Sashe 6
Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
miki ki ji? Na dauka Hajiya ta matsayin uwa take a gare ki, ta dauka zata yi miki fada ki ji ko ba kya so, tunda tace ki bi shi sai ki bi shi, baki san alherin da ya zo miki da shi ba Nan ta gaya mata cewa Mukhtar ya zo ne don ya kai ta Sierra Leone Amani tayi tsit! Kamar ruwa ya cinye ta, jikin ta yayi dan sanyi, da gaske yake ko kuwa yaudara ce don ta yarda ta bi shin? Me ya hana tun lokacin da yayi mata alkawarin ya cika? Sai yanzu da ta zama matar sa da bata da iko da kan ta? Hamida ta shiga lallashin ta, tana cewa ki bashi dama Sahibah, he s a very serious person babu batun wasa a abinda ya gayawa Mama, da gaske Sierra Leone zai kai ki Amani ta rage kukan ta ce Hamida, idan da amana bazaki gaya masa inda nake ba, daga yau na san ajin da zan ajiye ki, ya kamata tuntuni in fahimci kema kina yin mutumin nan, in ba ke ba babu wanda zai gaya masa inda nake Hamida ta soma kokarin kare kan ta da cewa wallahi tausayi Daddyn ki ke bani Amani ..bashi da lafiya kuma yana cikin damuwar inda kika shiga ni bana baki tausayi ko? Ni da a ka yi wa auren dole da wannan green snake din? Hamida ta ce wato sunayen nasa kala-kala ne har haka, shine Dirty Human Being yanzu kuma shi ne Green Snake , sannan Sumumu-kasau , duk shi kadai bawan Allah! Tsaki Amani tayi tace in dai Bauchi ce yau zan bar miki kayan ku, zan shiga duniya tunda hakan kike so, ba zaki bani refuge daga auren dole ba . Hamida ta yi murmushi tace don Allah Mama ta ce in kin tashi shiga duniyar ki wuce har bangon ta (birnin Sin) Suna wannan cece-kuce din Hajiya Muna ta shigo dakin, don ta ga Amani ta bi umarnin ta ko a ah, mai aikin ta biye da ita dauke da fakadeden tray da ake jera abinci da abin sha a kai, ta ce, Amani ga nan abinci dauki ki kai masa da kan ki, Hamida ki raka ta masaukin bakin, na sa Ali ya raka shi tun dazu Hamida ta ce da mai aikin ta wuce gaba ta kai masa abincin zasu zo yanzu. Ta dauka Amani zata bi umarnin Hajiyar ta, amma ga mamakin ta Hajiya na bada baya Amani ta yi rantsuwa ba inda zata je, in kuma Hamida ta takura mata sai ta fita to kuwa ta fita kenan har abada itada sake zuwa inda Hamida take. Hamida ta dauka wasa take yi, amma sai ta ga ta rantse ta kara rantsewa kan cewa bazata kwana inda Mukhtar yake ba, har ta ce saboda daurewa karya gindi sai ki sauke shi a gidan nan? Koda yake dama ai ke kika gayyato shi, don haka sai ki karasa ladan ki ki kai masa abinci. Ki kuma kwana kina taya shi hira Hamida ta rasa yadda zata yi da Amani, ta tabbata wajen taurin kai da kafiya babu na biyun ta duk fadin garin su Faskari tabbas ta Faskari kowa, sannan a tarbiyyar da aka yi mata ba a koya mata bin umarnin na gaba ba, sai dai ita tayi wa wani umarnin. Hamida zata soma yi mata wa azi ta mike ta hau hada kayan ta ta soma kuka a haukace, fadi take in dai don na zabi yin mafaka a wajen ki ne kika tona min asiri haka bari in tafi gidan karuwai cikin daren nan, in kika takura sai na je inda yake Hamida ta rike jakar kayan nata ta ce na kyale ki Amani, ba zan kara takura ki zuwa guest house ba, amma kin manta ya ce wajen Maman ki ya zo ya kai ki? Ta ce don wannan na yarda zan bi shi, ai zaman jirgi ne kuma babu transit, daga nan Bauchi kai tsaye a hau jirgin da zai je Freetown, inba haka ba na hakura, wallahi bana ko son ganinsa Hamida . Hamida ta hadiye dariya, ta soma mayar mata da kayan da take kwasowa cikin jakar ta, tace kada ki manta hausawa dai sun ce komai wayon amarya Hararar da Amani tayi mata kamar idanunta zasu fado kasa tasa ta ficewa daga dakin da sauri tana cigaba da tillika dariya. Masaukin Mukhtar din ta nufa, so take ta ji yaya tafiyar tasu zata kasance goben, tunda ta gane transit ne Amani bata so a yi a ko ina, bata kuma jin akwai jirgin Freetown daga Bauchi dole sai daga manyan birane wato Abuja ko Lagos. Hamidah tayi sallama a kofar guest room, daga ciki Mukhy ya amsa, bai kuma taso ya bude ba amma don ya ji muryar Hamida ne, a hankali ta ce Hamida ce, zan iya shigowa? Sannan ne ya taso ya bude, kallo daya Hamida tayi masa cikin kayan barci na DKNY ta ji zuciyar ta ta tsinke, sannnan ta doka da karfi, a zuciyar ta ta shiga neman tsari daga sharrin zuciya dana shaidan masu gaya mata tace da shi, ya kyale Amanin da ta tabbatar bata kaunar sa ita ya zo gare ta . Ta yi maza ta yi ta awizi ta nemi tsarin Allah daga sharrin zuciya dana cin amana, ta bi bayan Mukhtar zuwa cikin falo, suka zauna a kujerun da ke fuskantar juna a falon, har ya yi wanka ya canza shaddar jikin sa zuwa shirt da wando marasa kauri blue samfurin DKNY. Yana shirin taje sumar nan tasa da ta jike jagab da ruwa ta mammanne a saman fatar wuyan sa, da alama bai kai ga taje ta ba, fitowar sa kenan daga wanka Hamida ta kwankwasa masa kofar. Kamshin kakkarfan turaren sa na Azzaro Visit da ya fesa yanzu-yanzu, ya mamaye dakin, ya cakude da sanyin air conditioner ya bada wani atmosphere mai dadi a falon da sanyaya zuciyar duk wanda ya shake shi. Hamida ta russuna ta gaida Mukhy with much respect, kwarjinin sa na kara rikita nutsuwar da ta shigo da ita. Shikuwa ya kara daure fuskar nan tamau kamar yadda take as usual. Duk sai ta kara firgicewa, ga kwarjinin sa ya mamaye dakin. Yarinyar bata yi kama da masu kawo shirme ba amma me zata gaya masa da zata biyo shi har inda suka sauke shi a irin wannan lokacin? Da karfin sunan Allah a bakin ta Hamida ta samu nutsuwa ta ture duk abubuwan da shaidan ke kissima mata, ta ce. By the way, ni ce Hamidah Balewa, ni kawar ta ce tun muna secondary school Mukhtar yace I can relate, tunda har zata iya gudowa wajen ki har nan tun daga Faskari ba da izni na ko na Alhaji ba . Ya fada da dan fusata a muryar sa, na ganin ta ita kadai ba tare da Amani ba, wanda kai tsaye ba sai an gaya masa ba ya gane bazata zo su yi magana akan tafiyar su ta gobe ba. Hamidah ta karya murya tana fadin, ka yi hakuri Mr. Mukhtar, Amani sai a hankali, ina so in san tsarin tafiyar taku ne ta goben in mata bayani, don nayi kokari mu taho tare yanzu ta ki Da fusata sosai ya ce then bani da say da ita, in har bazata zo da kan ta ba, in baza ta je bama ni zan koma Katsina gobe, amma ki tabbatar mata kafata kafar ta, bisa umarnnin Alhaji Hamida ta ce in sha Allahu ma zata je, ai tafi kowa son ganin Maman nata . Mukhtar yace matsalar ku ce wannan, zuwan ko rashin sa, bani da asara a ciki, ki dai gaya mata in bazata je Sierra Leone din ba ta sanar da ni a daren yau ta waya, don in saki booking din, in kuma zata je shima ina son sani don in san ina muka nufa goben daga nan. Ta bani amsa ta waya ya wadatar. Zan jirata har karfe tara na safe, don booking din mu zuwa Lagos 12 na rana ne, daga can ne zamu hau jirgin Freetown, babu jirgi mai zuwa Sierra Leone anan Bauchi Hamida ta ce a ranta transit dole Sahibah! Allah ya fishsheki daga fushin wannan Zakin Ta dawo dakin su shi kuma ya rufe masaukin nasa ya kwanta. Ya dauki wayar sa ya kira Alhaji, Kamilu ne ya dauka suka gaisa ya tambaye shi ya hanya, ya gaya masa ya isa lafiya, sannan ya hada shi da Alhajin, ya gaya masa ya sauka a Bauchi lafiya, kawar tata Hamidah da iyayen ta mutanen kirki ne, don a gidan su ma suka bashi masauki, sun roke shi kada ya sauka a hotel Alhaji ya ce ai tuntuni na san Hamida mutuniyar kirki ce ba irin Tafisu ba, shi yasa na ke son abotar tasu, da mutum yana shirya mutum da tuni Hamida ta gyara min halin Amani, to abotar tasu ba irin wadda ake kira ta abokin barawo- barawo bace Sun dade suna tattaunawa, Mukhtar ya gayawa Alhaji dole sai sun kwana a Lagos kafin washegari da asubah su bi jirgin Freetown. Alhaji yace ta dai yarda zata je din ko? Mukhtar ya nisa, kafin a hankali ya ce Alhaji maganar yarda ta je ko rashin yardar ta duk basu taso ba, abu ne dana sani ba abinda take so kuma take buri a yanzu sama da ganin Innar tata, don haka zata bi ni ne ko bata so, donmai binciken nata dan damfara ne kawai, alkawari ne na yi mata kuma dole in cika shi, zan damkata gun mahaifiyar ta in yaso in ta ga dama don Allah kada ta biyo ni mu dawo. Ni ba a matse nake ba! Kunya ta kama Alhaji, sai ya hau Mukhtar da fada, na tambaye ka wannan? Kullum ana gaya maka ka koyi lallashin mace kana kara fandarewa Mukhy, ina gaya maka wannan ne (based on experience), da a ce na lallashi Jal an, na bi ta a hankali, na yi hakuri da ita da shirmen ta na rashin so na, ban kuma yi zuciya ba na saketa a asibiti wai don tana ikirarin bata so na, da na jure da har yanzu muna tare bamu rabu