← Book details Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 27

Sashe 4

Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin bacin rai tace nasamu tafida dazun nan jakadiya tazo min da labarin kuma inaji banyi kasa agwiwa ba natashi natafi wurin mai martaba domin jin sahihancin labarin anan ya tabbatar min da gaskiyar lamarin sai dai nayi takaici da ba abar min kai kazabi matarka da kanka ba kamar yadda aka yiwa sauran yan uwanka sai amma kirana gareka shine kar kayi jayayya da umarnin sarki domin hakan zai iya janyo maka fushin mai martaba akanka sanin kanka ne kuma fushin Allah yana daga cikin fushi na iyaye wannan hadisine ingantacce saga bakin annabinmu annabin rahma, kayi hakuri kayi biyayya idanuwansa jawur ya dago yadubi momcy dama momcy duk wanda kaji anbawa hakuri ai cutarsa akayi cikin damuwa tace babu komai tafida ni kaina narasa dalilin sarki nayimaka wannan irin aure acikin gaggawa amma babu komai kayi biyayya kawai ni naso ace ma wannan shashan dan uwan naka faisal za ayiwa auren, babu komai momcy nagode, tashi yayi yafita yanufi sashensu shida faisal yana shiga yasamu faisal kwance afalo cikin kujera cikeda damuwa yanemi wuri ya zauna faisal yana kallon fuskarsa yasan ya amsa kiran mai martaba tashi zaune yayi yadafa kafadar tafida abokina ya akayi?

Kamar tafida zai yi kuka yace faisal wlh bana son auren nan bana so bana so, cikin damuwa faisal yace wlh tafida dazun nan lokacin da akeyin maganar tun alokacin nafara rokon sarki akan yayi hakuri nasan bazaka so auren nan ba amma yaya chiroma da baba galadima suka hayayyako min da fada wai nida kai mun raina kowa afada bama bin umarnin mai martaba saboda mu yan gata ne nida kai ne kawai sarki zai bawa umarni mu tsaya muna jayayya dashi ganin sun dauki zafi yasa nataso nabaro wurin amma dan Allah kar kadamu kanka, lallashin tafida faisal yayi tayi da kalamai masu sanyaya zuciya tareda nuna masa illar rashin bin umarnin iyaye.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [9:21AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣6⃣
Na UMMI A'ISHA
Shidai tafida yau rauni yafi gaban ciwo kallon faisal yayi kasan Allah?

Ana daura auren nan sai nasaketa kowacece cikin sauri faisal yakatse shi kar kasoma yin haka abokina domin zaka aikata babban kuskure kar kazo kayi abinda mai martaba zaiyi fushi dakai, tashi tafida yayi yashige daki yabar faisal afalo cikeda damuwa domin damuwar tafida ta faisal ce.
***********************
Alhaji Ahmad Muhammad sani shine sarki na uku ajerin sarakunan garin misau ta jihar bauchi, garin misau babban gari ne sannan kuma babbar masarauta ce mai girman gaske, sarkin misau nayanzu shine sarki na uku yagaji sarautar ne ahannun mahaifinsa alh Muhammad sani nabiyu, alh Ahmad sani sarkin misau nayanzu yana da matan aure 2 hajiya kilishi (inno) da hajiya mabruka (momcy),hajiya Kilishi wadda akafi sani da inno itace uwar gida sunyi auren saurayi da budurwa ita da mai martaba lokacin baifi dan shekara 23 ba alokacin aka nadashi sarkin garin misau, Allah ya albarkacesu da yara guda 5 duka maza babban dan sarki shine chiroman misau alh Muhammad sani sai mai bimasa marafan misau alh adamu Ahmad sani sai turakin misau alh jamil ahmad sani sai barwan misau alh Mahmud ahmad sani sai kai gaman misau alh mannir ahmad sani daga nan sai dan autansu tafidan misau sannan hakimin disina alh ibrahim ahmad sani, amaryar mai martaba hajiya mabruka (momcy) yara biyu suka haifa da mai martaba babbar yarsu itace hajiya maryam (hajiya daso) sai kaninta alh faisal ahmad sani san turakin misau hakimin dambam, faisal da tafida tare suka taso adaki daya kasancewar babu yan ubanci agidan kowa yana kaunar dan uwansu bazaka taba iya banbance tsakanin dan hajiya inno da dan hajiya momcy ba saboda tsabar hadin kai, gaba daya yaran inno adakin momcy suke tasowa yayinda itama momcy ita ta aurar da hajiya daso kasancewar bata da ya mace, shi kuwa faisal da tafida kusan lokaci daya aka haifesu tsiransu kwana 5 ne atsakani shiyasa suka taso kamar wasu yan biyu sannan suka zama abokan juna dukkaninsu basuda wani aboki sai junansu tun suna yara haka suke kiran junansu kuma wani abin sha'awar shine bazaka taba jinsu sunyi fada ba kullum cikin zolayar junansu suke, gashi suna yar kama duk kuwa da cewar tafida yafi faisal kyau domin shi mahaifiyarsa ya dauko ita kuma bafulatana ce.
[10:03AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣7⃣
Na UMMI A'ISHA
Tunda suka taso basa rabuwa tare suke yin komai har suka zama samari shekarunsu daya tsayinsu daya kuma ko amakaranta ajinsu daya, tun lokacin da suka gama primary school suka tafi america acan sukayi karatunsu gaba daya suna gama degree suka jona masters dinsu, zaman da sukayi akasar waje anan tafida ya koyi shan ganye shikuma faisal yakoyi neman mata amma daga nan baya wata dabi'a shima tafida daga shan ganye baya komai mace kuwa babu abinda yake hadashi da ita sai asibiti idan bata da lafiya, tun akasar turai yan mata suke nuna masa maitarsu afili daga turawan har bakar fatar amma bai taba yadda ya kusanci kowacce mace ba neman mata sai dan uwansa faisal, suna kammala karatunsu suka dawo Nigeria kowannensu yakama aiki shi tafida kwararren likitane a fannin mata shikuma faisal auditor ne a ministry for local government, basu jima da fara aikiba akayi musu sarauta shi faisal sarautar sa san turakin misau hakimin dambam shikuma tafida sarautarsa tafidan misau hakimin disina,tun asali shi tafaida bamai yawan magana bane bashida surutu magana bata dameshi ba wannan dalilin ne yasa ake yimasa kallon mai girman kai yanmata dayawa kuma suke masa kollon mai takama dakyau basusan shi haka yakeba naturally.
***********************
Tafida yana shiga daki yakifa akan gado zuciyarsa sai tukuki take tamkar zata fasa kirjinsa tafito waje cikin damuwa faisal ya tashi yabishi cikin dakin yaci gaba da bashi baki amma tafida Ji yake kamar ya rushe da kuka, tashi yayi ysdauko ganye yafara busawa shikuma faisal ganin haka yasashi fara tsaki dalla malam kafita waje kagama busa hayakinka acan hararsa tafida yayi kana iya fita kai tunda ba daureka nayi ba dan iska kawai, dariya faisal yayi kaima ka kusa zama dan iskan ai tunda kakusa sanin hanyar da baka sani ba, tsaki tafida yayi yasake xukar tabar ya busar da hayakin ai wannan hanyar ko zan santa ba yanzu ba, kai dan iska ne sau nawa zaka santa?

Inji faisal murmushi tafida yayi kaine dan iska amma ni banida hadi da kowacce mace,yanzu ai zakayi hadin da ita faisal yafada yana dariya, hira suka cigaba dayi har karfe dayan dare sannan suka kwanta bacci amma shi tafida bacci gagarar idonsa yayi shima faisal din baiyi dayawa ba yatashi.

Kamar yadda yasaba fita yauma haka ya shirya ya dakin inno ya gaisheta dakyar ta amsa fuskarta babu walwala, fitowa yayi ya shiga dakin mai martaba shima hakan take, dakin momcy ya shiga itace ta karbeshi da fara'a ga kayan karyawa ta shirya masa sai data kara yi masa nasiha sannan yatashi yatafi.

Yana zuwa asibitin su ya zauna jugum yana nazari wai shi mai martaba zai yiwa auren dole, bayan auren dolen ma marar lafiyace yarinyar, kai ai auren nan bazai dadeba yafada yana bude laptop dinsa.
[10:30AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣8⃣
Na UMMI A'ISHA
Laptop dinsa yabude yashiga email dinsa anan yaci karo da wani sako daga kungiyar litocin mata ta duniya ta shirya musu wani course har na tsawon wata 5 kuma har dashi aciki zasu gudanar da course din ababban birnin kasar India wato Mumbai dadi yadanji domin dama garin yayi masa zafi da azamarsa yatashi yanufi maternity domin duba halin da suke ciki.

Tunda yadawo daga office yakule adaki shi kadai yafara cike ciken takardun tafiya course dinshi anan faisal yazo yasameshi abokina dama kana ciki, eh gani kaganni kuwa, akusa dashi faisal yazauna me kakeyi?

Wlh wani course zan tafi na 5 months, kai dazakayi aure wanne course kuma zakatafi bayan ga babban course zaka samu duka tafida yakaiwa faisal yace zan yimaka rashin mutunci wlh, dariya faisal yayi duk tsiyarka dai ana daura maka aure kazama bazawari,waya fada maka?

Wlh karya kake kaine bazawari amma ni virgin ne dariya faisal yayi ai mun kusa muga karshen virgin domin virgin zai koma disvirgin dariya tafida yayi yace ka karaci iskancinka kagama akwai ranar ramuko.

Tuni aka fara shirye shirye agidan mai martaba har an hada kayan aure irin na al'ada dana zamani ankai gidansu amarya kullum bushe bushe da raye raye akeyi agarin mai girma tafida zai angwance,ni ummi Aisha hannuna asama nace Allah yaja zamanin mai girma tafida, tunda aka fara shirin biki tafida baya shiga sabgar kowa agidan tsakaninsa da kowa gaisuwa ce daga angaisa shikenan dama can shi ba mai magana ba da faisal kawai yanzu yake magana mai tsawo shima faisal din dan bazai iya fushi dashi bane saboda sun shaku sosai, amma ko inno da mai martaba tsakaninsu gaisuwa ce yadda suke fushi dashi shima haka yake fushi dasu, ana igobe za afara gudanar da biki yafara shirye shiryen tafiyarsa India domin nan da sati 2 zasu fara gudanar da course din mai taken yaki da cutar sankarar mama (cancer),shi dai faisal shine yazama tamkar angon domin komai wanda ango yakeyi shine yayi, shikuma tafida hakan ko ajikinsa tashi yayi yaje wurin mai martaba yayi masa maganar tafiyarsa India maimartaba bai damuba yace babu matsala dama itama amaryar taka karatu takeyi koda tana nanma nace babu maganar tarewarta yanzu tunda bakaso duk lokacin dakaso ta tare nan gaba, dukar da kai tafida yayi yace godiya nake mai martaba Allah yakara nisan kwana yatashi yafita.
[8:41PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣9⃣
Na UMMI A'ISHA
Yana fita yayi kicibus da faisal kallon faisal yayi yadauke kai domin yafuskanci faisal ya zake akan auran nan, cikeda dariya faisal yaja hannunsa mutumina ya akayi?

Shiru yayi kamar baijishi ba cikin zolaya faisal yace wai kai duk dokin zaka samu hanyar ne ya hanaka magana?
Chapter 4 · 0% Book details