Sashe 17
Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yadda ya iya dole bayan yayi wanka ya canza kayan jikin sa zuwa farar jallabiyya kal kirar Dammam, ya yi sallah a masallacin kofar gidan sannan ya shiga cikin gidan da karamar tazbaha mai kyau a hannun sa. Nan ya gan su complete family a kan teburin cin abinci abin gwanin ban sha awa. Amani ta sha ado da laffaya koriya sharr da irin matsatsiyar rigar nan ta roba mai dogon hannu daga cikin laffayar light green itama. An yi mata wai irin setting din gashi wanda ya zubo a saman goshin ta ya zarce har bayan kunnen ta. Bakin nan sai shining yake da Elizabeth Arden Lip gloss kamar ka sace ta ka gudu (looking takeaway), idon nan nata mai kama da kwan zabo ya sha mascara gashin idon ya fito gazar-gazar. Rabon ta da yin ado irin wannnan bazata iya tunawa ba. Sai ko yanzu da take jin kanta a daidai wato bata da damuwar komai, tunda rayuwa ta koma mata daidai, ga ta ga uwar ta a duniya, ga kanne, sosai take cikin nishadi, barin ma data ji Safwan ya zo ya fadi sakon Mukhy na cewa gobe zai koma Katsina. Ai kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, yi ta yi kamar ta tashi ta ka rawa, murnar tata har kasa boyuwa ta yi sai da Mamma ta gane bakin ta ya ki rufuwa don Mukhy ya ce gobe zai koma ya bar ta a nan. A cikin zuciyar ta Jal an tana mamaki, ko meye aibun Mukhtar haka da matar sa ta kasa son sa? Mutum son kowa da shi a halitta da dabi a, abun alfaharin kowacce mace wajen kamun kai da kamewa da girmama iyayen ta, amma Amani na neman maraba da shi irin haka bata ko jin zata yi kewar sa don ko a waya bata ga sun gaisa ba balle text din soyayya. Kwata-kwata ta gama lura Mukhy baya ran ta, kamar kishin sa take akan Baban ta kamar kuma zuciyar ta bata taba kimsa mata soyayya a kan sa ba. Ta riga ta dauke shi rival a zuciyar ta, ko kuwa wani wanda ya tare mata gaba ya hanata rawar gaban hantsi. Sai Jal an ta shiga tambayar kan ta ko yar tata bata da lafiya ne irin ta ya mata ko kuma tana da shafar jinnu. Ta lura bayan dolonci, rashin kunya, rashin ilmin addini, rashin cikakkiyar tarbiyya har da rashin sanin muhimmancin da Allah ya baiwa miji a kan ta, da rashin sanin hakkin aure. Kada dai tarihi ne yake maimaita kan sa, tunda itama abunda ta yiwa Uban ta Alh. Usman kenan, kusan tsayin shekaru biyu tana wahalar da shi a dalilin bata son sa. Tunda ya aure ta sau daya ya taba samun sa ar ta, shima ta karfi, wanda daga baya ta gane rabon Amani ne ya rantse. Tana kuma lura da cewa tunda suka zo Amani bata je inda yake ba, bata kara bi ta kan sa ba, bata kara yin zancen sa ko kula da al amarin sa ba a matsayin su na sabon aure, balle ta damu da sanin halin da yake ciki a masaukin nasa, ko ta tambaya an kai masa abinci ko a ah? Don in an kira shi ya ci ma baya zuwa. Sai ta ji tausayin Mukhy mai tsanani da kaunar sa kamar dan cikin ta ya kamata, bata san dalili ba amma jin sa tayi ya kwanta a ranta kamar dan ta Safwan, ba banbanci, don in ba kuskure idanun ta suka yi mata ba ita ta hango kwantacciyar soyayyar Amani maras misaltuwa a can kasan kasaitattun idanun sa masu sheki da sparkling a duk sanda ya juya su a kan Amani. Ita a wurin ta Alhaji Usman ya kware shi, da ya hada shi da auren Amani, hakika ya so kan sa, domin Mukhy data ke faman kira yaron Baban ta ita sai taga ajin sa da kasaitar sa sun dame na Amani. Gashi ya san irin tarbiyyar da yayi mata amma ya hada dan mutane nagartacce, kamamme mai alkunya da wahala, don ya gan shi mai hakuri da biyayya. Ga wata irin nutsuwa da kamala a tare da shi irin wanda tsayar da addini da kula da sallah ke haifarwa namiji, wanda bata taba gani a matasa kamar sa ba. Ta shiga hangowa kan ta irin asarar surukin kwarai da zata yi, idan shashashar diyar nan tata tayi masa rikon sakainar kashin da zai gaji ya yakice ta. Sai ta yi maza ta mike tana tunanin abun yi na gaggawa, don kankarowa Amani mutunci ka idon Mukhtar kafin ya karasa zirarewa. Mukhtar yayi sallama duk suka amsa banda Amani, wadda a lokacin ta kai fork da ta cokalo dankalin turawa a jikin sa bakin ta, tana wata tauna a yangace kamar bata so. Jal an ta nuna masa kujerar da zai zauna mai fuskantar ta Amani ya tsugunna har kasa ya gaishe ta, yana ta kokarin kin dagowa ta ga fuskar sa, amma a kulawa irin ta Jal an, sai da ta hango yanayin da yake boye mata din, kuma a matsayin ta na babba ai ta san dalilin sa. Amma sai tace lafiya Mukhtar na gan ka haka babu walwala? Mukhtar ya ki zama a kujerar don ba zai iya tana kujera shima yana kan kuje ra ba, sai ya ce mata Mamma zan koma Freetown gobe da sassafe, daga can zan tashi Nigeria in sha Allah Ta kusa ce masa Amani fa? Don sai ta ji kamar bata kyauta ba in ta rike masa mata har tsayin watanni biyu nan gaba, bayan bashi da wata matar a can gida Katsinan. Kamar Mukhy ya san me Jal an take tunani sai yace, ita Amina Alhaji ya ce ta zauna da ke na dan wani lokaci, ta saba da nan din Jal an ta soma lalubo idon sa da yake boyewa da nata wayayyun idon na iyaye, ta ce. Are sure you are okay with her stay here? Cewa nake daurin aure kawai aka yi muku baku tare ba ko sau daya? In don ta ni ce ba abunda zata yi min alhalin tana da miji a gefe, gara ta wuce ku koma tare, zai fi min kwanciyar hankali da kai kan ka Ai jin haka Amani ta soma buga kafa irin wanda takewa Alhaji, tana fadin ita ta zo kenan, ba inda zata sake zuwa. Alhaji ne yasa take zaune a Katsina kuma ita kam yanzu ta barwa Mukhy shi halak malak. Sai ji kike gwajab! Mamma Jal an ta gwabje bakin da ya sha lip gloss, tace, Amina! Ashe baki da da a baki da ta ido? A gaban kannen ki kikewa mijin ki wannan diban rashin albarka? Tashi ku je ki bashi hakuri, na ce ki bashi hakuri har sai ya huce, ku yi sallama cikakkiya, kada in ganki a cikin gidannan sai da safe! Tuni Mukhtar ya kai bakin kofa don in ya cigaba da zama a wajen nan Amani ta kara magana ta rashin amincewa da umarnin ta, ko ta kara furta wani abu akan hakan ya san Mamma Jal an zata kara kai duka, da alama mai saurin hannu ce. Sosai dukan Jal an ya samu bakin Amani, tuni leben sama ya kumburo. Zata yi magana ta ji bakin ta ya mata nauyi, sai ta fara hawayen da baya yi mata wuya, a ranta ta ce shikenan itama uwa ta yayi sumumu-kasau dinsa na munafurci ya raba mu, Mamma kuma ta yi rantsuwa ta kara ta tashi ta tafi wajen mijin ta ko ta sassaba mata kamanni yanzun nan. Ko me ta tuna? Ta ja hannun Amani zuwa dakin ta da zafin nama saboda idanun su Fajur da suka bubbude suna kallon su, suna shiga ta rufo kofar da mukulli, ta dube ta da tausayi, don ta ga tsanar Mukhtar tsantsa a cikin idon ta. Ita victim ce ta kiyayyar auren dole ta san me Amani ke ji. Ta ce. Amina, bana so ki zamo daya daga cikin matan da aure da hakkin sa ke kai su wuta. Ba sai ya ce bai yafe miki ba Allah zai dubi hakkin sa a kan ki ya fidda masa, na san a shekarun ki kin san aure, kin san ma anar sa, amma a dolancin ki kina sa kafa kina takewa. Shin ya ta ko kin san irin kyautar darajar da Allah yayi miki kuwa da wannan salihin mijin da ya baki? Ina jiye miki ranar dana sani.... wadda aka ce ..... keya ce, tun da sauran mutuncin ki ki kankaro shi a idon Mukhtar, kafin ranar da zaki yi nadama mu kuma bama tare da ku an ta cigaba da yi mata nasiha iri-iri mai kashe jiki amma banda jiki mai kunnen kashi irin na Amani. Don nasihar da wa azin wani na shiga ne wani na fita ta daya kunnen. Ta kawo wasu kwayoyin magani ta bata ta ce ta hadiya yanzu tana gani kuma a gaban ta. Sai Amani ta tuno Haj. Muna, itama hakika ta bata irin wadannan kwayoyin kuma bata yarda ta sha ba, yanzun ma da Mamma Jal an ta dage sai ta sha a gaban ta, can kasan harshen ta ta kai su ta danne su da harshen ta ta kora ruwa. Mamma Jal an ta hada garwashin lantarki (burner) nan da nan ta zuba wani turare irin nasu na musamman tace ta tube ta turara jikin ta. Wanna ba musu ta yi, tunda turare ne kawai, sannan Jal an ta raka ta har kofar entrance na masaukin Mukhtar, tace ta wuce ciki tana kallon ta. Haka ta tsaya daga nesa sai da ta tabbatar Amani ta buga kofar, ta ga sanda Mukhy ya zo ya bude, da farko kamar ba zai bata hanya ta shiga ciki ba, don ta ga kamar jayayya suke, bata dai jin me suke fadi sosai kasancewar (by nature) din sa, Mukhy bai da daga murya wannan sai Amani idan ta so yin rashin kunya. Mukhtar yana bude kofar ya ga Amani ce, sai ya ki bata hanya, cewa yayi lafiya? Me kika zo yi wajen dan shege? Idanun ta suka yi rau-rau, a rayuwar ta bata taba yin maganar katobara ta yi nadama irin wannan maganar ba.