← Book details Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 27

Sashe 3

Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Akan me za ayi min wani aure yanzu kai ba gaka nan ba haba da Allah wlh bana so babu wanda zai rabani da gidan nan yanzu, kuma wlh duk yarinyar da tayi kuskure ta aureni sai ta raina kanta, dariya faisal yayi wadda takara kular da tafida kaga bani zaka fadawa ba kamata yayi kaje gurin mai martaba kayi masa wannan bayanin amma nidai ina tayaka murna sai dai shawarata agareka itace kasan mai martaba baya yin magana 2 daga yayi magana to yagamata so be careful kar kaje kajawa kanka, kaga mitumin nan nadazu daka samemu afada dashi?

Shine mahaifin yarinyar wlh kayi dacen suruki cikeda bakin ciki tafida yace malam banfa tambayeka ba dan haka kayi min shiru banza kawai dariya faisal yaci gaba dayi ganin haka yasa tafida ficewa daga dakin yatasamma lungun inno wadda yake da dan tazara daga sashensa, yana shiga yatarar da bata cikin dakin sai kuyanginta suna gyara dakin kusan ko wanne lokaci dakin nata cikin gyaransa ake, shiyasa koda yaushe yake cikin tsafta tamkar dakin sabuwar amarya, suna ganinsa sukayi waje suka bar aikin da sukeyi, gadon inno ya dale yakwanta idan dasabo kowa agidan yasaba ganinsa akan gadon inno koda wanne lokaci yagadama zai zo yahaye yasha baccinsa akai kamar wani yaron goye.
[9:36PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣2⃣
Na UMMI A'ISHA
Rufe idanuwansa yayi amma yasan ba bacci zai iya yi ba maganganun faisal ne kawai suke dawo masa jiya jiyan nan kagama fadamin idan an baka mace baka san yadda zakayi da itaba sai gashi nan da sati 2 zaka zama ango an baka mata, zunbur ya tashi zaune jin abin yake kamar a mafarki aurefa?

Daidai lokacin inno tashigo taganshi zaune akan gadonta, tafida ashe kana nan?

Nima daga wurin mai martaba nake yakira ni yabani wani sako wurinka ras!

Gabansa yafadi wato maganar faisal ta tabbata kenan ai kuwa tunda yake da mai martaba bai taba yimasa musu ba amma awannan karon dai zai yi, domin bai kamata ayi masa haka ba, abinda yafi cancanta shine abarshi ya zabi matarsa da kansa tunda sauran yayyensa ba haka akayi musu ba, maganar inno ce ta dawo dashi cikin hankalinsa mahaifinka yace nasanar dakai zai daura maka aure nan da sati 2 da wata yarinya yar gidan abokinsa amma ayadda naji yafada yarinyar ma ba lafiyayyiya bace, cikeda damuwa yace inno kuma ni za aurawa marar lfy?

Haba inno yanzu mace ma an daina yimata auren dole balle namiji kuma naga sauran duk ba haka aka yimusu ba agaskiya nidai afasa maganar auren nan idan bahaka ba wlh za aji kunya, cikeda tashin hankali inno tace haba tafida mai martaba kake fadawa haka?

Mahaifin naka zaka kunyata a idon duniya?

To bari kaji wannan sakon naka yafi karfina sai dai yanzu katashi da kanka kaje ka sanar dashi bazakabi zabin da yayi maka ba, amma kasani mahaifinka ba yayin magana 2 magana daya yakeyi kuma aduk inda yasaka doka a garin nan ana bi balle agidansa dan haka ina baka shawara da kayiwa mahaifinka biyayya kar kajawo abinda zaiyi fushi dakai, shiru tafida yayi ransa duk yagama jagulewa wannan wanne irin abu ne?

Shidai wlh wannan auren bada shiba, kallon inno yayi to inno abawa faisal mana amma sai ace ni za abawa?

Wlh bana so ni babu auren da zanyi ban shirya yin aure yanzu ba kafin inno tayi magana jakadiya tashigo gafara dai ranki yadade barka da hutawa ayi min izini nashigo, kya iya shigowa jakadiya inno tafada tana kokarin kishingida.
[10:49PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Shigowar jakadiya ne yasa tafida dago dara daran idanuwansa yafara kallon jakadiya cikin girmamawa jakadiya ta durkusa ranki yadade barka da hutawa, Allah ya kareki uwar dakina sarki ya aikoni, kallonta ta maida kan tafida mai girma tafida sako daga mai martaba sarkin adalci sarki nakwarai yace kaje yana son ganinka cikeda damuwa batare da tafida yabata amsa ba yatashi yafita izuwa lungun sarki gaba daya jinsa yake kamar a mafarki, yana isa dakin sarki yaja yatsaya abakin kofa sakamakon ganin maga kofa dayayi toge akofar, cikin girmamawa maga kofa yafada dakin sarki yayiwa sarki bayanin zuwan tafida, yashigo sarki yafada atakaice, dasauri maga kofa yadawo yayiwa tafida iso suka karasa dakin sarki sannan maga kofa yafita yabasu wuri sunkuyar dakai tafida yayi Allah yaja zamaninka yanzu na samu kiranka daga wurin jakadiya,eh nine naturata takira min kai, ranka yadade na amsa kira, ibrahim!

Mahaifin nasa yakira sunansa na'am, Allah yaja zamaninka, Allah yasa kafi haka tafida yafada kansa yana duke akasa, dalilin kiran da nayi maka shine kayi hakuri da abinda zakaji daga gareni, wato ibrahim aure zanyi maka nan damako biyu, ina fata zakayi dukkan wasu shirye shiryen dasuka dace nan da sati biyun, sannan ina so kayi hakuri da ita matar da zan aura maka domin ba lafiyayya bace kuma ga hotonta idan kana da bukatar gani, kansa akasa yace ya mai martaba ayi min adalci kuma asausauta min dan Allah afasa auren nan domin banida shirin tunkarar aure ahalin yanzu, kai!

Wata tsawa mai martaba yadaka masa wadda ni kaina ummi Aisha sai da narazana, bafa shawararka nake nema ba umarnine nake baka, yanzu kai ibrahim har kayi girman da zan fada maka magana kayi min musu?

Tuba nake ranka yadade, natuba mai zamani, ayi min afuwa hakika nayi kuskure amma ayafe min, cikin fada sarki yace to aure babu fashi zan daura shi inyaso aranar dana daura kana iya warwareshi ta hanyar sakin matar, ai kuwa zan sakenta tafida yafada acikin ransa.
[8:17AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Tabbas ko wacece sai narabu da ita danme za ayi min auren dole bayan ga faisal nan shi ba ayi masa ba, kuma naga komai mai martaba zai yi tare yake yi mana nida faisal sai a wannan ne za a banbanta mu?

Fadan mai martaba ne ya dawo da shi cikin hayyacinsa, sanin kankane ni ba karamin mutum bane bare jama'ata su rainani, bana alqawari in saba sannan bana yin magana biyu dan haka dolenka ka amincewa umarnina domin ba kaine ka haifeni ba nine na haifeka idan hukuncin dana yanke maka yayi maka tsauri to ka mutu kabar duniyar inyaso sai ka huta da auren da zanyi maka, tuba nake ranka yadade, ayi min aikin gafara, tashi kabani wuri mutumin banza mutumin wofi, Allah ya huci zuciyarka ya mai martaba cikin hanzari tafida yatashi yafita gaba daya idanuwansa sun kada sunyi jajawur kamar gauta, ransa in yayi dubu yagama baci, dakin inno ya koma acan yaci karo da momcy bai iya yi mata magana ba yashiga dakin inno yazauna akusa da kafafunta, inno wai dan Allah laifin me nayi muku ne haka kuka tsaneni?

Murmushi tayi irin nasu na manya haba tafida na, da daya tamkar da dubu, wlh tafida idan na rantse maka cewa dani da mai martaba munfi sonka fiyeda kowa acikin yayanmu ba zanyi kaffara ba, ni da mahaifinka duk cikin yayanmu munfi nuna maka so da kauna ba wai dan kasancewar ka dan auta ba a'a soyayyar daga Allah take haka nan Allah ya sanya mana sonka fiyeda sauran yan uwanka sannan nasan mahaifinka bazai taba cutar dakai ba, saboda idan kashiga damuwa sai yafika damuwar, dan Allah tafida ka kwantar da hankalinka kayiwa mahaifinka biyayya kaji?

Shi wannan mutumin da zai baka yar tasa mutumin sarki ne tun suna yara, yayiwa sarki alherai da dayawa wadanda bazasu lissafu ba to kaga kuwa shi ALHERI DANKO NE!

Baya faduwa kasa banza sannan kuma dadi musanye ne, abinda nakeso dakai kawai shine kayi biyayya, cikin kunar rai tafida yace amma inno ga ba faisal nan ba why not shi baza abashi ba?

Sai ni za abawa danni aka tsana?

Kai rufe min baki marar kunya inno tafada cikin fada dan kaga inata shawo kanka ina lallaminka da kalamai masu dadi shiyasa zaka fada min maganar banza?

Anki abawa faisal din kai aka yi niyyar bawa in yaso aranar da aka daura auren ka saketa ko kuma idan ankaita gidan naka ka kasheta kaji?

Fitsararren kawai in banda tsabar rashin kunya har sarki yabada umarni katsaya kana ja in ja da umarninsa?

To sai gareka karka fasa, tashi maza kafice min daga daki kuma kar nasake ganin kafarka acikin dakina, da sauri tafida yatashi yafita bayi da kuyangu sai mamaki suke domin inno bata taba yiwa tafida irin wannan fadan ba kowa agidan yasan tafida shine dan lelen inno da mai martaba.
[8:41AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣5⃣
Na A'ISHA (UMMI)
Tafiya yake ahankali duk da cewa dama haka yasaba tafiya amma tafiyar yau tasha banbam data kullum lungun momcy mahaifiyar abokinsa faisal kuma dan uwansa najini yanufa yana shiga jakadiya tayi masa iso yakarasa dakin momcy tana zaune akan gado wata baiwa tana yimata firfita da muhucin kaba gefenta kuma wata baiwar ce take yi mata labarun ban dariya ko sallama bai iyayiba yashiga take bayin suka bar abinda sukeyi suka tashi suka fita, akan daddumar dake malale acikin dakin ya zauna yadukar da kai barka da hutawa ranki yadade, barka kadai tafida,cikin damuwa yace momcy ko kin samu labarin abinda zai faru dani?
Chapter 3 · 0% Book details