← Book details Amani Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 22

Sashe 13

Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kika san bana so? Kin san yadda kukan mace ke kassara ni ya ji min ciwo a zuciya? Kin san ba abinda na tsana irin kuka a kunnuwa na? Kukan ma na mace, macen kuma matar aure na? Budar bakin Amani sai cewa ta yi ta ina nazama matar taka? Na dauka sai na karbi sadakin ka da hannu na da amincewa ta ne na zama matar taka? Koma ka tambayi Malamai, sadakin ka yana gun Baba Idi sai dai in shi ka aura. Idan mafarki kake to ka farka, ni Amani na fi karfin auren yaron gidan mu, matsiyaci irin ka kuma faqiri, sai zuciyar fir auna, me zai kai ni auren mutum mara asali da nasaba irin ka. Tunda ka zo gidan mu mun taba ganin wani naka? Ko beran masallaci bai taba zuwa wajen ka ya ce mana shi jinin ka bane ba, a hakan kake mafarkin ka aure ni? Ni da ke da gata na da arziki na da komai? Allah ya tsare ni. In mafarki kake Mr. Mukhtar ya kamata ka farka. Wa ya sani ko a bola a ka tsintoka? Dama an ce shegun ya shegen kyau ne da su...... Sai ya sakar mata gashin kan ta jikin sa yayi la asar bakidaya. Yau idan da ace ya taba furta cewa yana son Amani, da ya nemo kalaman sa duk inda suka shiga a kunne da kwakwalwar ta ya mayar da abin sa cikin cikin sa. Madallah da bai taba furtawa ba, sai ya yiwa kan sa murna da fatan alkhairi. Shin Alhaji ya san irin kalar gallafirar matar da ya aura masa mara ko kankanin tunani, ko sanin ya kamata? Wadda bata san darajar dan adam ba? Wadda babu humanity a zuciyar ta? Alhaji da kansa ya taba gaya masa Amani bata tauna magana in zata fade ta musamman in ran ta ya baci, kuma ba ruwan ta da lahanin da kalaman ta zasu yi wa mutum, amma duk da ya kwana da sanin hakan bai taba zaton zata iya budar baki ta ce masa shege ba. Ya koma gefen gado ya zauna dafe da kan sa yana maimaita inna lillahi wainna ilaihi rajioun . Ita da kan ta data fadi kalaman sai ta ji tana son mayar da su, ganin yadda suka taba shi sosai. To amma aka ce magana zarar bunu.... ta riga ta fita. Haka kawai ta dade tana kissimawa a ran ta Mukhy shege ne, shi yassa kyan sa yayi yawa, bata san kaikayin bakin da ya kai ta furtawa yau a gaban sa ba. Tafi alaqanta qaiqayin bakin nata da huce kan damin haushin kwana daki daya da Abdussalam ya sake hada su. Mukhtar ya dago idanun sa jazur, fuskar sa ma ta yi jazir abinki da farin mutum a cikin bacin rai, ya dubi Amani dake tsaye duk guilty ya lullube ta, zuwa yanzu ta daina kukan tabarar data ke yi masa. Ta kama bakin ta. Shi kam da son samu ne ya furta mata saki uku shine kawai zai huce. Amma sai ya tuno fuskar Alhaji Usman wadda rabin ta baya aiki, da jikin sa cikin wheelchair , da rokon da ya rika yi masa a kan yayi hakuri da Amani, abu ne da zai karasa shi lahira nan take idan ya ce masa ya saki Amani, saki har uku!. Ya shiga tuno tarin alkhairori Alhaji gare shi sai ya zama cikin dilemma na tunanin ya saki Amani ko a ah? A lokacin ita kuma sai ta ji tana so ta bashi hakuri, if possible, ta ce na maida kalamai na , ganin irin lahanin da suka yi masa, amma izzar ta da ego din ta suka hana ta. Sai ma tsaki data yi ta haye gadon ta bar shi nan zaune a gefen gadon, idanuwa sun kada, har tiriri suke, ta ja bargo abin ta har kan ta ta dukunkune jikin ta a ciki. A irin sake-saken da yake yi a yanzu sai ya ga ba abinda zai daidaita fushin da ke hankoro a kirjin sa, banda kwatar hakkin sa ta karfin tsiya a jikin Amani, ta hakan ne kadai zai huce abinda ta yi masa yanzun nan. Ya kuma goge rainin nan da take yi masa daga zuciya da kwakwalwar ta. Sai dai kuma, sai fuskar mahaifin sa ta gilma masa, wata kamilalliyar dattijiyar fuska mai cike da farin gemu da kamala, nannade cikin nadin larabawan Diffa, wanda ya rufe har rabin dogon karan hancin sa, ya tabbata mahaifin sa bai taba sakawa mace karfi a shimfida da sunan aure ba, wai don ya huce fushin sa daga tarin akuyanci da rikicin da suke masa a gida, (shi da ya tara su da yawa kenan ma), har ba adadi. Idan ya kasa hakuri da guda daya amanar ubangidan sa mai dimbin karamci a gare shi, wadda dama ubanta ma ya san halin ta, ya dauka ya bashi a haka, with good hope na zai iya taimaka masa su gyara halaye da dabi un ta, ashe kuwa ba zai iya kara guda ukun dake jiran sa a nan gaba ba, da kwarkwarori ma in ta kama, ya yi hakuri da su da halayen su kamar yadda mahaifin sa Issouffou Massaoudou ke yi da iyayen su mata ba. Yau shi Mukhtar tilon dan Issouffou Massaoudou mace mace ke ce ma shege sabida ta gan shi yana neman abinci a karkashin mahaifin ta!!! Life is not fair for him at all!!! Ko yace iyayen na sa su suka jawo masa!!! Zubewa ya yi a gefen Amani cikin kasala da mutuwar jiki, wadda zuwa lokacin ita har ta fara sakin minshari, sabida dadin barcin da ta samu nan take. Ko babu komai ta fadawa Mukhy abinda zai hanashi nashi baccin yau, itama huce bakin cikin kwana da shi daki guda again da suka hada baki shi da abokin Alhaji suka yi mata sanadin sa. Ga dakin wani dan akurki, gadon (6 by 4) wanda mutum biyu ba zasu iya kwanciya a kai ba tare da sun mannu da juna ba. Ga rashin na urar sanyaya daki sai fanka ta tsaye a daidai kan su. Mukhtar ya gayawa kan sa idan Amani ta kira shi shege shi ya jawo, sai bango ya tsage kadangare ke samun mashiga, abinda ta gani ne ko take tunani ne ta fada, Baban ta kuma bai mata adalci ba da ya bata wanda bata san asalin sa ba. Babu wani nasa da ya zo ya karba masa auren ta dole tayi masa gori har da mafi muni wato na shegantawa. Karo na farko da tunanin komawa gida ya zo wa Mukhy, ya ji ba abinda ya ke so irin ya bude ido ya gan shi a gaban iyayen sa da yan uwan sa. Ko da basu canza daga yadda ya san su ba. A kalla a yanzu ya san ciwon kan sa zai iya yi musu uzurin da a baya baya iya yi musu idan ya ji uzurin su daga bakin su. Wani irin gumi ya shiga yanko masa tun daga tsakar kan sa har zuwa yatsar kafar sa..... sai ka dauka ruwa aka kwara masa kwanon sha guda. Jik in sa ya hau rawa. Dai dai lokacin da maharbin ya harbi kurciyar dake kan bishiyar tsamiya, wadda ke rataye da kankanuwar jar laya a wuyan ta. **** ***** **** azzabi da masassara mai zafi ne ya taru ya rufe Mukhtar daga wannan lokacin, lokacin da ya mirgine ya kwanta a gadon cikin barin jiki da karkarwar sa bai sani ba. Sanyi ke kada shi ko ta ina, yana neman abun rufa, ga Amani ta janye bargon ita kadai ta cukuikuiye a cikin sa. Dan karfin da ya saura masa ba zai ishe shi kwatar bargon nan daga jikin Amani ba. Sai kawai ya kwanta ya kama ta ya kankame jikin sa yana bari da karkarwa, hakoran sa na haduwa da junan su, ji ka ke kaf-kaf-kaf Zafin zazzbin jikin sa sai da ya huda har cikin bargon nan, ya tadda fatar Amani, bayan kamar rabin awa da kwanciyar Mukhy a jikin ta, ba tun yau ba ita mutum ce mai nauyin barci sosai, hakan ne yasa har Mukhtar ya dade yana samun dumin jikin ta bata sani ba, ga hucin zazzabi dake fita daga hancin sa zuwa fuskar ta da bata rufe da bargon ba. Duk nauyin barcin da ke kan ta haka ta soma kokarin bude ido don ji take kamar an danne ta. Kamar numfashi na mata wuyar shaqa. Ilai kuwa da idon ta ya bude sosai, Mukhtar ne ta gani kankame da jikin ta cikin wani hali na numfarfashi tamkar ran sa na son fita. Idan ta ce bata tsorata ba, kuma bata wartsake nan take ba, ta san ta yi karya. Kokarin raba shi da jikin ta ta soma nan ta ji irin zafin da jikin nasa ya dauka. Kidimewa ta hanata daukar matakin da ya dace wato ta dauki wayar sa ta kira Faytoory, sai ta kama rawar jiki da kaduwa itama tana tunanin maganganun ta ne suka jefa shi a wannan halin. Tace na shiga uku ni Amina, shegen baki na zai kashe mutum! Sai ta fara hawaye tana fadin na mayar da kalamai na, can cikin ciki na Mukhtar, wallahi I don t really mean it Ina! Mukhy, bai san tana yi ba don zuwa lokacin ya gama zama unconscious, wato ya suma gabadaya. Fitsari ya kwacewa Amani daga tsaye ta sake shi piiiiiii, ta nufi kofa da gudu ta zare sakata tayi waje, sai ta rasa inda zata nufa. Kofa ta gani a rufe wadda tayi cikin gidan ta hau bugawa da karfi. An yi sa a Abdussalam idon sa biyu sallah ma yake yi da yake Malamin addini ne sosai. Amani saboda rudewa ce masa ta yi ka zo don Allah ba ya motsi, wallahi ba da niyya na fada ba, ba ni na kashe shi ba, ko da bana masa so na soyayya, ba zan kashe shi ba, ban ma san yadda ake kashe mutum ba Kafin ta rufe bakin ta Abdussalam ya kai kofar dakin. Ya ciccibo Mukhtar daga gadon ya kwantar a tsakar dakin, sannan ya rike tsintsiyar hannun sa ya tabbatar jijiyar tana motsawa. Kallo daya ya yi masa ya
Chapter 13 · 0% Book details