kowa ya san yana da shi ba ya bayyana, domin baya so Hajiya Jal an ta ga hidden side din sa na rashin walwalar nan. Gashi idan ya zo baya iya controlling din sa har sai ya bace don kan sa. Sannan haka kawai yake jin muryar Mamma Jal an da accent din ta kamar yadda yake jin tashin muryar Ummami, wanda hakan ke kara tono bacin ran dake kasan zuciyar sa na kewar Ummami da jin zafin ta (as well), yana kara bayyana a kan fuskar sa. Ba
Chapter 16 · 0% Book details