Sashe 12
Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin wahalallen barci Mukhy ya yi, da bai taba yin irin sa a wahala da tsayi a rayuwar sa ba, shi kadai ya san yadda zai fassara shi, da izayar da ya sha a cikin sa a dalilin yana daki daya da Amani. Da irin tsayin da daren ya yi masa, kafin a kira assalatu. Da asubahi tunda assalatun fari ya tashi yayi wankan da ya tabbatar ya dada kama shi karo na biyu, ba tare da ya amfana da komai daga yar mutanen Faskari ba. He sighed! In the toilet, saying to himself this lady is dilemma to him. Ya fito ya tada sallah, bayan ya idar ya soma hada kayan sa da ya fidda daga jaka. Saida ya kammala tattare kayan sa da ya zo dasu ya fahimci Amani ta tashi ta shiga wanka itama, don yana jiyo karar saukar ruwa a shower, ya fito falon ya zauna a kujerar da ta tashi da jakar kayan sa a gaban sa yana hada mata nata shirgin kafin ta fito, yanzun an yi sa a ta canza kayan jikin ta, ta sanya wasu wankakkun zani da riga na atampa super holland a jikin ta, wadanda da su ta shiga toilet din a hannun ta, fuskar nan tayi fresh da santsin sabulu mai kamshi sai daukar ido take. Mukhtar ya juyar da kan sa wani gefen daban, ji da yayi wani ignition irin wanda ya kwana cikin sa na tsunkulin sa, fatar bakin ta ta yi pink shar, tayi wani irin sumul kamar kasa hannu ka latsa don kaji irin sulbin ta, tasirin kebantuwar mace da miji a ranar farko ya cigaba da aiki a jikin sa yana waskewa da karfin hali irin nasa..., wadannan pinky lips din nata kawai ya ji ya ke son sumbata, musamman da ta sunkuya don daukar gyalen ta, ya hango abinda ya firgita shi ta cikin rigar ta, tsaye suke kyam cikin brazier, wadanda ake kira masu gindin tasa, da sauri ya kauda kan sa ya mike tsaye, saboda gabadaya ji yayi jikin sa na vibrating, yana amsar sakon da kwakwalwar sa ke darsawa, at the same time, ya shiga neman agajin Ubangiji a cikin ran sa, wani bakon al amari ne ya same shi again irin wanda ya kwana cikin sa jiya, shine ya sake ya dawo masa sabo, al amari ne mai wuyar fassaruwa a gare shi wanda bai taba kwana cikin irin sa ba sai jiyan, dukkan ilahirin jikin sa ke vibrating yana karbar sabon yanayin da ke sauka masa yana kashe kuzarin sa, ta hanyar sanya masa unbearable feelings na matukar son hada jiki da Amani. A rayuwar sa bai taba yi wa wata mace irin kallon da ya yi wa Amani jiya da yau ba, watakila hakan ne ya janyo masa fadawa wannan masifar. Bai taba saka idanun sa sosai a kan kowacce mace ba, don kiyaye dokar Ubangiji, sai yau a kan Amani Usman Faskari, da yake da tabbacin a yanzu ta zama matar sa, wato halalin sa. Mukhtar ya fahimci cigaba da zaman su wuri guda shi da Amani hatsari ne babba a gare shi, mai barazana ga mutuncin sa da kimar sa da girman sa a idanun ta, don Amani ba irin matan da lafiyayyen miji zai gani ya iya kauda kai bace. Sai kawai ya mike ido jajir ba tare da ya dube ta ba ya ce, Hajjaju, zamu wuce idan kin gama Amani ta dauki dan yalolon mayafin ta na raka ni gantali (cantitly) ta yafa, sannan ta zuge jakar kayan ta, bata amsa masa ba don duk ta bi ta tsargu da kallon da yake yi mata tun jiya kamar sabon maye, tafiyar tasu daga dakin nan zai fi bata ventilation da sassanyar iska, domin dai tun jiya bata shakar numfashi daidai yadda ya kamata idan ta tuna akwai Mukhtar da mayatattun idanun nan nasa a cikin dakin, abu daya ya kwantar mata da hankali jiyan, tayi barcin ta har da munshari, da ta fahimci ya bar mata falon ita kadai, ya shige cikin daki har ya rufo kofa da key ta ciki, bai kuma kara fitowa ba sai dazun da ya fito don yayi sallah. Sai kawai ta yi gaba zuwa kofa, ya janyo jakar sa ya fito shima ya rufa mata baya. Ya bada mukullin a reception sannan mai taxi ya dauke su zuwa filin jirgin Murtala Mohammed. Zuwan su ba jimawa suka tarar jirgin da zasu hau ya sauka. Ethiopian Airlines ne ya daga da su birnin Freetown, wato babban birnin kasar ta Sierra Leone. **** **** **** FREETOWN aukar su ke da wuya suka tarar da Abdussalam Faytoory wato abokin Alhaji ya zo daukar su daga nan filin jirgin saman Freetown, Lungi Airport. Abdussalam ya san lokacin da suka taso da kuma na saukar su. Don haka tun kafin su sauka yana arrival yana jiran saukar su. Abdussalam dan asalin kasar Saliyo ne kuma lardi (province) daya suka fito da iyayen Jal an. Ya karbi jakunkunan su yasa a bayan mota, gajiya ta gama bayyana a fuska da jikin Amani, amma bata so ta yada zango a ko ina yau sai dakin mahaifiyar ta. Son samu ta kwana a bayan ta, tana mai jin dumin ta itama. Amma Abdussalam kamar ya san damuwar ta, suna tafe a hanya yana tuki su kuma suna ta kallon gine-ginen birnin Freetown, wanda ya banbanta dana inda suka fito, sun shagaltu ga kallon mutane mabanbanta a halitta da suttura da wadanda suka saba gani a arewacin kasar Najeriya, duk da cewa suma Saliyo bakar fata ne amma yawancin su zaka samu dogaye ne masu kyawun sura mazan su da matan su, Faytoory ya ke gaya musu cewa yau a gidan sa zasu kwana, sai gobe in sun huta zasu wuce Eastern Province (Kenema) kenan, wato lardin da mahaifiyar ta take zaune, ya gaya musu shima dan can ne, kasuwancin fitar da iron ore ne ya ke kawo shi cikin Freetown. Kenema, shine jihar su Jal an wanda ke kan boarder din kasar Guinea da ta Liberia (Eastern Province), nanne mahadar mining din diamond industry na kasar Saliyo bakidaya. Ya kuma tabbatar musu Jal an tana raye ita da Yayar ta amma iyayen su sun jima da kwantawa dama, da yan ta biyu mace da namiji tare da ita wadanda mijin ta Lukman ya mutu ya bar mata, amma Yayar tata bata Saliyo yanzu haka, itama aure take yi a wata kasar daban cikin kasashen Africa. Mukhtar kusan ya fi Amani nuna farin cikin jin cewa Mama Jal an na raye, tsabar yadda ta zaqu su raba hanya da Mukhtar yasa ta kasa nuna farin cikin ta da wannan labarin da aka basu, tunda Faytoory ya ce sai ta kara kwana a Freetown kafin su wuce Kenema wanda ke nufin sake kwana tare da Mukhtar duk walwalar ta ta kau, dan farin cikin data samu kan ta a ciki, na jin cewa Mamanta na raye, da kasancewar ta cikin kasar da aka haifi mahaifiyar ta ta da ya bakunceta duk sai ya bace daga kan fuskar ta, komai ya daina burge ta, ko dama can ita bata taba sakawa a ran ta cewa mahaifiyar ta bata raye ba, Alhaji ne kawai yake tantama, cewa da tana raye da zuwa lokacin ko sau daya ne ta nemeta, tunda ta san garin da ta baro ta, ya bi ya take laifin sa kullum na Jal an yake hangowa, bayan shine da laifin komai. A kullum cikin mafarkin ta ta kan gan su tare ita da Maman nata, suna zantawa cikin kauna da soyayya irin na zantawar nan ta Uwa da diyar ta. Kyakkyawan dakin baki mai hade da toilet Faytoory ya basu a cikin gidan sa daga harabar shigowa, shi kuma ya shige cikin gidan don iyalin sa na Kenema, ya shigar musu da kayan su ya ce su kwanta da wuri don su samu hutawa sosai don gobe in sha Allahu karfe shidda zasu dauki hanya don tafiya ce a gaban su bata wasa ba zuwa lardin Kenema. Ai Abdussalam na bada baya, kamar jira take, ta samu bakin kofa ta zauna ta hada kai cikin guiwa ta soma girzawa Mukhtar kuka irin mai sosa zuciyar mutum, ya hana shi sakat, yasa shi a damuwar da zai kasa sukuni. Kuma idan ya ce kukan da ta soma bai bashi tsoro ba, bai taba shi ba, bai hargitsa shi ba ya yi karya, don sam bai ga me aka yi mata na kuka ba. Ga dai ta a Saliyo, gab da haduwa da Innar ta, to kukan na magani da menene? Kafin wani haushi ya zo ya tsaya masa a makoshi, ganin kukan nata har da shure-shure, na tabara da sakarci, tana yi tana fadin ita a daren nan zai dangana ta da mahaifiyar ta, ba zata kwana a dan tsukukun dakin nan tare da shi ba, ga babu wadatar iska da A/C, abincin da Abdussalam ya shigo musu da shi tasa kafa ta shure ya kife, tace munafurci ne suka shirya shi da Faytoory tun a waya, cewa su kwana a gidan sa kada su wuce a yau, don kawai ta kwana yana kare mata kallo ta wutsiyar ido, irin kallon da ya kwana yana mata a Lagos. Ai ta lura in tana barci sa ta yake a gaba yana kare mata kallo, har da taba mata gashi, ina ruwan sa da ita? Ko ta gaya masa ta karbi sadakin sa da hannun ta ne ba wajen Baba Idirisun ta baro mishi abin shi ba? Mukhtar yayi sukuti! Yana kallon ikon Allah, domin kuka take yi sosai mai hawaye da majina da sheshsheka. Tana fadin ko ya kai ta wurin Maman ta a daren nan, ko ta saka kururuwar da duk makota sai an ji su, in aka zo tace sato ta yayi Mukhtar bai san lokacin da ya isa gaban Amani ba ya damki kullin gashin kanta dake cikin ribbon ya mikar da ita tsaye cikin zafin nama, yace, idan baki yi kururuwar kin gaya musu cewa na sato ki bane baki cika butulu ba, daga abun kirki zaki yi min tukuicin tsiya? In baro komai nawa don in cika alkawarin dana dauka don kyautata rayuwar ki, ki saka min da wannan ihun da