Sashe 15
Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
, ya tuno tasa Ummamin, yau shekaru kusan goma sha biyar kenan rabon sa da ita. Yana ji Faytoory na cewa Amani ta cika ta haka a yayin da shikuma yake tsane hawayen sa da bayan hannun sa. Mama Jal an cikin jin kunya ta janye jikin ta daga na Amani, tace musu barka da zuwa ku shigo daga ciki Safwan da Fajur, suka mike suna kallon su da bakunta a idanun su, har falon ta ta yi ma Mukhtar da Faytoory iznin shiga, jikin ta har bari yake, sam ta manta babu mayafi a jikin ta domin jini ya gama bayyana kan sa, ya gaya mata yar ta ce ta Alhaji Usman Faskari ta biyo ta. Dama ta riga ta sani ko ba dade ko bajima zata zo gare ta, in har tana raye. Shi yasa bata taba damun kanta a kan ta ba, tunda dama babu shakuwa ta shayarwa a tsakanin su. Amma lokaci lokaci ta kan tuna cute fuskar jaririyar mai tsananin kama da ita, wadda bata dauko munin mahaifin ta ba ko a farce, ta kuma tambayi kan ta sau tari ko ta rayu? Zafafan hawaye ne suka zubo mata tana kallon Amani, wadda har zuwa lokacin kukan farin ciki take yi ta hada kai da bango. Mukhtar ya dubi Jal an sosai da tsoro da mamaki domin yatsan ta na karshe mai cindo da ya dauki hankalin sa a duka hannyen ta, da wasu attributes na ta da yawa, musamman data juya baya tana tafiya takun ta a kan duga dugai irin na Ummami, duk da kai tsaye baza a ce tana kama da Ummami a fuska ba, amma a wulge suna kama din, musamman idanun ta da dirin jikinta mai kauri ba irin na Amani dan shalaf ba, ga kuma cindon nan guda biyu dake hannun Ummami a nata hannuwan duka biyu hagu da dama itama. He was shocked! Truely shocked! Amma wace hujja gare shi na cewa Jal an jinin Ummami ce? Shi kan sa bai san komai akan Ummami ba, ko kasar data fito bai sani ba, babu wannan shakuwar a tsakanin su tun yana yaro, da zata yi hira da shi balle ta gaya masa wani abu makamancin wannan. Ya dai san Ummami ba yar Nijar bace, ba kuma haihuwar Diffa ba, wato bakuwar haure ce da aka auro tun ana cinikin auro matan Saliyo ga masu mulkin kasar Nijar, amma bata taba yi masa matashiya a kan kasar data fito ba ko zancen wani nata, yo ina ma ya gan ta ya zauna da ita? Sabida har ya bar gida ba shi da wannan alfarmar irin ta shakuwar Da da mahaifi da ita. Nan da nan wannan boyayyar suffar tasa ta bacin rai da rashin walwala mai bayyana lokaci lokaci a tare da shi ta zo ta lullube yanayin sa na annuri da yake ciki a yanzu, wato fuskar nan tasa ta bacin rai da hadewar fuska wadda da ita ya fi kamantuwa a koda yaushe. Faytoory kan sa sai da yayi noticing canzawar fuskar Mukhtar, a lokaci guda yayi jazur ya hade kamar hadari, duk wata walwala da ke kan fuskar sa a baya ta bace. A ran sa cewa ya ke Dubi dai yadda uwa ta rungume yar ta a bainar jama a tana kuma zaune da yan ta biyu a falo guda, daya tana homework daya na aiki a computer, ita kuma tana dafa musu abinci amma shi? Umh! Ummami bai taba samun zama irin wannan da ita ba tunda ta haife shi, sai ka ce ba haihuwar sa ta yi ba, ko kuma tana dana sanin haifar tasa. Kada ki so ki ga yadda fuska da idanun sa suka koma a wannan lokacin. Kafin ka ce meye wannan Jal an ta cika gaban su da kayan abinci da abin sha na alfarma, fadi ta ke ku ci ku sha, na tabbata kun sha tafiya, na tabbata daga Nigeria kuke. Ko daga Freetown zuwa Kenema sai mutum ya jigata a jirgin kasa Tana zama a kujera domin su gaisa Amani ta kara komawa jikin ta sai da ta san yadda tayi ta kwanta a jikin ta, kunya ta kama Jal an, ita kuwa Fajur ta kasa hakuri, ta matso tana tambayar Maman nasu Mamma wacece wannan mai kama da ke haka? Ke! Daga mun Mamma na Safwan yace Yayar mu ce ta Nigeria ko? Sai kuka ya kwacewa Jal an. Amani ta mika musu hannu ta jawo Fajur da Safwan jikin ta. an ta hada su su duka ta rungume a jikin ta tana cewa alhamdulillah! Jiki na ya dade yana bani kina raye dama, ko ba dade ko baji ma kuma na san zaki zo gare mu muddin da gaske na haife ki a duniya Mukhtar ya zamo kasa ya na bata hakuri cewa ta daina kuka, ga yar ta nan Alhaji ya ce a kawo mata. Yana rokon gafarar ta, kuma yana so in babu damuwa zai kira Alhaji a vedio call su yi magana da ita Ta ce babu komai amma ba yanzu ba sai ta gama ganawa da diyar ta. Faytoory ya yi musu sallama cewa zai wuce gidan sa, ya ce ko Mukhtar ya bi shi gidan sa ko hotel mafi kusa zai kai shi? Sai Mamma Jal an ta ce shi din Mukhtar waye a wurin Alhaji Usman Faskari? Mukhtar ya sunkuyar da kai kasa sosai ya kasa amsawa, sai Abdussalam ne ya gaya mata cewa mijin Amani ne. Angon ta. Alhaji ya gaya masa ya daura musu aure ko tarewa basu kai ga yi ba, tasa fitina sai an kawo ta, shine Mukhtar din ya ce sai an fara dangana ta da mahaifiyar ta kafin tarewar ta Wata irin soyayya da kaunar Mukhtar ta zo ta lullube Jal an, sai ta tsura masa ido tana murmushi tana jin wani irin son sa a ran ta, kwatankwacin yadda ta ji Amani yanzu a ran ta, tace da Faytoory, tunda haka ne ai ita ce da masaukin su su duka, akwai bangaren maigidan zata bashi ya sauka, in ya so in zasu koma Katsina sai Malam Abdussalam ya zo ya tafi da su filin jirgi. Ai Amani da jin Jal an tace haka ta zaburo ta kuma zumburo baki tace wallahi na zo kenan. Ni da Nigeria har abada! Daddy ya daina so na, me zan koma in yi? Shi dai ya koma, shine dan sa yanzu ba ni ba . Ai tun ba a je ko ina ba Jal an ta kai wa bakin Amani mahangurba da hannun daman ta, ta kuwa same shi a daidai, tana fadin ke kuma ashe baki da kunya? Mijin naki kike wa magana haka babu ladabi babu ganin girma? Hausar Jal an bata da karfi sosai amma sun gane abinda take fadi din, duk da cikin yaren Krio ta karasa fadin bazamu shirya ba ni da ke idan ba ladabi ga babba! Mukhtar sai ya dago da kyar don kunya ya ce mata ai shi a gobe zai koma Katsina, sabida ya baro ayyukan kamfani da yawa ga Alhaji ba lafiya, don ma dai yanzu ya samu dan sa Kamilu na kula da shi. Amma Mukhtar ya zabi komawa immediately ne don har zuwa lokacin a cike yake da Amani. Ya san Alhaji bai da matsala yanzu tunda yana tare da dangin sa, ga kuma kanwar sa a gidan wato Sahura. Ayyukan kamfani kuwa duk yana tafiyar da su ne ta yanar gizo da kwamfuta, sannan yana da mataimaka na kwarai. Amma so yake yayi nisa da Amani. Bayan sun ci abinci Faytoory yayi musu sallama ya tafi. Mama Jal an tace bata yarda ba sai ya yi kwana uku sun gana sosai. Tasa Safwan ya kai masa kayan sa dakin marigayi dake harabar shigowa gidan bayan fajur taje ta share ta kunna turaren wuta. Fajur da Safwan suna zaune manne da Amani, sun kasa matsawa ko nan da can kada ta tafi ta bar su. Safwan zai yi shekaru sha biyar Fajur kuma goma. Ta umarci Safwan ya raka Mukhtar ya huta, sai suka shiga daki ita da Amani da Fajur. Ta hada mata ruwan zafi mai kamshi tayi wanka sannan suka zauna suna kara gaisawa. Sallah ce kawai ta tayar dasu a wannan ranar don kwana suka yi a zaune, Amani na baiwa Maman ta labarin rayuwar ta da mahaifin ta gabadaya tun daga sanda ta fara wayo har zuwa yanzu, da yawan matan da ya dinga aura yana saki sabida ita, da artabun su da matar shi ta karshe Haj. Rabi, da halin da yake ciki a yanzu na shanyewar barin jiki, ta bata labarin haduwar shi da Mukhy a Paris, da kawo shi gidan su da yayi, ya bashi gida daura da nasu, ya kuma sakar masa ragamar kamfanonin ta da shagunan ta, yadda ya dinga fifita al amarin sa, da irin yardar da ke tsakanin su wadda take ganin ta rage mata daraja a gun mahaifin ta, har zuwa aura mata Mukhtar da yayi ba tareda yardar ta ba wanda shine abinda ya kara sawa ta tsani Mukhtar ta kuma amince Daddy yafi son sa yanzu a kan ta. tace Mamma wallahi bana son sa, ko kadan, ko ganin sa bana son yi, kyawun sa ko ilmi sa ko yanayin kasaitar sa dake burge Balewa bai taba ruda ta sun saka ya birge ni ba, ban taba son sa ba, kuma har gobe bazan so shi ba, sabida yaron Daddy ne a kasa na yake, kuma mara kirki mara dadin mu amala ba ya girmama ni. Mara asali mara nasaba gashi nan dai shi ba tsintacce ba shi ba Da ba. Cikin halayen sa bakidaya babu guda daya da zan iya ce miki mai kyau ne. Ga girman kai ga fadin rai, ba a saka shi ba a hana shi, a haka Daddy yake tunanin zan iya zaman aure da shi? A rayuwata in ba mijin da zan juya kamar waina a tanda ba, bazan taba yarda in aura ba Duk mazan duniya Daddy ya rasa wanda zai aura min sai wanda baida asali kuma a karkashi na yake? Ai karshen kaskantawa Daddy ya gama yi min ita, shi yasa na ce ba zan koma Katsina ba har duniya ta