Sashe 1
Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hausa novel blog
‹ Home
View web version
Thursday, 22 December 2016
aisha ummi at 01:08
ALHERI DANKO NE 1-50
mmi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣
Na UMMI A'ISHA
JAN KUNNE- duk wanda ya canza min wannan labarin ko ya canja sunan taurarin ciki, ko yayi min editing ALLAH YA ISA BAN YAFE BA.
Tafe yake yana cire safar hannun dake hannunsa yana cillar da ita akan tile din dake malale aharabar runfar asibitin, leburorin wurinne suke biyeda shi suna tsince duk abinda ya yar awurin shikuwa sai faman yatsina fuska yake yi sai kace yaune ranar farko wadda yafara karbar haihuwa kokuma yafara operation,ahankali yake tafiya sai kace marar jini ajiki yana sanye da light blue colour din t shirt mai dogon hannu da black din jeans idonsa sanye cikin farin gilashi amma da alama gilashin nasa na gayune bana kara karfin ido bane, duk inda ya ratsa babu abinda kakeji sai weldon sir!
Shi kuwa gogan baya magana sai daga hannu domin magana tana mutukar bashi wahala saboda yangarsa da jan ajinsa gashi da iyayi kamar mace amma hakan yana mutukar kara masa kyau kuma da alama iyayi nature dinshine, ayanda na hango fuskarsa zan iya kiyasta shekarunsa bazasu haura 27 ba aduniya,fari ne dogo siriri lange lange kana ganinsa zaka gane baya aikin wahala kuma hutu ya zauna ajikinsa, cikeda yanga ya karasa office dinsa wanda yake jere a rukunin ofisoshin manya likitoci ( consultants) wani office yabude yashiga wanda asaman kofar aka manna wani dan katako aka rubuta DR TAFIDA ajiki da manyan harrufa, ahankali yashiga cikin office din wanda yayi tsananin tsaruwa kamar ofishin shugaban kasa, kan wata doguwar kujera baka yaje yakwanta yamike yatasa kansa da hannun kujerar yafara cire (neck tied) din wuyan rigarsa yacire gilashin fuskar sa yalumshe manyan idanuwansa wanda suke zagaye da bakaken gashi masu mutukar baki sai da yadan huta sannan ya mike a hankali tamkar mace ya isa kan teburinsa yadanna wata kararrawa aguje wasu fadawa guda uku sanye cikin jajayen kaya suka shigo, suna shigowa suka fara zabga kirari, Allah ya taimaki mai girma tafida, dan sarki jikan sarki kuma sarkin gobe da yardar Allah, Allah yakara maka nisan kwana!
[6:56PM, 11/11/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣
Na UMMI A'ISHA
Hannu yadaga musu take sukayi shiru saboda sun gane nufinsa kuma dama can shi baya son yawan magana duk maganarshi atakaice yake yinta itama sai takama mutuka amma in bakamawa tayi ba sai dai yayi umarni da hannunsa, kallonsu yayi yanuna musu kan table dinsa tuni suka zabura suka fara harhada takardun dake kan table dinsa gamida dibar wasu files manya, laptop dinsa da brief case dinsa suna gama harhadawa sukayi waje yayinda shi kuma dr tafida ya sake mikewa a kujerar da yake kai sai da ya shafe sama da minti 20 ahaka sannan yatashi yahau kan kujerarsa ta aiki yajawo drawer dinsa yaciro tabar wiwi (ganye) yadauki ashana ya kyasta yafara busa hayaki, wani dan madaidaicin glass cup ya ajiye musamman akan table dinsa inda yake tara tokar tabar da yakesha kuma da alama yana sha akai akai domin har kofin yakusa cika da tokar tabar, zukar tabar wiwin yaci gaba dayi har ta kare sannan ya kishingida ajikin kujerarsa nanma yashafe fiyeda minti goma sannan yatashi ya dauki phones dinshi da gilashinsa yafita daga office din yana fita fadawansa suka zabura suka nufi motarsa dasauri suka bude masa gidan baya yashiga yazauna suka rufe kofar motar suka runtuma tasu yayinda daya daga cikinsu yashiga mazaunin direba ya zauna yatashi motar ya harba suka bar harabar cikin asibitin.
[7:33PM, 11/11/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣
Na UMMI A'ISHA
Fita sukayi daga harabar asibitin mutane sai kallon motocin nasu sukeyi gamida daga musu hannu amma dan mulkin yana daga kishingide acikin kujerar baya hannunsa rikeda jaridar daily trust yana karantawa da haka har suka isa kofar fada inda anan gidansu dr tafida yake, wani makeken gida nagani gaba dashi kuma filine babba tuni digarawan dake zaune abakin kofar gidan suka mimmike tsaye saboda ganin motar tafida,kan motocin suka kutsa cikin babban gidan wanda yasha zane iri iri da adon kala kala irin na sarakai nidai ummi Aisha tun daga nan nagane cewar gidan sarki nashigo domin gaba daya tsarin gidan namasu sarauta ne, cikeda iyayi da takama hadida kasaita dr tafida yafito daga cikin motar yatasamma cikin gidan wanda akalla sai da aka wuce zauruka sunfi 5 sannan yakarasa wani babban fili mai dauke da part part akalla zasu kai guda 5 kansa tsaye yawuce wani sashe mai mutukar kyau wanda yasha ado da kwalliya, budewa kofar falon yayi yashiga nan nahango wani dattijon mutum wanda akalla shekarunsa zasu kai 65 yana kishingide akan kilisan dake malale acikin falon wanda yawansu zai iya kaiwa guda biyar kala kala gashi jikin bangon dakin yasha zane na sarauta, gefensa tumtum ne wanda yajingina ajiki ga kayan marmari nan agefe dangin itatuwa kamar su inibi, tufa, ayaba, kankana, gwanda, zaitun, ruman, da sauran kayan itatuwa cike cikin wani dan madaidaicin kwando wanda aka tanada musamman dan adana kayan marmari, cikeda alamun gajiya yayi sallama ahankali yashiga wannan al'adarsa ce duk lokacin daya dawo daga office sai yaje ya gaida mahaifinsa da mahaifiyarsa,washe fuska dattijon yayi ya amsa sallamar da Wa'alaikas salam wa rahmatullahi wabrakatu, barka da zuwa ibrahim cikin jin dadi yakarasa inda mahaifin nasa yake yazube akasa yafara kwasar gaisuwa,barka da hutawa mai martaba dafatan mun sameku lfy, ya akaji da jama'a?
Cikin jin dadi yace alhamdulillah ibrahim dafatan ka dawo lfy?
Lfy lau yafada yana murmushi gamida mikewa yana fadin nabarka lfy ranka yadade, Allah yakara nisan kwana, Allah yaja zamani.
4⃣
Yana fitowa ya gangara izuwa wani sashen nagaba wanda tun daga nesa nafara hango bayi da kuyangu sai faman kaiwa da komowa suke, wasu suna aikace aikacen gida wasu kuma suna ta faman shige da fice tunda tafida yadoso su suka fara zubewa suna dibar gaisuwa barka da dawowa mai girma tafida, takawa lfy dan sarki jikan sarki, tafiya sannu sannu kwana nesa sarkin gobe, hannunsa kawai yake cira musu amma ko kala yakasa furtawa sai dai da alama sun san halin tafidan domin hakan bai hanasu cigaba da gaishe shi ba, ko kallo basu isheshi ba balle ya amsa gaisuwarsu wannan dalilin ne yasa mutane da dama suke kiransa da mai girman kai wasu kuma suce yanada iyayi da wulakanci to koma dai menene da alama iyayin nature dinsa ne
[8:36PM, 11/11/2015] Ummi A'isha: Tamkar wani mai ciwon kafa yaci gaba da tafiya har ya cimma sashen mahaifiyarsa hajiya Kilishi wadda yake tangamemen gaske yana shiga kasaitaccen falon nata wanda yasha adon kayan alatu yafara cin karo da bayinta wasu sunata aikin gyaran falon wasu sunata wawwatsa wani abu mai mutukar kamshi kamar turaren wuta suna ganinsa suka durkusa barka da shigowa mai girma tafida!
Kai kawai ya gyada yawuce cikin dakin inno kamar yadda yake kiran mahaifiyar tashi, akan wata katuwar darduma ya hangota tana zaune ta jingina bayanta da babban filo kafafuwanta kuma ta dorasu kan tumtum wata baiwa sai aikin mammatsa mata kafafun take, da sallamarsa yashiga yana shiga wannan baiwar ta zabura barka da zuwa yallabai, bai bata amsaba tatashi tafice, agefen gadon mahaifiyar tashi ya zauna wani irin gadone nakarfe mai runfa fentinsa kalar ruwan hoda yasha lallausar katifa da shinfidu na alfarma ga kamshi mai dadi dayake tashi daga cikin dakin, barka da hutawa inno yafada yana wani lallausan murmushi, yawwa barka da zuwa tafida tafada tana murmushin itama, kallo daya zakayi mata kagane cewa mahaifiyarshi ce domin babu ta inda ya barta akama, kamarsu daya dashi kuma da alama tana jidashi sosai, macece mai fara'ar gaske kuma bata tsufa ba dan shekarunta bazasu wuce 45 amma bazaka taba gane hakan ba saboda jikinta bai nuna ba ko kusa, cikeda kulawa tace zakaci abinci ne yanzu?
Kai ya girgiza tamkar wani karamin yaro yace a'a inno sai anjima yanzu bacci nakeji, to atashi lfy tafada tana murmushi,murmushi yakuma yi yakwanta akan gadon mahaifiyar tashi yaja filo yatasa kansa dandanan bacci yayi gaba dashi, tashi inno tayi takoma falo tazauna gudun kada azo adameshi yana bacci.
5⃣
Karfe 3:40 yatashi daga baccin da yakeyi yafito idonsa duk yayi kalar masu bacci afalo ya taradda inno tana salla dan haka bai tsayaba yawuceta yafita daga lungunta yanufi nashi yana shiga yafada toilet ya hada ruwan zafi yayi wanka yafito yasaka farar t.
Shirt mai gajeren hannu yasa wando jeans baki yafesa turaren FOGG yafito yanufi masallaci lokacin dayaje har anshiga salla, yana idarwa ya fito ya wuce ma 'ajiyar dawakai yasamu an shirya masa dokinsa anyi masa shimfida an gyarashi domin fita kilisa bai bata lokaci ba yahau suma fadawansa wanda suka hada da sarkin fada, sarkin mota, da maja sirdi suka hahhau nasu suka fito daga gidan ahankali suke tafiya tacikin garin har suka fita suka shiga dokar daji, dama idan da sabo sun saba dan kusan kullum sai tafida yafita kilisa, kilisa tana daya daga cikin abubuwan da suke burgeshi a harkar sarauta, tafiya kawai suke suna shakar iskar dake ratsa dajin sannan suka billa tawata hanyar domin komawa gida alokacin mangariba takusa yi har ta kawo jiki, suna zuwa gida ana kiran salla, akasalance tafida yasauka daga kan kosasshen dokinsa yayi alwala yashiga masallaci ana idar da salla yafito adaidai lokacin wata hadaddiyar mota tashigo baka kirar croutoure mai tsananin kyau ajiki an rubuta TAFIDA 1 kallon motar yayi yai tsaki yawuce gaba, agabansa aka yi packing din motar aka fito wani saurayine wanda zai kaishi atsaye kuma ashekaruma bazai fishiba yafito daga cikin motar yana dariya Allah yaja zamanin tafida, batare da tafidan yayi masa magana ba yawuce yafara tafiya shikuma yabishi abaya har suka karasa sashen tafidan suka shiga, afalo suka zauna cikin muryar iyayi tafida yace wai kai faisal meyasa bakada mutunci ne?
Motar tawa kadauka katafi yawon iskanci?
Dariya yayi wanda aka kira da suna faisal yace haba abokina kaima iskancin nan kana dan tafabawa, fuska tafida ya yamutsa, ni bana wani iskanci kaine dan iska, ok naji ni dan iskane saboda ina neman mata kai kuma dan ganye?