Sashe 20
Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
din da kake ciki da kuma al adu masu kyau na al ummar da ka taso a cikin su. Ke kam kin rako mata duniya!!! Ta sake rushewa da kuka, tana son fadin Mamma taba ni yayi ta yi fa duk ya hargitsa ni amma ga mamakin ta wannan maganar ta yi mata nauyi a baki, a ce ta gayawa Maman ta ita. Gaar ta bar bakin cikin ya kashe ta. Sai ta yi shiru, tana jin ciwon kalaman uwar. Da tace ta rako mata duniya wajen rashin iya tattalin miji! Da ballagazanci!! Ta ce har da dolanci !!! ***** ***** ***** un daga wannan ranar Mamma Jal an ta maida hankalin ta da lokacin ta kacokam! A kan gyaran tarbiyya da dabi u da addinin yar ta Amani. Gashi yau har Mukhtar yayi sati biyu da komawa Katsina, Jal an har girki tare suke yi da Amani don ta lura bata iya komai da ya shafi rayuwar mace a gidan aure ba. Kada girki ya ji labari. Hatta sallahr ta ta tsaya tana dubawa da gyarawa da saka Safwan ya dinga koya mata karatun Al qur ani kullum. Ba don bata san ranar komawar ta Katsina ba da a islamiyya zata saka ta. A hakan ma babu laifi don tana da kwakwalwa, tana daukar kananan surorin da Safwan ke kara mata kullum. Shakuwa mai tasanani ta shiga tsakanin Amani da kannen ta biyu wato Fajur da Safwan da mahaifiyar su da ke kokarin samar da kauna da shakuwa da hadin kai a tsakanin su. **** ***** **** KATSINA unda ya tafi bai kira Amani ba, ko sau daya, kai ko da kuskure, domin ya tarar da very tight schedules a kamfani da shagon ta, amma tabbas ya san yana kewar ta da rashin kunyar ta, kai har ma da fitsarar ta. Ya kan tun ranar su ta karshe with so much adoration Allah yayi mana hisabi ni da kai, sabida yadda kake cutar da ni da kuskure na! Sune kalaman ta da kullum yake yawan tunawa yayi murmushi. Masu tabbatar masa da cewa (for the first) tima tayi maganar da ta zo ta yi nadamar ta a rayuwa. Amma daga komawar sa Baba Idi har ma da Alhaji suka bude masa wuta kan sai sun dangana da iyayen sa ko danginsa don shima Baba Idi ya dage a kan hakan. Mukhtar kuma yafi son ya fara sulhunta Jal an da Alhaji tukunna kafin ya yarda su tafi Diffa, gabadaya har Mamma Jal an don dai ya kore curiousity din sa a kan cindon ta da na Ummami. Don haka ya gayawa Alhaji sakon Amani, na tana rokon su maida auren su shi da Maman ta. Alhaji Usman sai yayi dariya, yace a da can ma dana ke da cikakkiyar lafiya Jal an bata yarda ta zauna da ni ba sai a yanzu da nake da rabin jiki shanyayye, kuma ba zan iya sa ta haifar wasu yan ba? Dube ni a cikin wheelchair Mukhtar ya ji wani iri ya ce cikin tausayawa, ai Amani ta ce auren zuba ruwa a buta a kai bandaki da zuba ruwan wanka zaku yi. Ba sai don wannan kawai ake aure ba Alhaji, in ji ta . Alhaji bai san sanda ya bushe da dariya ba, ya ce ai ka sani Mukhtar ni bani da say, in dai a kan Jal an ne. Na bar komai a hannun ku kai da Amanin, idan har ta amince a hakan da nake ni ai zan fi kowa farin ciki A daren Mukhy ya yiwa Amani gajeren text messege , yana so ko yaya ya tsokane ta, inda yace. Shege ya zo gida lafiya, duk da baki nemi jin hakan ba. Alhaji ya amince da bukatar ki na maida auren sa da Mamma, idan har zaki yi masa yakin neman amincewar ta. Su Baba Idi zasu taho a maida auren . A kasan sakon sa ya rubuta; _Mai kama da shegu. Sanda sakon ya shigo wayar ta girki suke yi itada Fajur, don haka bata duba ba duk da ta ji alamar shigowar sa sai da suka kammala. Ta runtse idon ta kadan, a kan wannan kalma da ya kara ambata mata, ta yarda Mukhy, mutum ne mai tsananin riko, irin wadanda da wuya a cuce su su yafe, ba tare da sun rama fiye da abun da aka yi musu ba ko mafiyin sa, ko da zasu huce din ma kenan. A ranar ta nemi jin ta bakin Maman ta kan komawa mahaifin ta, ta ce for my sake Mammah! Ta hada hannayen su wuri guda tana rokon ta. Har da hawayen ta. A karshe Jal an ta amince zata komawa Baban Amani, albarkacin Amani da Mukhtar don su yi zaman aure na jinyar Alhaji, koko zaman auren zuba ruwa a buta da kai ruwan wanka kamar yadda Amani ta kira auren. Wata biyu bayan nan Mukhtar ya yiwa Baba Idirisu da su Kamilu da Baba Sahura shirin tahowa Kenema, shi kadai ya tsaya tare da Alhaji da kamfani, cikin kwana uku da zuwan su aka maida auren Ahaji da Jal an, farin cikin da Amani ke ciki ne yasa ita da kanta ta hada musu kayan su don su taho Katsina tare da su Baba Idi, wai biki zata yi wa Daddy da Mammah, biki na kece raini, hararar ta Jal an ta yi ta ce, ki fara shirin naki bikin dai, ni ba sa ar wasan ki bace Baba Idi dake wurin yace ai in suka isa Katsina ba zama zasu yi ba, mika ta wajen mijin ta zasu yi, zasu dunguma ne su wuce wajen iyayen sa a Diffa region, ta kasar Nijar. Kuma Mukhtar yace in sun tafi bazata dawo ba, sai ko da ganin gida Maganar sai ta tunowa Jal an da Yayar ta Aisata dake Nijar. To ai kamar a Diffa din ne ma dan aiken dake tsakanin su yace take aure. Tsakanin ta da Aisata sai aike, don bata taba fita daga gidan mijin ta ba tun ranar data shige shi. Ta sa a ranta zata nemi jin hakikanin inda take a Nijar din in sun je, bata dai tabbatar da inda take a can din ba don taba zuwa ta yi ba, zata nemo mutumin ya bata adireshin Aisata ko don ta yi wa Amani Uwa a can da jinin ta kuma uwar ta. **** **** **** a karamin shiri Mukhtar ke yi na isowar Maman su Jal an ba. Ya sa an fente gidan gabadaya da sabon farin fenti mai feshi, an shirya mata dakuna na alfarma da furnitures yan uban su. Sannan ya sa an shirya dakin Fajur kusa dana Amani, Safwan ma yasa na fidda masa daki daga waje kusa da na Kamilu. So gida ya zama full house, family house don hatta Baba Idrisu sun bashi dakin sauka a gidan duk lokacin da ya zo. Gidan Hon. Usman babban gida ne da ya lamushe dukiya mai yawa wajen ginawa a matsayin sa na Architectural Engineer, har gobe kuma kullum kara kyawun gidan ake da gyara shi yadda zai tafi daidai da zamani da duk wani sabon abun kawata da ya shigo da shi daga waje. Rakiya na ta hidimar dawowar uwar dakin ta, bata sama bata kasa don tabbatar da ta ajiye ma Amani komai na bukata, yadda suka saba. Ta ji labarin auren Amani da Mukhy a bakin Malam Tajudden tun kafin su dawo, tayi mamakin ta ita kadai ta bari. Yanzu kuwa Kamilu ya gaya mata har Babar Amani mahaifiya za a dawo don haka girke-girke na musamman ta yi musu, zuwa yamma kuwa sai taji dirin motocin da suka je debo su sun shigo, wato dai sun iso gidan lafiya. Gidan ya kaure da hayaniyar farin ciki, Mukhtar yana gidan sa yana barci bai san sun iso ba, don jiya kwana yayi da ma aikatan Alhaji ana meeting na amana, kan wanda zai jagoranci kamfanin Alhaji da gaskiya a cikin su tsofaffin ma aikatan Alhaji, sabida shi zai koma gida, bada jimawa ba. Bai kuma da niyyar dawowa. Boutique din Amani ya koma karkashin kulawar Kamilu kasancewar shima kasuwanci ya karanta. A karshe Mukhtar ya zabi Alhaji Badaru Matawalle wani tsohon ma aikacin kamfanin da sun fi shekara Talatin suna aiki tare da Alhaji, a shirya a bata, still dai an jure zaman tare na lokaci mai tsayi, an kuma san halin juna, Alh. Matawalle dan asalin Bindawa ne, shi Mukhtar ya baiwa kujerar sa karkashin saka hannun mutumin da Lauyoyin Alhaji, suka yi resolution kan za a cigaba da gudanar da ayyukan kamfani yadda aka saba bisa amana da gaskiya, Mukhtar ya ce ko yaya suka fahimci wani abu ya biyo baya na rashin gaskiya a kamfani, to kuwa zasu rufe kamfanin ne kawai. Aka yi komai a shari ance, sannan ya ce gobe zai ma Matawalle handing over na ofishin sa. Ba shi ya tashi daga barcin gajiyar da yake yi ba sai ana gab da kiran sallar maghriba. Don haka a gurguje ya shiga wanka yayi alwallah ya fito yana shiryawa a gaggauce, ya san yanzu su Amani sun dade da sauka. Ya rasa dalilin dokin da ke cin ran sa sai kace shi aka kawowa amarya ba Alhaji ba. Murmushi ya yiwa kan sa, wani abu da ba kasafai yake faruwa da shi ba, wato bai da yawan murmushi, kuma in yayin, shi kan sa ya san ba karamin kyau yake kara masa ba. Ya ce ma kan sa in haka ne ai shima yana da amaryar, sai dai tasa fitsararriya ce hamshakiyar shu uma mara kunya, ba irin ta Alhaji mai kirki da sanin ya kamata ba. Sanda yake fesa turaren sa watau Azzaro Visit bayan ya fito daga wanka, sai da wani farin cikin son ganin Amani ya darsu a ran sa. Yana duba wayar sa ya ga missed call din Alhaji dana Kamilu rututu, da sauri ya saka takalmi a kafar sa ya fita, bayan ya rufo kofar dakin da mukulli ya hau motar sa Bugatti wadda Alhaji neya bar masa ita zuwa gidan Alhajin, duk da ba nisa da nasa gidan tafiyar kafa ce kawai, ya kuma fi zuwa a kafan a yawancin lokuta, amma yau da yake cikin saurin isa gidan