← Book details Amani Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 22

Sashe 11

Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

air condition da rashin abun rufa. Da kyar in wuyan ta bai rike ba a irin wannan kwanciyar da tayi a kan kujera. Sai ya kasa wucewa toilet din da ya yi niyya domin ya yi wanka, ya koma uwar dakin ya dauko duvet din sa da filo guda daya, yana gayawa ran sa Amani amana ce ita a hannun sa, da mahaifin ta ya damka masa ba don ba ya so ba, ko don ya gaji da zama da ita ba, sai don aure shine cikar rayuwar diya mace, ya rabu da ita ya bashi ba don ya gaji da ita ba duk irin halin ta, ya bashi ne domin ya cikasa rayuwar ta ta diya mace. Duk abinda ya yi mata dazu yana sane, so yake ta rage masa kaifin baki amma ba shi da wata manufa a kan ta a daren yau, kai daga nan har zuwa wani lokaci mai tsahon da ba zai iya kintatawa ba bai da wata manufa ta dabam a kan ta. Ya zo ya rufa mata abin rufar, sannan ya soma kokarin saka mata filon a kasan wuyan ta da ta dora a kan masangalin kujera, kayan da ta zo da su ne a jikin ta har zuwa lokacin bata canza su ba, duk kuwa da cewa ta yi wanka, wai don kada Mukhy ya zaci tayi kwalliya saboda shi ya kara raina ta, duk da ta yi wanka amma sai ta mayar da kayan da ta tube. Gashin kan ta baki sidik mai laushi da tsayi ya watsu a kan hannun kujerar da ta tada kan ta. A hankali Mukhtar ya russuna yana kokarin saka mata filon da ya dauko a kasan wuyan ta, faffadan kirjin sa ya yi mata rumfa, sai ya ji ya kasa dagowa daga sunkuyon, sakamakon wani lallausar kamshi da ya shaka ta cikin gashin kanta, ya kara kusanta hancin sa zuwa daf da gashin kan ta, wanda ke fidda kamshin tsadadden turaren gashi na musamman, Mukhtar ya zama glued a hakan, yana ta shakar kamshin gashin Amani. Wanda hakan ya yi sanadin da wani bakon al amari ya bakunce shi, tun daga yatsar kafar sa ya tafi har zuwa cikin kwakwalwar sa..... Kamar cikin mafarki Amani ta ji ta shaki sansanyar kamshin turaren maza na Azzaro Visit , wani masculine perfume da kamshin sa ya ratsa ya tafi har cikin ruhin ta, ya kai ziyara hancin Amani da ke barci sadidan a cikin yan dakikai, sai ta muskuta ta gyara kwanciyar, yadda zata ji dadin cigaba da shakowa sosai, don ta dauka cikin mafarki ne. Hakan ya bashi access na ganin kyakkyawar fuskar ta sosai. Mukhtar ya tsura mata ido, yana kallon wannan kyakkyawar halitta ta Ubangiji, sai ya samu zuciyar sa da cewa inama yadda ta ke da kyan nan haka halin ta ma yake da kyau! Babu shakka shi kam da ya gama morewa. Yana dagowa don barin wurin dan yatsan sa ya sarko silin gahin kan ta, wanda hakan ya sa ta bude lumsassun idanun ta masu cike da barci da gajiya, da tabon busashshen hawayen da ya saka ta, suka sauka a hankali cikin nasa, sai Mukhy ya ji abinda bai taba ji a rayuwar sa ba. Ta mutstsike ido, ta kuma bude shi tangararau, nan ta tabbatar wa kanta da gaske Mukhtar ne sunkuye a saman kan ta tsayin lokacin da bata sani ba. She can t believe it, in aka ce kallon da ya dauki lokaci yana mata ba tareda ta sani ba na soyayya ne ko makamancin ta, to kallon me yake mata haka bayan ya gama ci mata mutunci? Shi kuma sai kawai ya wuce toilet cikin borin kunya ba tare da yace mata komai ba, don bai so ko kadan ta kama shi cikin wannan yanayin da ya same shi ba. Jin dumi data yi ne yasa ta duba jikin ta, sai ta ga ashe duvet din gadon ya dauko ya lulluba mata. Ta yi maza ta cire shi daga jikin ta ta ajiye a gefe, in ma wani abun ya saka mata a ciki don ya cutar da ita, to ta Allah ba tashi ba. Ya shiga toilet ne da niyyar ya dauro alwalla ya fito amma a yanayin da ya samu kan sa ya san wanka ya gama kama shi, kunyar kan sa da haushin kan sa suka taru suka lullube shi, yana wankan a shower yana cewa Amani masifa ce, ko kallon ta mutum ya cika yi wato sai janaba ta kama shi. Da ya fito sai ya kasa hada ido da ita, tana zaune tana tufke kanta da ya warware, anan falon ya shimfida darduma zai fara sallah, sai itama ta tuna bata yi sallar ba, ta mike ta nufi toilet ta dauro alwallah. Sai kawai ya fasa tada sallahr har sai da ta fito. Ba tare da ya dube ta ba ya ce mu yi jam i, yin hakan sunnah ne, sannan ki bi ni muyi nafila za ta yi musu da harare-hararen ta data saba ya ce is an option, not compulsory . Sai kawai ya tada sallar sa ya rabu da ita. Mukhtar da ya idar da sallah, sai ya zauna a kan kafafun sa yana lazimi, Amani ta tada tata sallahr a gefen sa ita kadai don ta ki yarda ya limance ta, har cewa take a ran ta haka kawai bata san asalin mutum ba zata yarda ya ja ta sallah? Da mayafin ta mai kama da abin tatar koko ta rufa a ka ta tada sallah, ta ki yarda suyi jam in sam, tana sallahr yana observing sallar tata, abin mamaki so many kurakurai a cikin sallar ta, ko zaman tahiya ba daidai ta yi ba. Data idar sai ya kasa shiru, ya ce Amani haka kike sallah a gurguje? Da wannan mayafin mai kama da abin tatar ko....? Takaici ya hana shi karasawa yayi shiru. Yana so ya ce ta yi masa karatun da ta ke yi a cikin sallar ya ji, sai ya ga cewa ba wannan ne lokacin da ya dace da duk wannan ba. Lallai aiki ne jawur a gaban sa. Yana jiran ta gaida shi, irin gaisuwar kauna da girmamawa da ya san Ummami na yi wa mahaifin sa, a duk lokacin da suka idar da sallahr farillah ita da shi, amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa, sai ma komawa data yi ta kwanta a saman kujerar data tashi, ta dauki wayar ta ta soma shiga yanar gizo, ta ture duvet din da ya rufa mata gefe guda don dai ta nuna masa bata bukatar komai da kowanne taimako da ya fito daga hannun sa. Mukhtar bai damu ba, jikin ta ko nasa? Amma ya riga ya sanyawa ran sa kin hakuri da rashin gaisuwar nan tata, a zuciyar sa ya ji takaicin wannan rashin tarbiyya nata, ya kuma gane ba karamin aiki ne jawur a gaban sa ba, in ya bar ta a haka me zata koyawa yan sa? Murya shake, ya ce ba ki iya gaisuwar bayan idar da sallah ba ko AMINA? Baki san gaida na gaba da ke ba? Baki san muhimmancin yin jam i tsakanin mace da miji ba? Baki san yawan ladan da ke cikin hakan ba? Gaisuwa ga miji in an idar da sallah al ada ce mai kyau ta iyayen mu da kannin mu Amani ta murguda baki ta kauda kai, ta ce a ran ta in Ustazu ya koma sai ya nemo duro, zata bashi kyautar lasifika . Bata san cewa a fili maganar ta fito ba. Mukhtar ya fusata ya ce haka kika ce? Fine. Abinda ya fi ustazu ma ki kira ni, amma dole ki gyara dabi u da tarbiyyar ki muddin muna tare, ba zan dauki ko dayan su ba, don ba haka na taso na ga ana yi a gidan mu ba. Oya! Ki gaishe ni ko a zuciyar ki ne, in ba haka ba mu koma gida kawai a fasa zuwa Saliyon Juya kai tayi tana kunkunin fadin in dai sai ta gaida shi ne, to kuwa saidai a koma gida din. Ya tabbatar ba zata gaishe shi din ba, takaicin ta kamar ya kashe shi, sai aka kira shi a waya shi yasa ya rabu da ita da zancen gaisuwa ya amsa wayar. Tana jin sa yana waya da wani mutum, wanda ta ji ya kira Abdussalam Faytoory, Alhaji ne ya hada su, cewa da sun sauka a Sierra Leone su kira shi, shi zai kai su har gidan su Jal an a Kenema. Shi Abdussalam din tsohon abokin harkar sa ne a Saliyo lokacin da yana harkar fitar da Iron ore, da Aluminium ore. Da turanci suke magana shi da Mukhtar, ya gaya masa suna Lagos, zasu tafi Airport da asubahin washegari daga nan su taso Sierra Leone. Ya dubi Amani bayan ya gama waya da Faytoory, ya na so ya ce ta tashi ta yi wankan kwanciya barci ta canza kayan jikin ta zuwa na barci su koma ciki, in ya so ya bar mata gadon, don ya ga zaman ta a kan kujerar ya takura ta, sai ya ga cewa wani daddadan barci irin na gajiya yayi awon gaba da ita. Ba da sanin Amani ba, Mukhtar ya ware ido tsab yana kallon ta, kallo sosai, irin wanda bai taba yi mata kwatankwacin sa ba. Kamar mai karewa halittar ta kallo, koda yake hakan ne, kallon kyautar da Alhaji yayi masa yake yi a nutse, a zaune, a tsanake, kallon da ya san a yanzu yana da hurumin yin sa ba tare da shamaki ba ko daukar zunibi ba. Ji yayi wani abu mai kama da sha awa na sake darsuwa a cikin ran sa, sauri ya yi mike ya bar wurin zuwa uwar dakin, ya haye gadon ya yi light off , ya kwanta, rokon Allah ya ke kada ya baiwa zuciyar sa ikon abinda take son darsa masa a daren yau, don bai shirya ba, itama kuma ya tabbata bazata taba yarda ba, bai san yana da lafiyar mazantaka ba sai yau da ya kebe da Amani, amma ya gwammace har abada ya dawwama cikin samartakar sa, da dai ace wani abu makamancin hakan ya hada shi da Amani.
Chapter 11 · 0% Book details