← Book details Amani Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 22

Sashe 21

Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yake sai kawai ya hau motar. Yana parking yana fitowa da Safwan ya fara tozali, yaron ya zo da gudu ya rungume shi, bakin Mukhtar yau a bude, fararen hakoran sa a warwaje, kai ka ce shi ya mallaki kamfanin COLGATE, abinda ya baiwa su Malam Tajudden matukar mamaki, sai far a yake yana rike da hannun Safwan suka shiga gidan, yana ta bashi labarin zuwan su da abubuwan da suka gani na mamaki a hanya. Kai tsaye falon Alhaji ya nufa inda ya tadda su su duka a can, har Mamma Jal an, sun hada kai ana cin abinci tana zubawa Alhaji ruwa a tambulan, wannan abu yayi matukar faranta ran Mukhtar. Yau rayuwar Ubangidan sa ta koma irin wadda ya dade yana masa fata, rayuwa mai kyau da ma ana wadda addinin musulunci yayi koyi da ita, ba irin kazantacciyar rayuwar sa ta baya ba ta babu wani jinin sa da zai rabi ni imar arzikin da Allah ya yi masa. Wadda watakila ita ta jawo masa yake ta shan wahala a rayuwar sa. Ya duba ya hanga a cikin su bai ga yar mulkin ba. Wadda tun zuwan su gidan da aka kauraye da hayaniya ta samu migraine wato ciwon kan barin kai guda wanda gajiya ta haifar mata, sai ta zame jikin ta ta haye sama dakin ta, ta shige ta kulle kan ta. Har da lika takardar data ke likawa Rakiya a jikin kofa an rubuta DO NOT DISTURB wato kada wanda ya zo ya dame ta. A duk sanda Rakiya taga ta lika mata wannan a jikin kofa bata kara zuwa kofar dakin sai ta neme ta don kan ta. To yau ma hakan, Rakiya ta zo don ta kawo mata nata abincin, don ta san bata cin abinci da mutane, nan ta ga abinda aka lika mata tuni ta yi ta kanta. Baba Sahura ta tambaye ta ina Uwa, ta san in ta ce UWA Amani take nufi, ta ce tana barcin gajiya ta lika kada a dame ta . Sahura ta ce Inye! Mulki sai mai shi. Wannan da basarake ta aura bansan ind zata kai mulki da iyawa ba Shigowar Mukhtar falon aka kauraye da yi masa barka da zuwa daga bakin kannen sa Fajur, Kamilu da sauran yan Baba Idi dana Sahura da suka zo daga Faskari yau. Baba Sahura na fadin ango ka sha kamshi, na Uwa farin mutum mai farar aniya alherin Allah ya kaiwa iyayen da suka haife ka . Sahura ta fadi hakan ne don ta san duk wannan kokarin na gyara rayuwar su data dan uwan su, kokarin sa ne bana wani ba. Shima yau ya kasa yin rowar murmushi, sai sakin sa yake gwanin sha awa. Ya zauna daf da Alhaji yana gaida Mammah, tace Mukhtar ya naga idanun ka sun tasa? Ina fatan lafiya dai? barci nayi mai yawa Mamma, da yake jiya mun kusan kwana muna meeting ta ce to madallah, ga abinci ta soma serving din sa burabuskon shinkafa da miyar ganye da naman tolo-tolo, ya ce Ai Mamma ban iya cin burabusko, shake ni yake yi ta mayar ta zuba masa fried sphaghetti da romon kaza sannan ya karba ya soma ci ana ta hirar Saliyo. Alhaji ganin kowa ya manta da Amani shi bai manta da ita ba, yar lelen sa tana like a ran sa. Yace Mukhy, ka gama cin abincin? Ya ce eh Alhaji . Alhaji yace awwa, to maza tashi ka je ka zo min da TAFISU yau labarin rayuwar ka zaka bamu dukkan mu. Da abinda ya rabo ka da iyayen ka tun da ka ce min suna raye, da dalilin da yasa baka ko so a yi maka zancen gida ko na kasar ku. Amma ina so ya zama an yi komai a gaban Uwa ta (Tafisu). Don haka je ka zo min da ita Kunya ta kama Mukhy, musamman da Jal an ta zuba masa ido, ta rasa mai yasa take jin sa kamar dan cikin ta, ta yaya zai iya tsallake Uwa da uban Amani ya je inda take a cikin gidan su? Sai da Alhaji ya sake maimaita umarnin sa, shi ba abun yace a aika Fajur ko Safwan ba, tunda Alhaji ne da kansa yayi magana. Da kyar ya iya mikewa ya bi matattakala da sassarfa zuwa sama, wato bangaren Amani. Yana zuwa kofar dakin ya ci karo da sakon ta na Do Not Disturb . A jikin marikin kofa. Dariya ce ta kama shi, sai kace a Hotel! Ai kuwa zata ga disturbance yanzun nan. Kofar ya hau kwankwasawa da karfin sa kuwa. Amani na tsakiyar barcin wahala barcin da migraine ya sabbaba mata, ta ji ana mata wannan bugun na rashin tsanaki. Ta mike cikin rangaji da sarawar kai ko kayan jikin ta da suka zo dasu a jikin ta bata cire ba balle dogon hill shoe dake kafar ta, haka ta afka gadon duka, tana tafe zuwa kofar a fusace, tana fadin mai raba ta da Rakiya yau sai Allah.....sai tayi kasa-kasa da ita, sai ta ci abu kaza-kazan ta. Tana budewa dogon ba abzinen yana sako kai cikin dakin har yana kusan ture ta, saura kadan ta fadi don dama jikin ta ba kwari. Ta yi maza ta rike marikin kofar. Farin gilashin dake idon sa ya zare, yadda zai ji dadin kallon matar tasa rigimammiya Amani Faskari, ta yi yar kiba kib-kib ta yi jawur ta murje abinta. Mai nuna ta samu kwanciyar hankalin da bata taba samu ba a zaman ta a Saliyo. Ga wani uban su kunshi mai ja da baki da Mamma tasa aka yi mata a sawayen ta da zara-zaran tafukan hannayen ta. Ta fito a amaryar ta sosai sai rashin mutunci fal a idanun ta. Tace a fusace. Shin baka ga an saka do not disturb bane? Da zaka zo ka tada ni daga barci bayan bani da lafiya? Mukhtar ya ce do not disturb, a dakin hotel kike? Ko wata tsiya kike kullawa a dakin banda barcin asara? Kuma na dauka a gidan mutane kike ba a gidan ki ba, da zaki kwanta kina zuba iko? Kallon mamaki Amani tayi masa, ta ce gidan namu ne gidan mutane? Ni da gidan uba na? Ya ce aikin kenan! Alfahari da Uba, ko anan aka binne cibiyar ki baki da ikon cewa kada a dame ki a gidan nan, tunda ba gidan mijin ki bane gidan Mama Jal an ne yanzu Amani tayi kwafa, ta koma gefen gado ta zauna tana fadin har akwai wani gida da ya fiyewa mace gidan uban ta? Mukhy ya ce sosai ma kuwa, gidan uban nata na wucin gadi ne, gidan da zata je ta haifi ya shine comfort zone din ta, shine inda duk mulkin data zuba babu mai kalubalantar ta . Amani ta zo iya wuya, idan nace maka ni kuma babu wani comfort zone da ya fiye min gidan uba na muhimmanci zaka yarda? Idan nace maka baka da gidan da ya isa ka ajiye babbar yarinya iri na zaka yarda? Idan nace maka Alhaji ya cuce ni iya cuta da ya bada aure na gare ka kaskantaccen bawan sa zaka yarda? Idan nace maka kyan ka da ake fadi bai taba bugar da ni ya sa na ji ka da wani matsayi a rai na ba saboda baka kai matsayin da zan aure ka ba zaka yarda? Ina bakin cikin abinda ya shiga tsakanin mu ranar nan a Saliyo, saboda kai ba aji na bane, ka yarda? Mukhy ya juyar da idanun sa da suka canza launi, yana kokarin hadiye bacin ran da ya taso masa, ya ce me kuwa zai hana ni yarda tunda na kwana da sanin yar Qaruna ce, Tafisu wadda tafi sauran mata, kuma a hakan aka bani sadaqar ta, ana roko na Allah Annabi in karba da hakuri, saboda Alhaji kan sa ya san ba yar kwarai ya haifa ba; ballagaza ce, banza ce, mahaukaciya ce kuma jahila, wadda ta rako mata duniya! Amani sai ta fashe da kukan da baya mata wuya na shagwaba da sakalci, amma na yau iya gaskiyar ta take yin sa bilhaqqi, domin Mukhy yayi mata cin mutunci da wani dan adam bai taba yi mata ba, tun ba a je ko ina ba, ai ga irin ta nan, Daddy ya sayo mata gori da rashin daraja a wajen wanda bai isa komai ba, sai ta kara tsinkewa da kuka. Mukhy yayi kwafa, yace yarinyar nan ina tausaya miki domin baki san rayuwa ba ko kadan, baki san Annabi ya faku ba, baki san dukkan mu darajar sa muke ci ba, duk wani rawanin tsiya ya kare a kan ki, Ubangiji ya la anci shaidan ya kuma fitar da shi daga Aljannah ne sabida girman kan sa da jin cewa yafi kowa. Baki san Allah ya ce Inna akramakum indallahi Atqakum . Ubangiji yayi alkawarin dankafar da ma abota girman kai dagawa da alfahari, masu girman kai iyalen shaidan ne, ni ina tausaya miki, ina kuma tausayawa kaina, sannan ina tausayawa ya na idan kika haife su baki yi hankali ba. Ke kam ai dadi ne ya yi miki yawa, shi yasa kika kasance mara godiyar Ubangiji; Uwa da Uban ki na son ki, suna tarairayar ki da ririta ki da son ganin kin zama matar aure ta kwarai, wani kama na iri na bai samu wannan gatan da kika samu ba. Don haka in kin gama ki zo suna kiran ki a kasa Daga haka ya juya ya fice ya koma wajen su Alhaji. Yana kokarin maida walwalar sa ta dazu, amma hakan ya faskara, domin kullum Amani ta ci mutuncin sa fita take kara yi a ran sa, ba a jimawa kuma in ya huce zata dawo ta yi masa kaka-gida a rai, ya manta duk wani aibun ta. Ba jimawa sai gata ta sauko cikin shiga ta kasaita, ta ci hill shoe din ta kamar mai shirin tafiya dinar babbar aminiya, ta kafe dauri a gaban goshi tana tana taunar cingam rakakas-rakakas. Ita a lallai ga wadda tafi sauran mata. Da dane, da tuni Alhaji ya fara yi mata kirarin TAFISU! Amma yanzu da yake yayi hankali sai cewa ya yi Uwa yaya kika sakko babu mayafi? Maza
Chapter 21 · 0% Book details