← Book details Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 27

Sashe 10

Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wurin misalin karfe 10 nadare tafida ya kalli faisal yace abokina dan Allah kayi min wani taimako, ina jinka fadi injishi, so nake gobe katafi disina gidansu hanfa kasamu mahaifinta kuyi magana ta fahinta kaji ko ahaka aka haifeta da lalurar kurmanci da bebanci, idan ba haka aka haifeta ka dauketa ka kaita asibitin tafawa balewa teaching hospital akwai likitan kurame acan kuma insha Allahu akwai taimakon da zai bata, cikeda tausayawa faisal yace dama kurma ce?

Kai yadaga wlh faisal kurma ce kuma bebiya bataji kuma bata magana amma tahadu fiyeda yadda baka zato gata da hazaka domin ahakan take karantar nursing, girgiza kai faisal yayi Allah sarki Allah yabata lfy ya daidaita tsakaninku, amin faisal sa'ar danayi ma da ban saketa ba tun da farko da matsalar da zan shiga sai tafi haka, kayi hakuri dai tafida ka kwantar da hankalinka tunda kasan illar saka damuwa acikin zuciya daga kai tafida yayi yashiga duniyar tunani har faisal yayi bacci amma shi faisal yadda yaga rana haka yaga dare ga wani azababben ciwo da kansa yake yi masa dakyar yatashi ya dauko brief case dinsa ya bude yadauki abin auna jini yafara auna jininsa nan yaga yahau fiyeda zatonsa ahankali ya mayar yakoma ya kwanta, alla alla yake gari ya waye dan faisal ya tafi disina.
[9:54AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
4⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Wayewar garin ranar faisal yashirya ya tafi disina alokacin tafida ko tashi zaune baya iya yi, lokacin da faisal yaje gidansu hanfa tarbar arziki mahaifanta sukayi masa, bayan sun gaisa yace baba dama zuwa nayi naji ko dama hanfa haka aka haifeta da wannan lalurar?

Cikeda alhini mahaifinta yace wlh faisal da bakinta da kunnenta muka haifeta har ta girma ta xama budurwa, haduwarta da lalurar shekaru uku baya ne da suka wuce tayi wata rashin lafiya mai tsanani tun daga lokacin tadaina magana tadaina ji, amma da lafiyarta lau yakarashe maganar yana kwalla, ayya Allah ya rufa asiri faisal yafada yanzu tana ina?

Tana ciki, dama ina sone zan kaita asibiti likita zai dubata, cikeda farin ciki mahaifinta yace Allah saka da alkhair madallah madalla nagode, tashi yayi ya shiga ciki bai jima ba sai gasu sun fito tare da ita kallonta faisal yayi agaskiya kyakkyawa ce sosai shiyasa tafida ya rikice da hannu suka gaisa ya bude mata mota tashiga yayiwa mahaifinta sallama suka tafi, suna zuwa asibitin faisal yafita yaje yabude mata polder aka nuna masa inda zai ga likita sannan yakoma yataho da hanfa suna zuwa tabi layi tazauna wurin ganin likita basu fi su biyar ba, tana nan zaune har layi yazo kanta suka shiga tare faisal, likitan da zai dubata bature ne nan yafara bincikarta yana wasu yan rubuce rubuce, tare da dauko wani zungureren almakashi yadauki audugu yatura a kunnen yafito dashi nan yacewa faisal gado zasu bata, za ayi mata aiki zasu biya kudi dubu dari bakwai da hamsin tashi faisal yayi yafita yaje banki ya ciro kudin yazo ya biya jifa jifa tafida yana kiranshi awaya yana tambayarshi halin da ake ciki, bayan ya gama biyan kudin ne yatafi gidansu hanfa ya sanar musu abinda zai gudana nan da nan mahaifiyarta tahada kaya suka nufi asibiti sai da faisal yagama yi musu komai sannan yayi sallama dasu yakoma misau sai yamma lis ya isa gida yana zuwa yasamu tafida kwance adakinsu ga ledar ruwa nan ana kara masa ashe duk wannan wayar da yake yimasa karfin hali kawai yakeyi shima yana kwance, sannu tafida yau likita ne dakansa ake kara masa ruwa?

Murmushi tafida yayi faisal ya kukayi da hanfa?

Cikin fara'a faisal yace an bata gado aiki zasuyi mata nan da kwana 3 fatan dai Allah yasa adace amin faisal nagode Allah yabar zumunci, haba tafida duk abinda nayi maka ai kaina nayiwa Allah yabaku lafiya, tashi yayi yafita saboda tsabar tausayin dan uwansa da ya shigeshi.
[9:54AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
4⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Acikin kwanakin kullum sai faisal yaje garin disina yayinda shikuma tafida yana nan akwance yana jinya jininsa ne yahau over gashi tunda yake bai taba yin hawan jini ba sai a wannan lokacin, ranar da za ayiwa hanfa aikin aranar faisal yatafi da sassafe dama duk abinda suke bukata shi yake kai musu, yana zuwa asibitin ya samu za ashiga da ita dakin da za ayi mata aikin ga iyayenta agefe ko wannensu zuciyoyinsu babu dadi haka shima faisal yatsaya suna nan tsaye har tsawon awa 2 sannan aka fito da ita kai daga ganinta kasan tawahala mutuka wani daki aka zarce da ita amma da alama ba ayi nasara ba, sai bakar wuya da tasha domin sai da aka fara yimata fanfo sannan aka yimata wankin kunne kai wuya dai kala kala tashata amma bata samu lafiya ba domin sauki daga Allah yake nan mamanta tafashe da kuka shi kansa faisal ji yake kamar yayi kukan domin bai san halinda tafida zai shiga ba idan yaji cewa bata warke ba, tashi yayi yashiga office din likitan dan neman karin bayani anan likitan yake sanar dashi cewa sunyi iya bakin kokarinsu amma ba adace ba kuma amma kunnenta lafiya lau yake dan haka agobe ma zasu iya tafiya gida godiya faisal yayi masa yafito yazo yasamu iyayenta yayi musu bayanin abinda likita yace, babu komai Allah yasa haka shine yafi alheri mahaifin hanfa yafada alokacin faisal yayi musu sallama yakama hanyar misau yana zuwa ya tarar da tafida yana jiransa nan ya zauna yafada masa dukkan abinda ya wakana, cikin damuwa tafida yace babu komai ni dama ita nakeso ba wani abu nata ba amma yanzu abinda nakeso dakai faisal dan Allah kaciri kudi gobe kaje kasiya musu gida mai kyau ka zuba musu furnitures kasiya musu kayan abinci domin babu amfanin ni ina zaune awuri mai kyau ina cin mai kyau amma matata tana cikin kuncin rayuwa kai faisal yadaga hakane Allah yakaimu goben.

Acikin kankanin lokaci faisal yaje garin disina yasiyawa su hanfa hadadden gida mai kyau wanda yadace da zamani yazuba musu furnitures dama unguwar ba unguwace mai hayaniya ba babu bata lokaci suka koma gidan nan iyayenta da ita kanta suka shiga yiwa faisal addu'a domin duk atunanisu shine yake yi musu wannan hidimar, lokacin da faisal yadawo gida ya sanar da tafida ba karamin dadi yajiba anan yake sanar da faisal cewa an hadashi da wani malamin addini wanda yake taimakawa mutane dan haka zaije ya duba hanfa ko Allah zai sa adace, hakan kuwa akayi faisal yaje yadauki malami suka tafi gidansu hanfa, suna zuwa malamin yace taje tadauro alwala sannan ya bukaci da abashi ruwan zamzam original ba jabun ba nan faisal yatashi yaje wani Islamic chemist anan cikin garin ya siyo yakawo, ruwan zamzam din malamin yajuye acikin wani koko yafara addu'a yana watsawa akan fuskar hanfa take tafadi akasa, cigaba da watsawar yayi yanayi yana addu'a har aka kwashe tsawon lokuta alokacin yafara yiwa su faisal bayanin cewa hakika hanfa tana fama da matsala ta jinnu kuma kurame ne gashi sunfi wahalar sha'ani amma aci gaba da addu'a, nan faisal ya zauna agarin bai tafi misau ba sai dai suna yin waya da tafida.

Kwana uku malamin nan yayi yana yiwa hanfa magani amma shiru sai akwana na hudune Allah yabada nasara jinnun sukayi magana amma da hannu suke nuni da haka malamin yace sufita daga jikinta amma da yake masu taurin kaine sai da suka sha wahala sannan suka fita.
[9:56AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
4⃣5⃣
Na UMMI A'ISHA
Sai da malamin yaja musu kunnen cewa su sakar mata kunnenta da bakinta kafin su fita, suna fita tayi wata irin atishawa mai karfin gaske, Allahu akhbar hakika sauki da rashinsa daga Allah suke tuni tafara wani bacci mai nauyi, malamin ne yajiyo gasu faisal yace wato abinda yafaru shine ruwan zafi ita wannan baiwar Allah ta zuba musu to shine suka shiga jikinta amma insha Allahu yanzu tasamu waraka farin cikine ya mamaye zukatansu asannan mamanta tayi magana tace dama lokacin taliya tadafa tana tacewa tashekar da ruwan shikenan tun daga lokacin tafara jinya, girgiza kai malamin yayi shiyasa ba aso azubar da ruwan zafi akasa dan haka sai akiyaye nan suka zazzauna suna jiran farkawarta sai da ta dade tana bacci sannan ta farka bakinta dauke da addu'a nan fa ta kalli mamanta tace mama!

Wato masu karatu ni ummi Aisha sauran kadan nasaki wayata tafadi taci screen saboda tsananin zakin muryar hanfa danaji wata irin zazzakar murya ce da ita shi kansa faisal ji yayi kamar wata balarabiya balarabiya tazama maida kallonta tayi ga faisal tace nagode Allah yasaka da alheri tana gama fadin haka tatashi hawaye suna bin kumatunta tashiga daki tayi alwala tafara salla domin nuna godiyar ta ga Allah yayinda shi kuma faisal yadauki malam suka koma misau suna zuwa yafara yiwa tafida albishir ai tafida bai san lokacin da yadiro daga kan gado ba yazo ya rungume faisal tuni yaji jikinshi yaware nan yafara tambayar faisal nawa za abawa malam?

Yace duk abinda yasamu domin shi bai yanke ba, ok to zan bashi dubu dari biyar da mota daya da gida guda daya take shima tafida yafada bathroom yadauro alwala yazo yafara nuna godiyarsa ga Allah.

Bayan hanfa ta warware ne tafara shirin komawa makaranta nanfa tafida yayi siyayya mai tarin yawa yabawa faisal ya kaimata duk abinda yasan zata bukata sai da yasai mata kayan kwalliya da kayan abinci da drinks kala kala hatta pad sai da ya siya mata ga turarruka masu tsada nan iyayenta da ita suka shiga godiya bayan tafiyar faisal mahaifinta yake ta yabon faisal sannan yabata labarin cin mutuncin da dan uwan faisal din yayi masa wato mijinta tafida tun daga nan taji ta tsani tafidan tun kafin ta ganshi.
Chapter 10 · 0% Book details