Sashe 8
Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kisisina irin na ya mata sai dolanci. To cigaba da dolancin ki, amma ki kama shi ta nan ta nuna can kasan Amani Hamida bata san sanda dariya ta kubuce mata ba don ta lura Amani kallon Haj. Muna kawai take tana cewa toh! amma kwata-kwata bata san inda zantukan Hajiyar suka dosa ba, ta dai karba ta aje ta kuma yi godiya. Amma ta ce ba zata iya cin komai a ciki ba yanzu sabida tana jin yunwa. Hajiyata sa aka kawo musu abinci suka karya amma Hajiyar na fita ta tattara magungunan ta mayar a ledar su. Ta cewa Hamidah "in kin gama dariyar muguntar taki sai ki je ki gaya masa na shirya . Hamida ta ce yar aiken ki ko? To da mecece? Hamida sai ta dauki wayar Amani ta danna ma Mukhtar kira ta na cewa ki ji tsoron Allah Amani, mijin naki ne Dirty Human Being? Smart Ass, Bad Egg. Ai ko karen gidan ku bakya kira da wadannan sunan ba balle mutum dan adam Ita dai bata ce komai ba amma ta sa a ranta zata canza sunan koda ba da wani sunan mai ma ana ba, amma dai zata canza wannan din, ganin yadda Hamidah ke Magana a kai kamar zata yi kuka. Hakan yasa ta tabbatar bata son sunan ga Mukhtar. Ko yaya ne tana ragawa Hamidah saboda duk tijararta ta san Hamida Balewa mai kaunar ta ce. Mukhtar na cikin sanya links din hannun rigar da ya sanya ta ash colour getzner ya ga na kiran sa, dauke kai yayi kamar kada ya daga don ya san arziki ba zai sa Amani kiran sa ba. Abu daya yasa shi amsawa ganin lokacin tafiyar su filin jirgi yayi. Don haka ya amsa, amma ba tare da ya ce uffan ba. Sai ya ji Hamidah ce, ta ce sun gama shiryawa kuma direba yana bakin entrance na masaukin sa da mota bakar land cruiser zasu raka su har filin jirgi. Mukhtar sai ya samu kan sa da cewa Hamidah madallah da karamcin ki. Madallah da kawa irin ki. Allah ya baki miji na gari kema Ki yi min godiya wajen Hajiya mun gode sosai, da zumunci, Alhaji ya ce a yi muku godiya". Zuciyar Hamidah ta cika da jin dadin wadannan kalamai na Mukhtar, sai ta ji wani karfin guiwa ya shige ta na son kara taimakawa aminiyar ta ta zauna da wannan mutum da babu wada ya taba shiga ran ta kamar sa. Hakika Mukhtar Diffa, yana da charisma ta farin jini a duk inda ya shiga, ba ga manya ba ba ga yara ba. Duk wanda wata kankanuwar mu amala ta hada shi da shi sai ya so shi, ya kuma bar shi da begen son cigaba da alaqa da shi idan ya bar wajen. Har dakin Hajiya Muna Hamida ta raka Amani ta yi mata sallama daga nan suka wuce ma adanar motocin gidan. Tana janye da jakar Amani. Tuni Mukhtar direban ya bude masa mota ya shiga gidan gaba ya zauna yana jiran fitowar su, yana yi yana duba agogon fatar dake daure damtsen hannun sa samfurin RADO. Da suka karaso ta cikin farin glasses din da ke idon sa wanda ya makala shi saman dogon karan hancin sa ya hango Amani tana tahowa, da gantalallen mayafin da ta yafa, tafiyar nan tata kamar ta macen Dawisu bai canza ba, duk da cewa zuciyar ta da kamannin ta sun canza zuwa na bacin rai zallah. A hakan kuma sai tayi wani irin kyau ba dan kadan ba. amma mayafin da ta yafa wanda saman kirjin ta kawai ya lullube ya bakanta masa rai. Haka ya shanye abin a ran sa albarkacin direba da Hamidah. Suka shiga baya su biyun ita da Hamidah direba ya saka jakar kayan ta a boot kusa da jakar Mukhtar, sannan ya shiga mazaunin sa ya ja motar suka fita daga gidan su Hamidah. Sai da suka hau kwalta sosai Hamidah ta gaida Mukhtar, kamar ba zai amsa ba sai kuma ya amsa din, har ya ce mata "yaya fama da bakuwa?" Sai ta yi murmushi ta ce ai na saba da wannan bakuwar tawa mai rigima, mai giggiwa . Ta mudubin motar Amani da Mukhtar suka hada ido unexpectedly ta sakar masa harara, bai yi kasa a guiwa ba wajen maida mata da wadda tafi tata zafi. Ya kuma maida kan sa bisa titi. Hamida tace don Allah Mr. Mukhtar da kun sauka ku kira ni in tabbbatar kun sauka lafiya . Ya ce "in sha Allah". Duk Amani na jin su, amma ko kallon su bata kara yi ba. Sai haushin Hamidah da ya kara cika ta. Sun tarar jirgin da zasu hau zuwa Lagos har ya kusa gama lodi, don haka a gurguje suka yi sallama da Hamidah ta bashi jakar Amani a hannun sa, ya hada da tashi yana turawa Amani na bin shi a baya, yana cewa a ran sa yau shi Mukhtar ne da dakon kaya, Alhaji ya ce yayi komai don ya lallaba ta, amma kuwa dakon kaya ai is frustrating, musamman ga namiji kamar sa, to amma ita yanzu din iyalin sa ce. Annabi SAW kuma yayi umarni da a tausayawa mata, dattijai da kananan yara, a agaza musu. But duk da haka yaji abin weird a gare shi. Seat din shi a cikin jirgin kusa da nata ne, tana daga jikin taga a takure yana gefen ta. Amani tana ji ana a daura belt jirgi zai tashi amma taki daurawa. Ba don tana da burin ganin Innar ta ba, kafin Allah ya dau ran ta da ta roki Allah jirgin ya fado duk su mace da dai ta zauna da shi har abada a matsayin mijin ta uban yan ta. Jirgin Max Air ya daga da su, Mukhtar sai ya saka hannu a bayan kwibin ta yana fastening mata belt din, ko babu komai diyar Alhaji ce shi kuma servant din Alhaji ne, don haka ba faduwa bane don ya hidimta mata a dalilin Alhaji Usman Faskari ne, jirgin bai dire su a ko'ina ba cikin dan kankanin lokaci sa a birnin Ikko. Da suka sauka shi ya dauko kayan su again suka fito daga terminal, mai taxi ya zo gaban su yana tambayar ina zasu je? Mukhtar sai yace masa any nearest good hotel . Amani bata ji ba, don a lokacin tana waya ne da Hamidah tana gaya mata gasu a Ikko, amma bata ga an ce a tsaya a shiga jirgin Freetown ba, Hamida ta fashe da dariya ta ce to kika sani ko jirgin yamma ne ko na dare? Ta ce, bar zancen wasa Hamidah, kina gani fa ya tsayar da taxi, gidan wa zamu je?" Hamidah ta kasa tsayar da dariyar ta ta ce "ki fidda ni a lamarin ki, tunda babu arziki a ciki, naga alama baki san Annabi ya faku ba, ina laifinsa ya baro komai nasa da ayyukan sa da Alhajin sa, don ya dangana ki da Maman ki?" Amani ta ce "to ni na saka shi? Ban ce a bar ni a ga iyawa ta ba? ban ce a bar ni zan kai kaina ba? Kuma in jirgin yamma ne zamu shiga ba waiting lounge zamu je mu zauna ba? Hamidah ta ce. "Ki tambaye shi mana da kan ki ina zaku je din? Me yasa za a yi transit? Ni Hamida ina nan Bauchi ina na san me kuke ciki ke da mijin ki a birnin Ikko? Dole ta kyale Hamidah don daga karshe ma ta kashe wayar ta daga gama fadin hakan hakan, bata so Mukhtar ya san da ita Amani take waya kada ya dauka ko da saka hannun ta a rashin mutuncin da Amani ke yi masa, fatan ta Allah yasa wannan tafiya ta zama silar shiryawar su da kuma sanadin alkhairori a cikin auren su. Already mai taxi ya saka kayan su a bayan motar, ya budewa Mukhtar gidan baya ya shiga. Hajiyar tsayawa tayi kikam tana jiran karin bayani na inda za a je daga gare sa. Amma bata ga alamar Mukhy na da niyyar yi mata bayanin komai ba, sai ma wata muguwar harara da Mukhtar din ya sakar mata, wadda ita kan ta ma amsa ce na cewa ba bayanin da zata samu daga bakin sa. Zata yi magana ya ce a fusace, idan kika sake kika tambaye ni ina zamu je? Zan ce miki sayar da kan ki zan yi a Ikko malama. Don kan naki zai yi tsada, kamar yadda kike yarinya mai tsada, na tabbata zai isheni in ja jarin da zan yi kudi, in tashi daga matsayin yaron Baban ki, ko kya daina raina ni Sakatoto ta yi da baki tana kallon sa. Kafin ta yi aune taji ya fizgi hannun ta ya saka ta a bayan motar ya rufe. Shi kuma direba bai bata lokaci ba ya ja motar. Hotel din dake manne da Lagos International Airport ya kaisu wa to Legend Hotel . Mukhtar ya sallame shi da kudin da suka zarta abinda ya bukata, Amani ta zauna na tsayin lokaci a cikin motar, ta kasa fitowa daga motar nan, kai ko kwakkwaran motsi ta kasa, ta rasa inda zata saka kan ta ta ji dadi a wannan lokacin. Sai wani irin kokawa take da numfashin ta saboda bakin ciki. Saboda (this will be the first day) da zata kebe da namiji, kuma mai amsa sunan mijin ta a muhalli guda, sannan wai a ce ba kowa bane mijin face MOUKHTAR DIFFA . Wani kwayan mutum guda daya da duk duniya babu wanda ta ke wa kallon bai isa ba, kallon abnormal human being , kuma matsala ga farin cikin ta irin sa. Ta tsani halayyar sa, girman kan sa da charismatic personality din sa, ta raina shi kamar yadda ta raina Karen kofar gidan su, tana ganin sa a ba komai ba, face yaron gidan su, mai hidimtawa Alhajin ta don samun na abinci, wanda karfi da yaji ya kwace mata mahaifi, ya shiga tsakanin soyayyar dake tsakanin ta da mahaifin ta, soyayya mai asali da tushe wadda Alhaji ke yi mata. Zuwan Mukhtar cikin rayuwar su ya canza wannan. Ya sauya rayuwar gidan su gabadaya, ya sauya mata mahaifi da