← Book details Amani Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 22

Sashe 2

Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Littafin SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI) [email protected] THE AMINA-BRIDE can cikin gida Amani ce sunkuye tana jan ruwa a rijiya domin tayi wanka, sai ta ji muryar Kawun ta Malam Idrisu daga zaure yana fadin a shigo da goron da alewa a kai dakin Talatu ta raba ta baiwa kowa. Sannan ya shiga kwalawa matar sa Baba Talatu kira yana cewa kina ina ne Talatu? An daura auren UWA da wannan yaron (Mukhtar) yanzun nan, turo min ita, ga nan sadakin ta in bata a hannun ta Talatu ta fito daga dakin ta tana daura kallabi ta dubi inda Amani ke tsaye a gindin rijiya wadda a lokacin ta dakata da jan ruwan kadan, tana sauraron me Kawun ta Baba Idi ke cewa, Talatu ta ce ai gata nan a tsaye, tana jin ka Kawu Idrisu yace au to! Banza kika yi da ni kenan Uwa? To bar jan ruwan ki same ni a daki in baki sadakin ki Amani ta cigaba da jan ruwan ta wani malolon bakin ciki ya zo ya tsaya a makogaron ta, ya ki wucewa ya tokare numfashin ta, ta ma kasa fahimtar me Kawun ta ke nufi data same shi a daki. Kawai sai gani suka yi ta saki gugan a cikin rijiyar ji kake cundum! Ta wuce dakin da aka sauke ta. Kayan ta ta hau tattarawa tana dannawa a jakar da tazo da ita. Baba Idi na can yana jiran zuwan ta ya bata sadakin ta, ta sulale ta fice daga gidan ba tare da kowa ya ankara da fitar ta ba. don Talatu ta koma daki tana shiri don fita ta gayawa yan uwa da abokan arzikin su daurin auren da aka yi yau dinnan da gayyatar su wunin biki a gobe. Daddy da Mukhtar suna dakin da aka sauki Daddy din, suna tattauanawa bayan daurin aure, kan Mukhtar a sunkuye yana jin yadda Hon. Usman ke masa magana cikin tsananin raunin murya, wadda babu komai a cikin ta sai kauna da tausayin diyar sa Amani, wadda a yau ya danka amanar ta a hannun mijin aure mafi soyuwa a zuciyar sa. A daidai lokacin Amani ta fice daga gidan ba tare da sun sani ba, dan acaba ta tare ta ce ya kai ta tasha. Tunda take a rayuwar ta bata taba hawa acaba ba sai yau. Da ya fizgi babur din saura kadan ta wuntsilo kasa, ta kama rigar dan acaban nan ta damke tana salati, nan tsamin hammatar dan Acaba ya kusa sumar da ita. A haka ya fizge ta zuwa tasha yana fadin Hajiya sakar ni don Allah kada kisa duk mu kifa, in baki iya hawa ba ki taka sayyadar ki mana? A can dakin Baba Idi, Hon. Usman ya cigaba da cewa Mukhtar wanda a yanzu ya tashi daga yaron sa ya koma surukin sa. Mukhtar bana neman komai daga gare ka sai tausayi da kyautatawa ga Amani, bata san kowacce irin wahalar rayuwa ba kada ka bar ta ta sha wahala, amma na yarda duk inda zaka shiga a duniya ka tafi tare da ita, ka tausaya mata, ka kasance mai hakuri da halayen ta, na san zaka iya shi yasa na baka, da na san bazaka iya da ita ba ko kusa ba zan fara tunnanin hada ku aure ba. Na lamunce maka kuyi amfani da duk abinda ta mallaka tare, ka taimaka mata ta cigaba da juya dukiyar ta ko bayan rai na. Sannan Baban ku Idi yayi magana a kan cewa yana son muje ga dangin ka mu kai musu matar ka idan iyayen ka basa raye. Yace hankalin sa ba zai taba kwanciya ba in ba ya ga asali da tushen ka ba, ka yi hakuri da abinda ya ce dinnan, ba rashin kauna bace gaskiyar aure kenan, ta fanni na bani da matsala da wannan, ka sani ko ba ka da kowa a duniya na riga na amince ka zama suruki a gare ni. To amma nima inada na gaba da ni wanda shine waliyi a gare ta, kamar yadda na zama waliyin ka, dole a yi masa uzurin da yake so na dangana ta da iyayen ka Mukhtar ya yi shiru, kansa na kasa, sai kara dukar da kan nasa kasa yake yi yana jin faruwar komai kamar a mafarki. Wai Amani ta zama matar sa ta sunnah daga yau. Wannan al amari sounds unbelievable! Amma ba a mamaki da ikon Allah. Zuwa yanzu ba zai ce ga gurbin da ya ajiye Amani a zuciyar sa ba, da wannan sabon matsayin nata na mata a gare shi. Illa iyaka ya san zuciyar sa bata kin auren. Amma kuma maganar da Alhaji ke yi yanzu a bar dubawa ce, Alhaji yayi kokari matuka da ya bashi auren yar sa ba tare da ya san kowa nasa ba, ba kuma tare da ya san wani abu akan sa ba (asali, tushe da nasaba). Sai ya shiga tambayar kan sa ko shi a karan kan sa ya shirya komawa gida din? Idan bai shirya ba sai yaushe? Mutuwa bata sallama, duk da cewa har yanzu zuciyar sa bata huce ba, bata shirya komawa ga iyayen sa ba, amma hakika yana son ganin Ummami. Ko da ba don mahaifin sa ba zai koma saboda ita, ta kasance mace mai rauni karkashin ikon mahaifin sa wasu abubuwan da yawa da yake zarginta da su ya kamata ya yi mata uzuri a kan su, cewa ba ta da karfi a kan rayuwar sa sai abinda mijin ta da kuma al adar su ta wanzar a kan ta, wato tana bin norms, culture and tradition ne na daular su. Me yasa tuntuni bai yi wa Ummami wannan uzurin ba? Da Daddy ya ga Mukhtar ya yi zurfi a tunani, sai yace Mukhy, in fa baka son komawa ni ba zan takura maka ba, amma ya kamata kayi tunanin cewa yanzu ya zaka tara wadanda dole wataran zasu bukaci sani ko ganin dangin su, na fahimci akwai abunda kake boye mini, ko ince yake damun ka da baka so in sani, amma ina ganin mun wuce wannan stage din yanzu, mun zama daya fa Mukhy, feel free with me ka gaya min damuwar ka da abinda ya rabo ka da gida don Allah Mukhtar ya muskuta sannan yayi ajiyar zuciya, a hankali ya soma baiwa Alhaji amsa duk da cewa bai shirya bashi amsar ba. Alhaji ka yi hakuri ka bar maganar zuwa Diffa zuwa nan gaba kadan, ka bani dama in fara cikawa Amani alkawarin dana daukar mata first, na kai ta ga mahaifiyar ta bisa amincewar ka. Nayi maka alkawarin bayan wannan in muka dawo zan dauke ku duka har Baba Idrisu da Baba Sahura mu tafi Diffa ku ga asali na mu kuma gabatar da Amani ga mahaifa na. m very sorry Alhaji, da na boye maka cewa iyaye na suna nan a raye, koda yake da baki na ban taba furta maka cewa basa raye ba, kai ne kake tsammanin hakan Hon. Usman ya shiga Hamdala yana fadin masha Allah, to shikenan Mukhtar, take your time. Na amince ka dauki Amani ku tafi Sierra Leone daga nan ku nemi mahaifiyar ta. Zan baka adireshin gidan iyayen mahaifiyar ta a rubuce. Sai kayi muku booking jirgi gobe in Allah ya kai mu sai ku wuce, na so in yi muku biki na alfarma kafin tarewa amma yanzu ina ganin ku fara isa ga mahaifiyar ta ko hankalin ta ya kwanta, in yaso ayi komai tare da dangin ta na Uwa dana uba zai fi sa ta farin ciki har ta karbi auren da sauki, ka san halin mutuniyar taka har yanzu ba wai ta amince bane, nayi gaban kai na ne na abinda addini ya ce in yi, wato a matsayin ta na budurwa in zaba mata miji nagari, ba tare da na bi ra ayin ta ba. To amma na amince sai in ba Da na Mukhtar bane mijin Amani, in shi ne kuwa bani da haufin nan bada jimawa ba zai sarrafa min Amani zuwa yadda nake burin ku zauna tare cikin kauna da soyayya mai yawa. Ina kara cewa ka yi hakuri da Amani, hakuri ba dan kadan ba, har ka aro wani ka kara a kan wanda kake da shi, mai hakuri shi ya kan dafa dutse har ya sha romon sa. Ina mata kwadayin samun tarbiyya wadda ta dace daga gareka Daga nan Alhaji ya ce ya gyara masa shimfida yana so zai kwanta ya huta, ya jaddada masa cewa ya yi booking masu jirgin tafiya Saliyo tun a daren yau, ya kuma shiga cikin gidan ya gayawa Amani yanzu idan ya fita cewa ta shirya gobe zai cika mata burin ta. shi kuma Mukhy zai cika mata alkawarin ta. Bayan ya bar dakin da Alhajin yake dakin da aka sauke shi ya nufa wato dakin Kamilu, sai ya tsaya daga zaure ya kira Isyaka da ke wucewa ya ce in ka shiga ciki ka turo min Amani, kace sakon Alhaji zan bata . Kunya ta sa ya kasa shiga gidan kamar yadda Alhaji ya umarce shi. Yaro Isyaka ya je cikin gidan ya duba har dakin Laure ya duba da na Baba Talatu amma bai gan ta ba, ya tambayi Laure ko tana ina? Tace nima tun dazu ban ganta ba. naje makaranta yanzu na dawo. Ya koma ya gayawa Mukhtar bata nan. Mukhtar ya ce ya koma ya tambayo Baba Talatu, ko ta gaya mata zata wani wuri, Talatu ta ce rabo na da ita tun da na gan ta a gindin rijiya bayan daurin aure, kafin in fita zuwa makwabta, Kawun ta ya yi mata kiran duniyar nan ta karbi sadakin ta amma yarinyar nan tayi funfurus ta yi banza da shi bata je ba har ya gaji ya fita masallaci. Mukhtar bai san sanda ya baro zauren ya tako ya shigo gidan ba, har da shi aka caje gidan kaf babu Amani babu ko tsinken ta. Daga baya kwakwalwar sa ta gaya masa babu shakka Amani ta samu labarin daurin auren su ne daga bakin Baba Idi, ta kuma yanke hukuncin gudu . Da dai ta bi umarnin mahaifin ta a kan sa. Zuciyar sa tayi bakikkirin, ran sa yayi mummunan baci da Amani, yana mamakin
Chapter 2 · 0% Book details