Sashe 14
Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gane halin da yake ciki wato; sihiri mai karfi ke fita daga jikin sa. Ya ce da Amani ta shiga dakin da ta ga ya fito ta duba bayan kofar dakin zata ga kwarya ta dauko masa, zata ganta da ruwan ganyen magarya a ciki, da gudu ta je ta kawo, ya karanta wasu kebantattun surori da ta awizai na karya sihiri ya tofa a ciki, sannan ya ce ta taimaka masa ya cirewa Mukhtar riga. In ka ga bare-bare a gurin Amani wanda hannnun ta ke yi yayin cirewa Mukhy riga kamar tsohuwa yar shekara casa in, tana kici-kicin cirewa Mukhy riga, tana kauda kai cikin jin kunya da faduwar gaba, kamar ta ce kasar ta tsage ta shige, kafin ta kalli kirjin sa mai cike da lallausar gargasa, baka wuluk, irin ta gashin kan sa, haka ta cire rigar ta jefar, ta koma can gefen su ta rufe ido tana ta tuba, na tuba ya Ubangiji na tuba! Astagfirullah kuwa a jejjere haka ta hau jero ta ta kai sau hamsin, don ita gabadaya ta baiwa kan ta laifin ta ne, muggan maganganun ta ne suka jefa Mukhtar a wannan halin na mutu kwakwai, rai kwakwai. Abdussalam ya shafe duka jikin sa da ruwan maganin nan, har fuskar sa da gashin kan sa, ya bar shi daga shi sai short nicker da ke jikin sa, sannan ya maida shi gadon ya ja bargon ya rufe shi da shi, yana kallon yadda Mukhtar ya bude ido a hankali ya kuma mayar ya rufe, alamar barci mai nauyi yayi gaba da shi. Fatar bakin sa dake motsawa da ace zaka fahimta, ka kuma san abida ke zuciyar sa, zaka gane sunan garin su yake ambata watau. DIFFA......DIFFA.......DIFFA! (With extreme nostalgia). Daga baya bakin ma ya daina motsin kiran Diffan, ya yi shiru, ya mike sosai a cikin bargon don barcin sa yayi nisa. Faytoory ya maida duban sa ga takurarriya mai barin jiki, Amani, yace kada ki tashe shi sai ya tashi don kan sa, hakika akwai sammu a jikin sa wanda nake da tabbacin yanzu, ya fita Amani ta dago a zabure, tana tambayar Faytoory menene sammu? Ya ce sihiri iyakar tsorata Amani ta tsorata, don ta san ba ka da mai yi maka wannan sai makiyi, to shi kuwa Mukhtar da ko aboki bai da shi a Katsina bayan Alhaji, wa zai yi masa sihirin? Ta damu kwarai da jin wannan zance, don tana ganin rashin farfadowar sa da safe a kan lokaci zai janyo mata tsaiko ko wani jinkirin na isa ga Kenema. Ba lafiyar sa ce ta dameta ba. Allah cikin ikon sa ma da Asubah da kan sa ya tashi ya shiga toilet ya yi alwallah, sai da ya fito ya lura da ita a dai dai kafar gadon tana gyangyadi, da alama a haka ta kwana a zaune. Ya shiga mamaki yana son tuno abubuwan da suka faru daren jiya ganin barci take amma tana hawaye, amma kadan yake iya tunawa. Yasa kafa ya shure ta ya ce dallah malama ki tashi ki sallah Amani ta bude ido a firgice, ta dube shi tana kulubi, tana kunkunin cewa in gama jinyar ka, in kwana a zaune saboda kai, amma ka ce min Dalla Malama, wannan rashin godiya har ina! Amma kadan da aikin dan adam, ka yi masa rana ya yi maka dare. Ka yi da yar halak, cikin Usmanu da Jal Dan murmushi Mukhtar ya yi, ya daga hannu zai tada sallah sai ya fasa ya ce in jira ki ki yi alwalar muyi jam i tare? Ko har yanzu kina kan bakan ki na bazaki bi limancin shege ba? Idon ta ya firfito waje, ta dauka ya manta sakamakon jiya ya fita daga hayyacin sa, ta dauka zancen ya wuce, ashe babu abinda ya goge daga cikin kan sa, ko da ya kwana ba cikin hayyacin nasa ba. Wannan karon ba musu ta dauro awallar ta fito ta bi shi jam in, don ta tsorata da furucin sa, wanda yanzu cikin kwanciyar hankali yayi shi babu bacin rai ko kankani a tare da shi, sai da ya fara da raka atainil fajr, sannan suka bada faralin asubahi tare, ya nuna mata yadda ake zaman tahiya na sosai ba irin yadda take yi ba shakwar-kwar a kan kafar ta ba, ya kuma ce ta yi masa tahiyar ta a fili ya ji. Nan ne Amani ta zumbura baki ta ce ai ban ga shaidar zaman ka Alaramma ba tukunna, na dai ga shaidar karatun ka a kan kasuwanci, wadda kuma a kan sa na san ka. Ka bar ni da sallah ta in bar ka da halin ka kai ma tunda dai ba kabarin mu daya ba Mukhtar ya kasa cewa komai, don Amani ta zarce da tunanin sa a rashin hankali. Gashi kan sa yana dan sara masa kadan-kadan, ba ya son yawan magana, sai ya jingina da bango yana jan carbin sa, yana cewa. Ya Allah ka taya ni, da abinda ka san bazan iya ba a kan yarinyar nan, Allah ka shirya ta, idan mai shiryuwa ce, idan ba mai shiryuwa ba ce Allah ka yi min musanye da mace tagari mafi alkhairi a kan ta. Ka shaida ya Ubangiji ban kasance butulu ba, mai manta alkhairi, shi yasa na ke hakuri da halayen ta. Ka horemin duk wani nau i na hakuri da fin karfin zuciya, daga cikin wanda ka baiwa Annabawan Ka tsarkaka Wai sai taji addu ar tasa bata yi mata dadi ba, (idan ba mai shiryuwa ba ce Allah ya musanya masa da mafi alkhairin ta). Me Mukhtar yake nufi da wannn muguwar addu ar a gare ta? Yana nufin Allah ya bashi wata macen data fi ki alkhairi, wadda bazata dinga cutar da shi daga kalaman bakin ta marassa dadi ba Zuciyar ta tayi gaggawar bata amsa. To ta Allah ba taka ba, in ma mutuwa kake roka min don ka auri wata, saboda kana jin nauyin Alhaji in ina raye! Zai shige toilet domin yin wanka ya dan dakata jin abinda take fada, ashe kin san da auren? Ai na dauka ko sadakina baki karba ba Baba Idi kika barwa, Baba Idi na aura? Ta fuske kamar ba da ita yake ba, ya gyada ya shiga wankan sa. Kafin karfe shiddan da Abdussalam ya deba musu sun kintsa suna jiran sa, ji take kamar tayi tsuntsuwa ta bar su, don ta ga kamar su duka yanga suke mata. Ko da Faytoori ya zo ma sai da ya bashi magani cike da kokon duma ya sha sosai, ya bashi kullin wasu a leda ya ce ya jika kullum ya sha ya kuma yi wanka. Da Mukhtar ya nemi ba asi sai kawai ya ce masa na fahimci baka da lafiya ne, wannan kuma ba komai bane tsari ne da dafa i irin nawa na baka. A motar Abdussalam suka wuce zuwa filin jirgin kasa, a nan ya bar motar tasa suka hau jirgin kasa mai shiga har cikin Kenema Province. Zuciyar Amani sai tsalle take a cikin kirjin ta tana kissima ko wacce irin tarba Mamanta Jal an zata yi mata? Ko zata yarda cewa itama yar ta ce da ta haifa tunda an ce ta samu wasu yan bayan ita??? **** **** **** KENEMA PROVINCE, SIERRA LEONE idan da suka nufa matsakaicin gida ne da bai cika girma ba, akwai karamin gate wanda mota zata iya shiga har cikin sa. Taxi din data dauko su daga fili jirgin kasa zuwa gidan ta ajiye su a kofar karamin gate din. Suka karasa, Faytoory ya danna kararrawa yana gaya musu nan ne gidan da Jal an ke rayuwa, tun bayan rasuwar mijin ta uban yaranta, ta ci gadon wannan kyakkyawan karamin gidan ita da yan ta. Fajur, baki ji ana danna kararrawa bane? In ji Yayan ta Safwan wanda kan sa ke kan allon kwamfutar bisa cinya (laptop). Rubutu nake yi, bana son tashi . Ta bashi amsa cikin hausar su da ba sosai take fita ba, amma a junan su suna yawan yin ta, saboda yaren su na Krio da ya mamayi harshen su wanda shine Lingua Franca na kasar, musamman a lardin su na Kenema. Hajiya Jal an data fito daga kitchen sai kawai ta karasa ta bude kofar da kan ta. Don ta san halin Fajur da kiwa. Tunda tace hakan bazata tashi a kan lokaci ba. Don ta san kiwa irin ta Fajur, zata bar baki ne su yi ta tsayuwa sai ta mula don kan ta zata tashi ta bude. Fara, doguwa kuma siririyar yarinyar da ke tsaye a wurin ta bi da kallo, doguwa sambaleliya mai kira da tsayin matan Saliyo, (a perfect replica of herself) idan ba idon ta ne ke mata gizo irin wanda ya saba yi mata ba, exactly kamar yadda take a tsaye dirarriya shekaru ashirin da daya a baya. Tana son tuno inda ta san ta amma ta kasa. Sai dai feeling of familiarity da wani maternal sensation dake kara mamayar ta. Kamar ta san ta a wani wajen! Kamar ta dade da sani da sabawa da yarinyar da ke tsayen haka ta ji a ran ta. Amma iyaka tunanin ta bata iya ta tuno a ina ta san ta din ba. Amani ta jingina da kofa tana kallon Maman ta da bata bukatar a yi mata karin bayani, Jal an ce, Jal an din Daddy Usman, wadda ta hana shi iya rayuwa da kowacce mace sabida wannan kyawu nata da haiba da ba duk mata Allah ya yi wa ba, gata nan da kuruciyar ta har yau (at the age of fourty), wasu hawayen farin ciki suka soma tsera a kan fararen kundukukin ta. A hankali bakin ta dake rawa ya motsa cikin furta haruffan. Ma.....Ma... Mama na! an, wadda ta zama kamar an soma rewinding casette a cikin kan ta, ta soma zaro idanun ta sosai, kafin ta mika mata hannu ita kuma ta tafi da gudu ta shige. Suka rungume juna kamar bazasu saki ba suka saki kuka a tare mai sauti. Mukhtar da Faytoory sai suka koma daga gefe cikin tausayawa, Mukhtar ya ji hawaye na son tsatstsafo masa domin sai ya ji wannan rungumar inama shi Ummami ta yi wa