Sashe 7
Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina ruwanku dasu, wannan abun da kukeyi babu kyau hassada ce ita kuma hassada Annabi yayi hani da ita domin akwai wani ingantaccen hadisi da manzon Allah s.a.w yake cewa iyyakum wal hasadu, fa innal hasadu ta akulul hasanati kama ya akulul narul hadabe, ma'ana nahaneku da hassada domin ita hassada lallai tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta take cinye itatuwa ko kuma karare, dan haka wannan abin da kukeyi wlh bashida amfani ko kadan,soyayya ta Allah ce idan kukayi hakuri kuma zaku samu rabonku, tana gama fadin haka tabar wurin takoma cikin female ward, tsaki sakina taja wannan damuwarki ce amma wlh bazai yiyu ace mu masu baki da kunne yakimu yaso kurma ba.
Tafida jinsa yake kamar bashiba har yaje gida,shidai bai taba soyayyaba asalima ko budurwa bai taba yiba saboda shi miskili ne nagaske kai kallon mata ma bai dameshi ba, baya hulda da mata ko kadan amma yau yayi gamo, gamo wanda za a iya cewa kyakkyawan gamo.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣9⃣
Na UMMI A'ISHA
Cikeda farin ciki ya isa gida sai wata walwala yakeyi marar kan gado domin babu wadda ya saba ganinshi cikin wannan yanayin su kansu fadawansa mamaki sukeyi yadda yau yake cikin nishadi da walwala, suna isa tangamemen gidansu yafito daga cikin mota fadawan dasuke tsaron kofar suka mimmike tsaye suka fara gyara kintsi gaba salamun baya salamun barka da shigowa tafidan zamani tafida ba akawo maka wargi, takawarka lafiya dan toron giwa, dan zaki kafi karfin rainon kura, ko kura ta mutu tafi karfin kare yaja gawarta, namijin dawa kake mai kayan alfarma, barka da shigowa zaki dangin sikari, tsawo dangin rama, takawarka lafiya gaba salamun baya salamun, cikeda jin dadi tafida yadaga musu hannu kamar yadda yasaba yanufi zauren dazai sadashi da lungun mai martaba yana zuwa kansa tsaye yawuce cikin dakin mai martaba yasameshi zaune yana kallon labarai atashar CNN zubewa yayi yafara diban gaisuwa, sannan yatashi yafita yanufi wurin inno itama a falonta ya taradda ita tana kishingide jikin tumtum ga bayi zagaye da ita sunayi mata firfita ka kayan motsa baki a gabanta shiga yayi yazauna a kan kujera bayinta suka tashi suka fiffita anan ya zamo kasa ya gaida ta yatashi yafita yau gaba daya jinsa yake kamar wani sabon mutum dan tsabar nishadi, yana isa dakinsu yashiga toilet yayi wanka yafito yasaka kayan yan kwallo jar riga mai number 1 ajikin rigar da wando dogo,adaki yayi salla yana idarwa yafito yanufi wurin dawakansa yasamu har an daura masa sirdi domin fita kilisa shi kadai kawai ake jira baiyi wata wata ba ya haye dokin shima sarkin fada yahau nasa da alama yau su biyu zasu fita kilisar, tafe suke ahankali kowannensu rikeda linzamin dokinsa har suka isa wasu manyan gonaki, tafida ne yayi yar magana ahankali kamar yadda yasaba, sarkin fada wannan gonar idan baka mantaba nataba fada muku zatayi daidai da tsarin danakeso wurin gina business suit dina, Allah ya taimakeka tafida sarkin fada ya fada,amma yallabai wani hanzari ba gudu ba wannan gonar itama ta sirikinka kace idan ban mantaba, yatsina fuska tafida yayi koma tawaye a cikin satin nan za afara yimin aiki, Allah yaja kwana,Allah yasa kafi haka, sarkin fada yafada amma acikin zuciyarsa cewa yake wannan wanne irin mutum ne ace duk gonakin sirikinka sai bi kakeyi kana karbewa kana gini marassa dalili.

3⃣0⃣
Na UMMI A'ISHA
Haka suka karaci shawaginsu suka koma gida lokacin magriba tana daf da kawo jiki, suna isa gida tafida yasauka daga dokinsa a gajiye ya shige gida afalonsu ya zube akan carpet ya kwanta gaba daya ya gama gajiya, jinsa yake kamar yayi wani gagarumin aiki, fuskar wannan yarinyar ya hango take yayi wani murmushi insha Allahu sai na auri wannan yarinyar yafada azuciyarsa domin kyakkyawa ce ajin karshe, amma mamakinsa shine yadda take karatun science alhalin kuma bata ji kuma bata magana hakika ta cika yar baiwa gashi komai nata mai kyaune tamkar ita tayi kanta saboda yadda halittar ta tatsaru sosai, lumshe manyan idanuwansa yayi oh ko meye sunanta?
Tsabar yarude yamanta bai tambayi sunanta ba shigowar faisal cikin falon ne yasashi dago kansa yakalleshi abokina daga ina?
Zama faisal yayi daga dambam nake kasan garin nawa kullum basa rabo da rikicin manoma da makiyaya, murmushi tafida yayi uhm dakyau hakimi, dariya faisal yayi kaima dai dadinta hakimin ne, murmushi tafida yayi masa wadda har saida faisal yayi masa magana yau naga kana ta fara'a kodai?
Murmushi tafida yayi babu abinda yafaru amma nazo maka da albishir nasamo matar aure dariya faisal yafara yi bakada seti tafida yaushe kayi aure da har zaka fara neman wani?
Tsaki tafida yayi kaga babu ruwanka malam ni namanta ma wlh da wani auren da mai martaba yayi min, kallonsa faisal yayi to wlh kafadawa yarinya gaskiya tunda wuri ka sanar da ita gaskiyar lamari kai bazawari ne ba saurayi ba dan kanada mata yakarasa maganar cikeda dariyar mugunta,shiru tafida yayi masa bai bashi amsaba amma yatsani faisal[truncated by WhatsApp]
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣1⃣
Kallon faisal yayi malam banida lokacinka yanzu yana gama fadin haka ya mike yanufi lungun inno zuciyarsa fes domin yana cikeda farin ciki a wannan rana.
Daren ranar bacci kadan yayi domin alla alla yake gari ya waye yaje yaga wannan yarinyar, asuba tana yi yatashi yafita masallaci yayi salla yana dawowa ya dauko alqur'aninsa ya buda yafara karantawa har karfe 6 tayi sannan yaje yayi wanka yafito ya shirya cikin suit ash colour hatta takalmin kafarsa ash colour ne yadaura agogon Gucci na azurfa duk wannan budurin da yakeyi faisal yana kwance yana kallonsa sai da yagama shiryawa tsaf faisal yace gaskiya kayi kyau mitumina wlh babu wanda zai ganka yace kai ba saurayi bane kamar ba kayi aure ba, tsaki tafida yayi Allah yasa kaima asatin nan dai ayi maka auren inyaso muga ta tsiya, dariya faisal yayi gaskiya kam gara mai martaba ya taimaka min yayi min aure tunda gashi har Kanina zaiyi mata 2 ina zaune niko daya banyi ba dariya tafida yayi yajuya yafita bai ce komai ba yana fita yashiga gurin inno ya gaidata yafito yaje wurin mai martaba shima ya gaidashi sannan yayi haramar tafiya office lolacin karfe 8 saura minti 20.
Yana zuwa office yazauna akan table dinsa yadauki yar farar takarda yayi rubutu yasa agaban rigarsa yafito yanufi female ward, yana shiga nurses suka fara gaisheshi morning sir!
Morning kawai yake cewa yawuce, da haka har yaje last bed inda budurwar nan take, kallon kyakkyawar fuskarta yayi yai mata murmushi ita dinma shi take kalllo wata farar takarda ya miko mata takarba yana bata yajuya yafita dama abinda yakawo shi kenan, theatre ya hara dan yanada aiki acan, yana fita ta bude takardar tafara karantawa rubutunsa kyau kadai kamar wadda aka buga ajikin computer, sakon nasa takaranta kamar haka "some people hv a nice smile, some hv a nice eyes,and some hv a nice faces, you u hv all of them & nice heart Good morning & hv a nice day!
I.
T, tana gama karantawa sai kuma tasoma hawaye wanda nikaina ummi Aisha ban san ko na menene ba.

3⃣2⃣
Na UMMI A'ISHA
Kuka take sosai wannan wanne irin abune da aurenta ta rinka son wani mutum nadaban, istigfari tafara yi ba kakkautawa acikin yanayin kawarta zara'u sulaiman tazo ta sameta zama tayi gefen gadon tafara tambayarta da hannu meyafaru?
Dakyar tadauki biro zara'u yau zan bar asibitin nan dama kin san acikin satin nan zan gama practical dina gida zan koma idan kingama naki ma hadu a sch dariya zara'u tayi to kijirani zanje nadawo tana gama rubuta mata ta tashi tafita, hawayenta tagoge tadauki takardar taboyeta acikin rigarta, tana nan zaune aka kawo wata mata marar lafiya agadon kusa da ita aka kwantar ta Jim kadan sai ga likitanta yazo wato dr tafida idonsa akanta yaje yagama duba matar nan yabata dukkan taimakon daya kamata sannan yadawo inda take, da ido yayi mata alama wai meya sameta idonta yayi ja, murmushi tayi takada hannu alamar babu komai takarda yadauka yarubuta mata meye sunanki?
Da babban baki tabashi amsa sunana HANFA yana karantawa yayi murmushi meye ma'anar hanfa?
Dan ni ban taba jin wannan sunan ba, murmushi tayi yakamata ka rinka bibiyar tarihi amma nabaka assignment go and find out d meaning of hanfa murmushi yayi yace zan kuwa baki mamaki domin zan samo miki ayau basai gobe ba yana gama rubutawa yabata yafita daga masu jinyar har nurses din kallonsu suke tayi to kodai sun san juna wannan abin mamaki ya isa domin ada ibrahim tafida (I.t) baya tsayawa yayi magana da patient amma gashi yau yatsaya yanata rubuce rubuce da kurma gulma nurses din suka fara yi agefe daya duk dai sun san ita wannan marar lafiyar yar practical ta hadu ta cancanci hakan.

3⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Agurguje yagama abinda yakeyi ya koma gida abinda bai saba yiba tashi karfe biyu amma yau yayi saboda yana so yasamu damar binciko ma'anar sunan hanfa, yana zuwa gida yasamu sirikinsa yana fitowa daga fada ko kallonsa bayi ba balle yasa ran zai gaisheshi tafiyarsa yayi cikeda takama fadawa suna biye dashi suna takawarka lafiya dan toron giwa gaba salamun baya salamun dahaka yashige gida dakinsu yaje yabaje ya jawo laptop dinsa yafara searching din hanfa sai da yadade yana nema sannan ya samo cikeda farin ciki yatashi yaje dakin inno bata cikin dakin dan haka kan gadonta ya haye yayi dai dai yana tunanin hanfa ba shakka sunanta ya dace da ita kuma ya cancanceta ganin inno bata shigoba yasashi mikewa zai fita daga dakin sai gata kuma ta shigo,a'a tafida dama kana nanne?
Kai yadaga mata ina nan inno ai tun dazu nadawo amma sake fita zanyi, to amma dai sai kaci abinci ko?