← Book details Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 27

Sashe 21

Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ita kam hanfa tana zuwa hostel ta tarar da zarah hannunta rikeda key point din chemistry tana karantawa kayan ta ajiye ta kwanta saboda tagama gajiya, sannu da zuwa zarah tafada tana kallonta yawwa sannu zarah dan Allah ki debo min ruwa atuka tuka ki dafa min zanyi wanka cikeda tausayawa zarah tace to ta tashi tadauki bucket taje tuka tuka tadebo mata ruwan tazo ta kunna gas tadora mata ruwan zafi, kallon zarah hanfa tayi ga abinci kizo ki dauka harda ice cream,a'a kifara yin wankan idan kika fito sai muci, ni na koshi zarah kici kawai tashi tayi tajuye ruwan zafin ta tafi bathroom domin yin wanka.
[8:15PM, 11/29/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
9⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Shi kam tafida yana can zuciyarsa fes domin jinsa yake wasai sakamakon yau ya samu hanfa son ranshi, sai da daddare yasamu zarafin kiranta suka dan taba hira sakamakon bata jin dadi jikinta har wani zazzabi zazzabi take ji amma bata sanar dashi ba, kullum yana kiranta awaya suna hira amma bai san bata da lafiya ba,nan kuwa tana jin jiki sosai domin ko class bata fita saboda tafiyar ma wahala take yi mata shi dai tafida bai san wainar da take toyawa ba.

Ranar laraba kawai da yamma ya shirya yatafi makarantar yana zuwa yahadu da zarah a area class amma bai ga hanfa ba anan yake tambayar zarah cikeda mamaki ta sanar dashi hanfa fa bata da lafiya tun ranar da ya zo yadauketa, hankalinsa yaji yatashi nan ya tura zarah taje ta taho masa da ita, koda zarah taje hanfa dariya tayi tace duk kinbi kin tayarwa da mijina hankali bayan ni kuma nawarke, wayasaki ki cemasa banida lafiya?

Kallonta zarah tayi Allah ya baki hakuri, amin hanfa ta fada tazira doguwar riga suka fito, bakisa turare ba zarah tafada, babu turaren da zan sa balle yaji kamshi yakasa hakuri yaje yasake yi min jina jina, dariya zarah tayi mrs tafida kenan, lokacin da suka fito tun daga nesa tafida yake kallon tafiyarta babu laifi yanzu ta dan dawo dai dai amma ba yadda take ba, karasowa tayi tabude motar ta shiga ita kuma zarah ta wuce class, kallon tafida tayi sannu da zuwa,yawwa sannunki da kokari,murmushi tayi me nayi?

Shiru yayi bai bata amsa ba wai adole yayi fushi,dauke kansa yayi daga kallonta,kallo tabishi dashi yana sanye da orange colour din riga da dark blue colour din jeans sai kamshi mai dadine yake fita daga jikinsa, hannunsa dake ajiye akan hand break ta kalla yatsunsa zara zara sai kyalli suke faratansa kuwa tamkar ya shafa musu lanfen fari.
[8:44PM, 11/29/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
9⃣5⃣
Na UMMI A'ISHA
Babban dan yatsansa na tsakiya ta kalla yana sanye cikin zoben azurfa mai kyau, ya daura agogon azurfa a hannunsa ahankali takai hannunta tadora akan hannunsa, wai me nayi maka tafada tana shafa hannunsa nan tafida yaji ta fara rudashi amma dai duk da haka baiyi magana ba, ci gaba da wasa da hannun sa tayi da hannunta, ka yi hakuri idan wani abu nayi maka, shine bakida lafiya amma baki fada min ba ko?

Murmushi hanfa tayi takai masa kiss akumatunsa kayi hakuri ai na warke, ban hakura ba to me kake so nayi maka ka hakura?

Nidai ban hakura ba kanta tadora akan kafadarsa dan Allah kar kayi fushi dani kasan idan miji yana fushi da matarsa tana rasa rahamar ubangiji tafada kwalla ta ciko idonta, jiyowa tafida yayi yarungume ta nibana fushi dake amma dai banji dadin abinda kika yi min ba dabaki fada min naji miki ciyo ba, ni ba ciyo kaji min ba, to me nayi miki?

Ai nawarke shikenan, ban yarda ba yafada yana kissing din goshinta, kin san ma'anar sunanki?

Eh babana ya taba fada min saboda tun ina yarinya har nagirma ban taba jin mai sunana ba shine na tambayi babana ya fada min, murmushi tafida yayi kajita yanzu ke din mecece idan ba yarinya ba?

Wlh yanzu ni ba yarinya bace na girma, hannunta ya dan matsa nine nasa kika girma ko?

A'a kai din da me kafini?

Baki sani ba?

Na mayar dake babbar mace yanzu, zoben hannunsa ta murza dama can ni nagirma, haka dai kika ce, zan fada miki fassarar sunanki amma sai a first night dinmu, wanne first night kuma?

Bayan aikin gama ya gama, uhm waya fada miki?

To meya saura?

Ai ka rigada ka gama first night dinka tun jimawa kar ki kara fadin haka har yanzu ni saurayine, hmmm kai kam har yanzu saurayine amma ni kagama mayar dani bazawara, dariya tafida yafara yi sannan yace mata wlh kin bani dariya ai kema har yanzu budurwa ce, kafada ne kawai dan naji dadi amma ni kaina ajikina ina jin natashi daga budurwa, to tsaya yanzu yaya kike so ayi?

Kawai ka fada min ma'anar sunana kadaina batun sai first night, to zan fada miki amma ba yanzu ba, to Allah yakaimu lokacin tafada tana saka dan yatsansa a bakinta, sai da suka karaci abunsu sannan tafida yay[truncated by WhatsApp]
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [6:11PM, 11/30/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
9⃣6⃣
Na UMMI A'ISHA
Tun daga ranar tafida bai dawo makarantar ba saboda exam hanfa zata fara dan haka yayi hakuri ya kyaleta domin tasamu damar yin karatu, amma atakure yake da rashinta, sai dai kullum suna makale awaya, lokacin da zarah zata tafi gida ya aiki babban zaginsa yakai wa hanfa waya hadaddiya mai tsadar gaske nan suke wuni kullum suna hira har ta kammala exams dinta tafara shirin komawa gida aranar da zata tafi ma bashine yakai ta ba fadawansa ya tura suka dauketa suka kaita gida.

Bayan tafiyarta da kwana 2 mai martaba yatura jakadiya takira masa tafida da faisal nan suka taso suka taho atare suna zuwa turakin soro yayi musu iso nan da nan fadawa suka fara zabga kirari, barkanku da zuwa samarin kirki sarki ya gaisheku, takawarku lfy gaba salamun baya salamun, cikin girmamawa suka shiga cikin fadar suka zube suka fara gaisawa, murmushi sarki yayi tareda yin gyaran murya, ibrahim, faisal Allah yayi muku albarka yayana, hakika ina alfahari daku acikin yayana musamman kai ibrahim domin ina sane da dukkan abin alkairan da kake yiwa iyayen matarka hakika naji dadi marar misaltuwa kuma hakan da kayi ya nuna min cewa nine na haifeka kuma dama tun farko nasan zabin da nayi maka zai zama alheri agareka shiyasa kaga na jajurce, shi mahaifin matarka yayi min alherin da bazan iya mantawa ba shiyasa nayi burin hada Zuri'a dashi saboda mutumin kirki ne sannan yasan yakamata, a matsayina na mahaifinku ina horonku da ku yawaita aikata ayyukan alheri arayuwarku domin shi ALHERI DANKO NE, sannan duk wanda ka yiwa alheri bazai manta ba mutukar ba butulu bane,magana ta biyu kuma itace nan da sati uku za ayi shagalin bikinku kowa akai masa matarsa, godiya sukayi tareda fadin Allah ya tabbatar da alheri, nan suka taso suka fito kowannensu fuskarsa dauke da murmushi, shi dai tafida duk da mai martaba bai fada masa alherin da baban hanfa yayi masa ba yasan alherin mai girma ne nan yaji soyayyar hanfa tasake ratsa shi.
[7:12PM, 11/30/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
9⃣7⃣
Na UMMI A'ISHA
Shirye shirye aka fara domin gudanar da shagalin bikin amma tafida yafi kowa zumudi ita kanta hanfa har mamaki yake bata sai kace bai santa a matsayin ya mace ba saboda komai cewa yake sai a first night dinsu zai fada mata.

Masu gyaran jiki da kunshi da gyaran gashi aka dauko takanas daga garin nijar nan suka shiga gyara hanfa ciki da waje kafin kace wani abu tuni kamaninta sun sauya jikinta yayi sulbi da taushi gamida laushi har wani santsi yakeyi duk da cewa bawai kalarta ce ta canja ba tana nan a bakarta mai duhu amma tayi kyau, tun daga gashin kanta har kafarta sai da aka wanke aka yi mata jan lalle mai kyau, ga gyaran fuska da aka yi mata, yayinda itama gimbiyar faisal zarah tana can ana gyarata, tsakanin tafida da hanfa wayace amma tun kafin ya ganta yabi ya gama rudewa kamar wadda za akwace masa ita.

Yauma hanfa zaune take a makeken falon gidansu kasancewar tafida yabawa babanta gidan da yagina a gonarsa kuma gidan babba ne gashi yasha kayan alatu, daga ita sai daurin kirji gabanta da kaskon turaren wuta tana turara jikinta da turare mai kamshi Wanda ni kaina ummi Aisha sai da naji kamshin ya ratsani, wayarta ce tayi kara murmushi tayi tun kafin ta daga domin tasan tafidane yau tun safe bai ber kunnenta ya huta ba, hello munib tafada ahankali, gaskiya ni ban yarda ba ki canja min suna, dariya tayi kabari sai nazo gidanka sannan zan canja maka sunan, murmushi yayi to shikenan ai saura kwana biyu, dariya tayi anjima zan kiraka, haka suka gama wayar suna cikeda shaukin juna.
Chapter 21 · 0% Book details