← Book details Amani Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 22

Sashe 4

Amani Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta saba, don duk zuwan da take yi Bauchi a jirgi take zuwa har wani lokacin da rakiyar yar aikin ta Rakiya wadda ke daukar mata jaka. Yau kuma ta gan ta helter-skelter daga ita sai jakar kayan ta babu alamun tun wayewar garin yau ta yi wanka. Amma tunda basu gaya mata me ya faru da ita ba da yasa ta irin wannan balaguron wahalar sai itama bata tambaya ba, tace a ran ta in ta yi wari zata ji ne. Ta sa aka shiryo abinci mai rai da motsi ta saka ta a gaba da lallashi da ban baki irin na uwa har sai da ta yarda ta ci kadan, amma jin abincin nan Amani ke yi tamkar dussa sabida yadda zuciyar ta ke cunkushe da bacin ran Daddy da abinda yayi mata. Ba don mahaifi mahaifi bane kotu zata yi karar su su biyun alkali ya bi mata hakkin ta. Amma me? Ta sani duk tsiya tana jin Daddy a ran ta, tana son Baban ta wani irin so, ba zata so ya tsaya a mumbarin shari ah da yar sa ta cikin sa ba ko da kuwa ace ta samu tabin hankali ne. Amma Mukhtar kam will pay for that, btunda ya amince aka yi mata auren dole da shi bazata taba yarda ta zama matar sa ba, bai isa ba bai kai wannan matsayin ba, bari Hamidah ta zo su nemi mafita, tana tunanin tafiya Saliyo a cikin satin nan kawai in ta je kuma ta tafi kenan, ko a gidan talbijin da radio ne zata nemo Maman ta mai suna Jal an, tunda Daddy ya ce suna kama sak, kuma sanda ta haife ta kamar girman ta take in ji Daddy. In ya so sai ta yi amfani da hoton kanta da kanta ta nemi Maman nata da shi (a wautar ta). Duk da dai ko hoton ta bai taba nuna mata ba. Amma dai zata je Saliyo kota halin kaka, ko da zata bi lungu-lungu layi-layi ne tana tambayar mai suna Jal an mai kama da ita. Abu daya kenan da zata iya fadi a kan Maman nata watau sunan ta. Haka tayi ta tunani irin na soki burutsu da rashin madafa. Ta yi wanka a dakin Hamida ta yi sallolin da ke kan ta. Tana cikin sallah tana kallon kiran Mukhtar na shigowa wayar ta da sunan da tayi saving lambar sa da shi. Ya kira sau biyu bata daga ba sai bai kara ba. Don shi mutum ne mara jure wulakanci. Can kuma sai ga na Daddy. A lokacin ta idar da sallah. Amma daga Mukhtar din har Daddy din sai ta rufe ido taki amsawa, babu wanda ta amsawa don a ganin ta basu da abinda zasu gaya mata ta yafe wannan laifin da Daddy yayi mata. Ta bar su suka yi ta kira har suka gaji suka saurara mata. Daddy ya mata dogon text wanda a ciki yayi ta lallashin ta abun tausayi, yana tambayar inda ta shiga? Yace tana so hawan jinin sa ya tashi ko? Tana so rabin jikin da yake motsawa shima ya karasa mutuwa saboda damuwar rashin ta ko? Amma ko karantawa Tafisu bata yi ba ta share shi (deleting) don ta san data karanta zata samu rauni a zuciyar ta ta fasa aiwatar da kudurin ta. Sai ta kira Hamidah ta gaya mata ta sauka lafiya da irin tarbar da Mama tayi mata, tace I really appreciate Mama s welcome, sai naji kamar Mama na ce, kin ji dadin ki Hamdy, mother is everything, yanzu wa ya isa ya yi miki auren dole Mama na raye? Auren ma da bawan gidan ku . sai kuka. Hamida ta yi maza ta ce akul Sahibah! Ki gyara kalaman ki, ta ina ya zama bawan gidan ku? Don kawai yana ma Daddy aiki yana biyan sa albashi? Kin san bauta kuwa? Kin san tun a wane karni aka daina bauta sai ta Ubangiji? Tukunnama ta ina neman halal da dogaro da kai ya zama bauta? Sahibah, Ubangiji da ya halicci dan adam ya girmama shi ya karrama shi a kan duka sauran halittu, ki daina kaskanta dan adam ko waye shi wai don yana ci a karkashin ki, musamman shi Mukhtar a yanzu, ki ringa sanin irin kalaman da zaki ke furtawa a kan sa yanzu, sabida mijin ki ne, da iyaye suka daura muku aure na musulunci ke da shi. Ba ruwan mala ikun ki (Raqib da Atid) da cewa wai bakya son sa aka aura miki, dukkan furucin ki da ayyukan ki a kan sa zasu rubuta ne kawai ga lahirar ki. In haka ne ina amfanin kalaman batanci da kaskanci ga mijin auren ka ko yaya yake? Balle Mukhtar bai yi kama da yadda kike kaskanta shi ba, bai yi kama da wulakantaccen mutum ba. Wai me kika dauki kanki ne Amani? Inna akramakum indallahi atqaakum! Yanzu dai ki bar komai a hannu na sai na iso, sai mu shawarta abun yi, ki kwantar da hankalin ki kin ji Sahibah? Idan ina nan babu mai miki abinda ba kya so in zuba ido, wallahi sai inda karfi na ya kare wajen taya ki kwatar hakkin ki, amma banda akan mahaifin ki, ko yaushe ki dinga tuna matsayin Daddy a gare ki, da wahalar da yayi dake da rayuwar ki, da tsayin lokacin da ya dauka yana faranta miki, ko a cikin iyaye shi na daban ne, ya fi karfin yayi hukunci a kan rayuwar ki ki tsallake ki zauna lafiya da Ubangijin ki Ko nasihar Hamida ta shige ta, to fa bata bar ta ta yi tasiri mai yawa a tare da ita ba, duk da ta san Hamida gaskiya ta fada. Sai ta hau lullube tasirin kalaman Hamidah da hujjoji na son zuciya, tare da cewa ko me Daddy yayi mata a rayuwa hakkin sa ne ya yi mata tunda shi ya haife ta ya kuma raba ta da uwar ta, amma bashi da ikon yi mata auren dole. Ta koma ta jingina bayan ta a gadon ta kwanta a gadon Hamidah ta rufe idon ta, ta ja duvet ta lullube har saman kan ta, tana jin duniya na kara kuntata a gare ta in ta tuna igiyoyin auren Mukhy har ukku sun hau kan ta. A haka Hamidah ta iso gidan ta tadda ita. Ta dauka barci ta ke yi, bata san ta dai rufe ido bane kawai tana dandanar azabar zuciya, sai ta aje jakar hannun ta da mayafin ta ta shiga toilet domin ta rage marar ta, kafin ta fito Mukhtar ya cigaba da kiran layin Amani. Wayar na gefen kan ta amma ta saka ta a silent don ma kada su cigaba da damun ta shi da Alhaji don haka bata san ma ana kiran nata ba. Mukhtar kuwa Alhaji ne ya saka shi a gaba da magiya kan yayi ta kiran layin nata ko Allah zai sa ta dauka, yayi mata albishir din ta dawo gida daga inda ta yi kaura a kaita Sierra Leone har dakin mahaifiyar ta in har an same ta a raye, in dai zata yi hakuri da mijin da ya zabar mata, ya ce, Mukhtar ya lallashe ta kawai ta dawo, in yaso ta fadi duk abinda take so ya yi mata, don cikin hukuncin da ya yi babu canji har abada ko bayan ran sa Mukhtar zai cigaba da rikon igiyar auren ta Shi yadda Alhaji ke shagwaba Amani yana tattashin ta da gudun bacin ran ta abun yana matukar bashi mamaki da tu ajjibi, wai dama akwai irin wadannan iyayen a wannan zamanin da muke ciki, ko a kasar shi ne kawai babu irin su? Ko a nashi lardin ne kadai babu su? Hamida taga wayar Amani na haske sai ta lallaba ta leka. Sunan da aka yi saving mai kiran da shi shi ya tabbatar mata Mukhtar ne da kiran nan ba wani ba. DIRTY HUMAN BEING! Dariya ce mai karfi ta ji tana son kwace mata, ta toshe bakin ta. Ta lallaba ta dauke wayar ta fice da ita can harabar gidan su ta samu kujerar roba fara tas ta zauna a karkashin bukkar shan iska ta gidan su, sannan ta amsa wayar Mukhtar da sallama. Daga jin sallamar da amon muryar da nutsuwar da ke ciki muryar kai har ma da tarin respect ya san ba Amani bace. Ga dukkan mamakin sa, sai ya ji wani tsoro da fargabar abinda za a ce masa ya samu mai wayar na shigar sa, a hankali ya amsa sallamar Hamidah, sannan duk suka yi shiru na yan dakikai irin na rashin sabo da juna, Hamidah ce ta karya shirun da cewa. Mr. Mukhtar ne ko? Ya amsa mata, rather subdued, cikin sautin sa da alamar mamakin inda ta san shi haka farat daya ta ambaci sunan shi, bai yi tunanin ma Amani ta yi ajiye numba din sa ba balle a ce tanazancen sa da wani nata a yadda ya san bata son sa dinnan bata kuma son zaman sa a gidan su, kuma bata so wata alaqa take hada su. A kasaice yace mata eh, nine. Excuse me pls, Ko zan iya sanin daga ina aka amsa wayar nan? Hamidah tace daga garin Bauchi ne Bauchi?! Mukhtar ya tambaya cikin mamaki, a me ta je, kuma wa ya kai ta? Ya jerowa Hamidah tambayoyin a jere a sukwane, don kuwa bai ga alamun ta fidda ko sisi daga account din ta ba, balle ya yi tunanin ta hau jirgi. Hamidah ta gaya masa gaskiyar komai na yadda suka yi sabani ita da Amanin, ta tafi Katsina wajen ta ita kuma ta taho wajen ta a Bauchi. Mukhtar har da ajiyar zuciya da ya ji cewa a (Sharon) wato motar kasuwa ta je Bauchi ita kadai, ya tausaya mata a ran sa, don ya san wani abu ne da bata saba ba, duk a cikin kiyayyar sa ne ko meye ma ya san zata iya, yace, pls my sister do me a favour, kada ki gaya mata na kira kuma kin amsa, ki bani address din gidan naku zan zo in tafi da ita gobe, saboda a bisa umarnin mahaifinta Sierra Leone zamu wuce daga nan gidan ku kai tsaye in
Chapter 4 · 0% Book details