Sashe 3
Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kafiya da taurin kan ta, wai shi mace ke gudu! Macen ma wadda in ba don darajar mahaifin ta ba ko kallo bata ishe shi ba, bai ji ya damu da inda ta tafi ba don ya san dai ba zata yi nisa ba, tunda bata da adireshin Maman nata, yana ji a jikin sa Balogun Sunday yaudarar ta kawai yayi, yafi damuwa da halin da Alhaji zai shiga in aka gaya masa cewa ta gudu! Ya dade tsaye cikin kunan rai, ya tambayi kan sa ko meye aibun sa haka da Amani ke masa irin wannan kiyayyar, bayan na kasancewar sa yaron Baban ta kamar yadda take yawan ikirari??? **** **** **** THE RUNAWAY BRIDE mani Faskari, jingine jikin tagar motar haya ta Sharon mai tafiya garin Bauchi, ta yi kuka tayi kuka a cikin mota har ta godewa Allah. Da wuya wani abu ya sanya Amani kuka, mace ce mai dakakkiyar zuciya kuma jajirtacciya mai jin cewa ko me namiji zai iya itama zata iya, amma yau da ta tabbatar da igiyar auren Mukhtar ta hau kan ta, daga bakin da ba zai mata karya ba, igiyar kuma ba ta kowa ba ta Mukhtar Diffa, babu shakka an shammace ta, domin bata taba kawowa haka da wurwuri Daddy zai yi wanan danyen hukuncin ba, ta dauka ko zai yin sai ya nemo dangin Mukhtar tukunna wanda kafin nan ita ta yi kokari ta gudu gun Innar ta. A wannan lokacin she cannot control her tears domin ji tayi tagama faduwa kasa warwas! Babu class dinnan, ta kare mata, kuma yanzu bata fi sauran mata ba tunda ta kare a yaron Baban ta. Kenan sunan TAFISU ya bar ta yanzu, bai dace da ita ba yanzu, duk sauran mata sun fi ta aji, ajin ta ya fadi! Tunda a karshe duk gatan nata da ego din ta da Daddy ke fadi ta kare a bada sadakar auren ta ga mijin da zata kira yaron gidan su, mara asali mara nasaba da ko tushen sa ba a sani ba. Tana da tabbacin Daddy sadakar ta ya baiwa Mukhy, tana da tabbacin sadakin ta ma Daddy ne ya biya, don Mukhy ta tabbata ba zai taba cewa yana son ta ba ko da yana son ta din, balle zata iya rantsuwa ta ci laya kan cewa yadda bata kaunar sa haka shima baya kaunar ta, ko magana da yake mata a kan dole ne bisa tirsasawar Daddy da ko kallo bazata ishe shi ba a dai wannan girman kan nasa da rashin son raini, kamar yadda itama koda kuskure bata taba jin son sa a ranta ba sai jin zafin sa, na kwace mata soyayyar mahaifin ta da yayi, tana bakin cikin wannan abu, tana kishin Mukhy for that, tana jin haushin wannan matsayi da yake da shi a gun Alhaji mai girman da ya kamo nata ko tace ya zarta nata yanzu a wurin mahaifin ta Hon. Usman. Babban abunda ke sa ta kara tsanar Mukhy shi ne rashin walwalar sa, kamewar sa mai hanawa ka tunkare shi da maganar da ka yi niyya, ko ta shirya ci masa mutunci ko rama rashin mutuncin da yake mata kallo daya zai yi mata ta ji bazata iya ba, a takaice yanayin rayuwar sa mai matukar aji da yanayin halittar sa na rashin daukar wargi ko raini yana ci mata tuwo a kwarya, yana hanawa ta taka shi a duk sanda ta so. A wurin ta wadannan halaye ne da bata so a Da namiji, domin zasu hana ta jan zaren ta yadda take so a gun mijin auren ta. Allah da ya halicce ta yayi ta mutum ce mai tsananin izzah da fadin rai, wato mai tsananin son a bata girma, mai son mulkar mutane a karkashin ta, ta yadda in sun ganta har suyi ta bare-baren jiki don cika umarnin ta, a duniyar ta mutum ce ita mai son kowa ya zauna a kasan ta, tana juyawa tana mulki yadda take so, tana kuma taka duk wanda ya shiga hancinta. Tun tasowar ta a haka ta taso da wannan mummunar dabi a, tunda a kan ta Daddyn ta ya raine ta, cewa ta fi kowa gata, ta fi kowa iko, wato ta riga ta taso a matsayin mutum mai juya mutane a karkashin ta da basu order su bi, sai ta ke fatan hakan ya dore har a gidan auren ta, har kuma karshen rayuwar ta wato shima mijin duk da ta aura ya ya zama tana juya shi kamar hakan. Amma auren Mukhtar ta tabbata babu shakka sai dai ita ta koma kasan sa, a irin halaye da dabi un sa da ta dade da sani, wanda wannan wani abu ne da bazata taba yarda da shi ba. Daddy ya gama kaskanta ta, don haka ta yanke shawarar barin su shi da Mukhtar din nasa, ta bar musu gidan ta bar musu garin, in ya so Daddy yayi zuciya ya haifawa Mukhtar din sa wata yar a gobe ya aura masa. Tunda ya asirce shi har yana fadin bai iya surukuntaka da kowa sai shi. Ita wallahi sau dubu gara mata Alhaji Sadi akan Mukhy, ko babu komai zata juya shi yadda take so, musamman data fahimci yadda ya gama macewa a son ta, zai yi wuya tasa kara ya tsallake duk yawan shekarun nan nasa. Sannan zai yi ta tarairayar ta ne irin na tsohon da ya dau yarinya, amma Mukhtar??? Wani kukan ya kara kwace ma Amani, ta kifa kai a kan tafukan ta tana ta yi ba kakkautawa. Wato duk wasu plans din ta na gidan aure Daddy ya rusa mata su, ta hanyar aura mata wanda ya fita izza. Mujin da yake da tabbacin bazata iya mulka ba. Iyaka tunanin ta bata ga ina ya dace ta je ba, in ta shiga duniya saboda bakin cikin Mukhtar ita tayi asara domin kuwa sunan ta ne zai koma karuwa hakan kuma ba zai hana Mukhy rayuwar sa cikin sukuni da sakewa tare da mahaifin ta ba, kamar yadda yake yi tana nan, watakila ma har Daddy ya nema masa wata yar mutuncin ya aura masa, ita su manta da ita da rayuwar ta gabadaya, su shafe babin ta, wannan itace babbar nasarar da Mukhtar zai yi a kan ta da zata dauwama tana haunting din ta, ta dauwama cikin cizon yatsa ba tare da ta iya ramawa ba. Don haka ta yanke shawarar tafiya Bauchi gun Hamidah. Kafin ta samu damar da zata wuce Sierra Leone daga Bauchin, ko a kafa ko a kan fiffiken ta, zata nemo Innar ta. Duk da ta san Hamida bazata taba bin bayan ta ba, cewa zata yi a nemi zabin Allah a yi wa iyaye biyayya. Ta tabbata wadannan sune kalaman Hamidah da basa taba canzawa daga haka. Tuni ta haddace su har bata son kari. Zata iya yi wa Daddy kowacce irin biyayya amma banda ta auren kaskanci irin wannan da ya yi mata, babu kaskacin daya wuce mata wannan a duniya, duk mazan duniya a ce ta rasa miji na kece raini kamar yadda take macen kece raini sai Mukhy, wato yaron sa da tafi tsana a duniya a bisa dalilai da hujjojin ta wadanda take ganin sun isa hana ta karbar wannan auren ko me Daddy zai yi mata a kan sa kuwa. Sai da tafiya ta mika sosai, suka yi wa shiyyar garin Katsina fintinkau sannan ta gaji da kukan, ta fiddo hankaci ta share fuskar ta, ta fyace hancin ta sannan ta dauko wayar ta data kashe ta kunna. Kamar jira wayar take a kunna ta, sai ga kiran Hamida Balewa ya shigo. Ta yi ajiyar zuciya, ta sani Hamidah is always there for her whenever she needs her, duk da basu da ra ayi guda a kan komai, amma a kalla tana sauraron ta attentively tana taya ta damuwa da damuwar ta, in abin kuka ya sameta suna kokawa tare, in na bakin ciki ne ma suna yi tare, kuma tana bata shelter a gidan su a duk sanda ta bukata, da shawarwari masu inganci duk da ba duka take dauka ba, kafin ta daga wayar muryar ta duk ta dusashe don kuka. Hamidah tace Sahibah kina ina? Gani a gidan ku, maigadin ku na fadin baku nan duka gidan kun yi tafiya, yanzu ina zan same ki? Da dusashshiyar muryar ta data ci kuka ta koshi ta ce, Hamdy, mun yi sabani toh, ina hanyar Bauchi yanzu haka nima, wajen ki na nufa, don bani da wajen zuwa Ta fashe da kuka. Hamidah na jin haka ta fahimci komai, ko dai an daura, ko ana gab da daurawa shine ta gudo. Alright Sahibah, ki isa Bauchi lafiya, zan yi waya da Mama yanzu a gyara miki daki na don watakila ki rigani isa, zan sa direba ya juyo da ni Bauchi nima yanzu duk da na gaji, amma ba zan kwana a ko ina ba tunda ba kya nan gara in juyo, tafiyar dare ce dai na san ta same mu Suka aje wayar a tare. Sannan Hamida ta kira Mahaifiyar ta Hajiya Muna ta gaya mata batun zuwan Amani, amma bata gaya mata ko a kan menene ba, mutum ce mai kiyaye sirrin wanda ya amince mata kwarai da gaske, ta roki Maman ta Haj. Muna kan ta lallashi Amani ta ci abinci tayi wanka ta kwanta ta huta kan ta iso. Ta kuma ce, don Allah Mama a nemi Panadol a bata ta sha kafin ta kwanta Sai dare suka shiga Bauchi, suna ta waya da Hamida, ita tasa direban Baban ta ya zo tasha ya dauki Amani zuwa gidan su dake unguwar Fati Mu azu. Har dakin Hamidah mai aiki ta shiga da kayan Amani bisa umarin Hajiyar Hamidah. Sannan aka kaita falon Haj. Muna. Hajiya Muna ba tun yau ta san Amani ba, da irin amintakar da ke tsakanin ta da Hamidah tun suna sakadire a Ulul Albaab Science Secondary School Katsina suke tare, ta dubi kyakkyawar fuskar Amani ta ga duk ta yi zuru-zuru idon ta ya kode don kuka tayi wujiga wujiga da wahalar zaman motar haya don bata saba ba, nan take ta gane ba zuwan arziki Amani ta yi ba wannan karon kamar yadda