Sashe 5
Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sai alokacin tafida yayi murmushi wlh kai wannan yadama ni yanzu ba wannan ne agabana ba, dariya faisal yayi zo muje abokina kaji hannunsa yakama suka nufi cikin gida har dakinsu suka zazzauna faisal ya dubeshi yace dan Allah tafida ka tsaya ka nutsu ka rungumi matarka shifa aure mukaddari ne, cikin jin haushi tafida yace me zai hana kai ka rungumi kaddarar ka aureta?
Dariya faisal yayi ai ni ba abani bane amma kai kaga da yake dan gatane aure za ayi maka kasha sha'aninka tsaki tafida yayi yajawo earphone dinsa yajona ajikin wayarsa yafara shan sauti dariya faisal yayi yace kadai kusa ka zama bazawari, jin shiru tafida bai amsa ba yasashi gane cewa bai ji abinda yace ba domin dayaji da sai ya bashi kyakkyawar amsa domin babu abinda yatsana irin yaji yakirashi da bazawari tashi faisal yayi yafita yana dariya.
Shirye shiryen biki ya kankama yayinda shi kuma tafida yaketa shirye shiryen barin kasar, ranar alhamis aka sanya amarya a lalle faisal shine yake tsaye akan komai kullum baya samun lokacin kansa daga nan zai yi nan gidan mai martaba kuwa ya cika yayi dam da al'umma garin in banda kade kade da raye raye babu abinda akeyi domin sarki zai aurar da dan autansa kuma dan gaban goshinsa amma shi tafida in banda fushi babu abinda yakeyi gaba daya yadaina walwala yazama marar fara'a gashi kullum sai sunyi fada da faisal, ranar juma'a aka fara niyyar daura auren tafida amma kememe yaki kirshayawa.
[9:05PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣0⃣
Na A'ISHA (UMMI)
Babu yadda faisal bai yi da tafida ba kan ya shirya su fita domin da misalin karfe 1:30 za adaura auren amma yaki yarda yatashi ya shirya tun faisal yana yimasa cikin lallami har yafara fada shiru tafida yayi masa bai tanka masa ba, ganin haka yasa faisal yakara tunzura ya hasala yafita daga dakin, lokacin har su mai martaba sun tafi inda za adaura suren, faisal shi kadai yatafi yasha fararen kaya masu tsada yana zuwa lokacin wurin yacika makil amma haka yasamu ya kutsa ya isa wurin mai martaba sarki yana ganinsa yafara tambayarsa ina tafida cikeda damuwa yace ranka yadade bashida lafiya ne bazai iya zuwa ba, cikin fushi mai martaba yace yayi daidai kuma rashin zuwansa bashine zai sani nafasa yimasa wannan auren da nayi niyya ba, hakuri faisal yafara bawa sarki tuba muke ya mai martaba ayi mana uzuri,galadima ne ya matso yace ranka yadade ni ina ganin afasa daura auren nan da tafida abawa faisal, girgiza kai sarki yayi a'a galadima banki ta takaba amma nidai da tafida zan daura auren nan, nan aka fara daurin aure waliyyan amarya sunzo aka daura auren tafida da amaryarsa akan sadaki naira dubu dari, ana gama daurin aure sarki yakira uban amarya gefe yafara yimasa bayani kan cewar amarya ba yanzu za akawota ba sai lokacin da yayi magana gyada kai mahaifin amaryar yayi tareda yiwa mai martaba godiya, ana kammalawa faisal ya koma gida afalo ya taradda tafida kwance yana danna wayarsa dariya faisal yafara yi yamikawa tafida hannu assalamu alaikum mr ango harara tafida ya cilla masa yayi tsaki wata dariya faisal yayi mr ango asamo hanya lafiya amma banda rashin imani dan wlh idan kayi mata takarfi zaka iya kasheta, tashi zaune tafida yayi wlh faisal kar ka kaini bango, ya isheka, murmushi tafida yayi daga fadar gaskiya?
Allah yabaka hakuri gyara kayanka baya zama sauke mu raba, murmushi tafida yayi yau kam yazama amma kabari duk lokacin dana nemi hanyar narasa zan nemi taimakonka, zama faisal yayi bawani nan dama can kasan inda take, wai kai sau nawa zan fada maka ne?
Wlh Allah ni ban san ta inda take ba kai nifa ko haihuwa idan zan karba bana tsayawa naduba kawai aikina nakeyi dariya Faisal yayi to congratulations yanzu zaka gane ta inda take sallamar jakadiya ce ta katse musu hirar tasu.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [9:27PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣1⃣
Na UMMI A'ISHA
Har cikin falon jakadiya tashigo tarussuna barkanku da hutawa samarin kwarai tafida ta kalla ranka yadade mai martaba yana kira tana gama fadin haka tajuya tana cewa afito lafiya, tashi tafida yayi yafita shikuma faisal bai bishi ba domin yasan fada zaisha awurin mai martaba yana tsoron kar yaje ahada dashi, tafida yana isa dakin mai martaba yasameshi shida inno da momcy zazzaune gabansa wuri yasamu yazauna gabansa yanata harbawa, cikin fada mai martaba yafara magana ibrahim ka raina kowa agidan nanko?
Kanuna mana mu bamu isa dakai ba kenan tunda har za muyi maka umarni amma kasa kafa ka shure, saboda baka daukemu da daraja ba shine zaka ki halattar daurin aurenka ko?
To ka kyauta kuma duk abinda kayi daidai ne domin ahalin yanzu sai dai kanemi wani uban amma baniba aure kuma nayi maka shi sai dai zaka iya nunawa duniya rashin matsayina ta hanyar sakin matar, nanfa inno itama tadauka ya saketa mana shiyasani kuma mutumin banza kawai kai in banda tsabar raini har ayi maka umarni ka ki bi?
Yaran yanzu bakuda kunya kota sisin kobo muda aurenma basai an tare zakaga matar ba,waye zai tsaya jin ra'ayin mutum, hakuri momcy tafara basu hajiya inno ayi hakuri dai, mai martaba dana yayi kuskure amma ayi hakuri ayi masa gafara ayafe masa kar yashiga cikin wani hali dan Allah aduba kokena, tashi inno tayi tafita tanata fada shima mai martaba tashi yayi yafice yatafi fada, kallonsa momcy tayi tafida baka kyauta ba meyasa zakaki zuwa wurin daurin auren?
Cikin kasala yace momcy ni auren ne bana so, 27 years nayi aure?
Is too early wlh,murmushi momcy tayi babu komai yanzu abinda nakeso dakai anjima da daddare kuzo kaida faisal kubawa sarki hakuri kaji?
Naji momcy, yawwa Allah yayi maka albarka, tashi yayi shima yafita.
[9:47PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣2⃣
Na UMMI A'ISHA
Da daddare faisal yasaka tafida agaba sukaje wurin sarki suka bashi hakuri amma sai dakyar suka samu ya sauko sa'arsu daya su yan lelensa ne domin badan hakaba da zai dade yana fushin bai huceba, daga nan sashen inno suka shiga itama suka bata hakuri tsakanin da da uwa sai Allah nan itama ta huce tace tahakura suna dawowa dakinsu faisal yafara bawa tafida shawara, abokina kafin katafi India yakamata kaje kaga amaryarka kayi mata sallama, tsaki tafida yayi naji zanje, yawwa mutumina yakamata kaje.
Abangaren gidansu amarya kuwa koda mahaifinta yaje musu da batun rashin tariya dawuri nan dangi suka fara kace nace wasu kuma mamakine ya kamasu wannan wanne irin aure ne kodan anga basuda kudi shiyasa za araina musu wayo?
Shidai uban amarya baice komai ba kuma zancen da nake yimuku har yau nidai ummi Aisha banga kalar amaryar tafida ba balle na zayyano muku yanda take, kasancewar sarki mutum ne mai adalci yasa ya aikawa da gidansu amarya kayan abinci kala kala yace arinka ciyar da amarya kuma duk lokacin da yakare zai aiko wani sannan duk wata bukata tata arinka sanar dashi hakan da yayi ba Karamin dadi gidansu amaryar sukaji ba.
Tafida shirin tafiya yagamu domin yau saura kwana 2 yabar kasar, wanka yayi ya shirya yadau kwalliya cikin bakin danyen boyel yasa bakar hula takalmin kafarsa ma baki yaafito sai zuba kamshin turare yake take fadawansa suka bude masa motarsa yashiga suka rufa masa baya driver yaja sai disina, suna zuwa suka zarce wani dan madaidaicin gida daga ganin gidan gidan talakawa ne masu rufin asiri, cikeda yatsina fuska tafida yafito daga motarsa yanufi cikin gidan fadawansa suna take masa baya, babu ko sallama yakutsa kai cikin gidan yana rayawa aransa wai dan abin kunya nanne gidan sirikansa kai Allah ya kiyaye, atsakar gida yahango mahaifin matarsa da mahaifiyarta tana hura wuta, kafarsa yasa yayi bol da wata buta ta farin karfe atsakar gidan da alama butar mai gidan ce, dayake gwanine wurin kwallo take butar tawuce tasaman kan mai gidan taje tadaki bango tadawo baya tafadi atsakar gidan ta tankwashe yanda bazata moruba har abada.
[10:07PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Cikin tashin hankali mahaifiyar matarsa tafara magana suwaye ku?
Me kukazo yi anan gidan?
Cikin yayyatsina fuska tafida yadubi wannan mitumin yace bawan Allah yadda kasa aka daura min aure da yarka to tun wuri kaje kasa awarwareshi domin bazan zauna da itaba kuma bazan taba sonta ba, banda tsabar son zuciya tayaya zaka dauki yarka ka kaiwa mai martaba rallarta har alika min ita, to bana sonta kuma sai nasaketa sai asannan suka gane ashe shine mijin yarsu sirikinsu duk cikinsu babu wadda yayi masa magana kawai tsayawa sukayi suna kallonsa fadawansa kuwa sai fadi suke hutawarka lafiya tafida wannan sako naka ya je inda kakeso yaje, abi tafida a zauna lafiya tafida buhun karangiya ko an zazzage dole sai ya makale, gaba salamun baya salamun dan sarki jikan sarki, gunbar dotse, icen kan kabari titi kafi karfin a tsallakaka dole sai an waiga, takawarka lafiya toron giwa dawisu da ado aka sanka, ragayar dutse namijin fama, juyawa tafida yayi yafita daga cikin gidan fadawansa suka rufa masa baya kai tsaye fadarsa yawuce inda wakilinsa yake, anan ya tambayi wakilin nasa wacce gonace tafi kowacce girma agarin?