← Book details Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 27

Sashe 2

Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Filon kusa dashi tafida yadauka yajefeshi kai dan iska ne idan ni dan ganye ne ai dasauki tunda har yanzu ni saurayine cikakken saurayi kuma, dariya abokin nasa yayi dakyau virgin boy, amma dai abi ahankali banda ganganci,shiru tafida yayi bai kara magana ba domin shi baya doguwar magana idan kajishi yayi magana mai tsawo to da mahaifinsa ne ko mahaifiyarshi ko kuma abokinsa faisal.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [7:23PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE !
6⃣
Na UMMI A'ISHA
Tashi tafida yayi ya shiga daki yahaye gado yakwanta minti kadan faisal yabiyoshi cikin dakin abokina ya zaka kwanta bayan ba mugama magana ba?

Kai malam bana son surutu, eh nasani ai shiyasa nake son na sanar dakai cewa na dauki wadannan kudin naka nayi sadaka dasu, tsaki tafida yayi mtwww to ina fata ba iskanci kaje kayi da kudina ba?

Murmushi faisal yasake yi wai kai finka laifi nayi?

Kaima fa mai laifi ne, kana shan ganye over ni kuma ina neman mata jifa jifa ba koda yaushe ba, murmushi tafida yayi yatashi zaune, to ai ni matan ne ma tsoronsu nake, gaba daya ban san ta inda zanbi ba yanzu haka idan ka ajiye min mace wlh ban san yadda zanyi da itaba, wata irin dariya faisal yayi hahahaha!

Ammafa kacika dan rainin wayo, ta ina kake karbar haihuwa?

Kaida ka karanci mata kasan yadda suke, karfa ka manta kai likitan matane su kake gani kake dubawa akoda yaushe, dan malalacin murmushi tafida yasaki to sai aka fada maka kuma nasan hanyar?

Karya kake kasani mana, dariya tafida yayi kai dan iska ne, wlh duk ranar da mai martaba yasan kana neman mata sai ya tube rawanin da ya daura maka,cikin dariya shima faisal din yace kamar yadda kaima mai martaba zai tube rawanin daya daura maka ba duk ranar da yagane kai mugun dan ganye ne, murmushi tafida yayi ra'ayina shine nasamu cikakkiyar budurwa kamar yadda nake cikakken saurayi, taba baki faisal yayi eh munji kai saurayine amma ai dan ganyene, dariya tafida yayi duk da haka dai nafika,ni yanzu ma ka kyaleni wlh yunwa nakeji sai da inno tace naci abinci dazu nace bacci zanyi amma bari nayi mata waya akawo mana, wayarshi ya dauka kirar yota phone yakira inno yace akawo masa abinci shida faisal ba awani jimaba sai ga kuyangi guda 2 sun shigo hannuwansu dauke da tirarrika na silba manya manya anan suka ajiye suka fita, suna fita faisal ya fara bubbude kwanukan abincin, abinci ne kala kala na gargajiya saukowa tafida yayi suna ci suna hira har suka gama, suna gamawa suka tafi masallaci sukayi salla suka shigo gida afalo faisal yazauna yafara waya da yanmatansa shi kuma tafida yawuce daki yafada kan gado yajanyo tabar wiwi yafara zuka.
7⃣
Washe gari dasafe dr tafida yashirya tsaf cikin shirinsa nafita office bakin wando yasa da bakar t.shirt mai dogon hannu yadora jar jacket asama yasa bakin takalmi cover shoe
[7:38PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: Yafesa turaren fogg yafito lokacin faisal yanata bacci kasancewar shi a ministry for local government yake aiki baya fita dawuri shikuwa tafida 7:30 yasaba fita office, yana fitowa sarkin fada da sarkin mota sukazo suka zube suka fara zabga kirari barka da fitowa mazajen fama hadiri sa gabanka inda kakeso, murucin kan dutsi baka fitoba sai da ka shirya, atafe dakyau, atsaye dakyau amma azaune kafi dadin kallo dan ahmadu jikan sani gyara kintsi giwa kinfi karfin waiwaye, kura ko kin mutu kinfi karfin kare, wani kaya sai amale wane jaki, cikeda takama yace barkanku da safiya yawuce cikin gida yanufi dakin inno mahaifiyarshi alokacin har ta harhada masa kayan karyawarshi tsaf ta zuba acikin akushi mai kyau tana jiran shigowarsa, yana shiga yazube agabanta tana kushingide hannunta rikeda carbi tana ja sukuma bayinta har sun fara aikace aikacen da suka saba yi, barka da asuba inno yafada idonsa akasa, barka da tashi tafida, kafito lfy?

Lfy lau inno, to Allah yabada sa'a, Allah ya tsareka, Allah yadawo dakai lfy, amin inno nabarki lfy, tashi yayi yafita yanufi sashen mai martaba lokacin shima yana zaune afalonsa yana karatun alqur'ani mai girma, cikin girmamawa tafida yadurkusa barka da asuba ranka yadade, cikin murmushi yace yawwa ibrahim har anfito?

To Allah yatsare Allah yabada sa'a, amin mai martaba yafada yatashi yafita inda aka adana motarsa yanufa aka bude masa gidan baya yashiga yazauna cikeda nuna isa yake daddana wayar hannunsa fadawa sai kawo gaisuwa suke yi amma yakasa amsawa,asibitin Rasheed shekoni specialist hospital suka dosa inda tafida yake aiki.
[7:48PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
8⃣
Na UMMI A'ISHA
Suna zuwa kamar kullum yafito yashiga office dinsa wanda yake jere ajerin gwanon ofisoshin kwararru na asibitin, yana zama wata nurse tashigo tana sanye da fararen kaya,morning sir!

Morning ya amsa mata idonsa yana kan laptop dinshi yana daddannawa, sir akwai patient wanda jiya kayiwa operation tofa har yanzu bata farfado ba, cikeda damuwa ya tashi domin shi yana tausayin mata duk lokacin dayaga mace acikin halin rashin lafiya sai yaji kamar zaiyi kuka, maternity yanufa wannan nurse din tana biye dashi abaya ita dai wannan likitan yana burgeta domin yasan aikinsa matsalarsa kawai yanada girman kai ga nuna isa kamar shine sarkin ko dan sarauta ne?

Yahadu sosai ga kudi da sarauta ga ilmi ga uwa uba kyau, yana shiga maternity yafara bin patient din daya bayan daya yana dubasu har yagama yakoma office dinsa alokacin yafara ganin marassa lfy wadanda suka zo ganin likita kuma gaba dayansu matane domin shi mata kawai yake dubawa baya duba maza sai wurin 11 yagama ganin marassa lfy yayi breakfast yatashi yashiga round.
[8:16PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
9⃣
Na UMMI A'ISHA
Yana dawowa daga round yanemi wuri a office dinsa yazauna lokaci lokaci fadawansa suna lekowa domin ganin lafiyarsa, sai misalin karfe 5 yatashi lokacin yafito daga theatre cikin gari suka shiga akan hanyarsu ta tafiyane suka ratsa tawani dan kauye anan yaga wata makekiyar gona wadda akalla zata kai kilo mita 5 anyi shukar shinkafa aciki, shukar tayi kyau sosai sarkin mota ya yiwa magana cewa ya tsaya cikin sauri ya taka birki yaja ya tsaya yabude kofa yafito suma fadawan firfitowa sukayi suka tsattsaya, gonar ya zubawa ido ta kayatar dashi hakika wannan zatayi daidai da wurin da yake nema domin gina business suit dinshi hadida gidan shakatawarsa motar ya koma yashiga ya zauna, fadawansa suka shisshiga suka nufi gida tun da suka shiga yasan cewa mai martaba yau yana fada dan hakan fadan yashiga wacce ta kayatu sosai, mai martaba yana zaune akan wata karagar mulkinsa ta alfarma wadda tasha ado da zinare, gefe daga hannunsa nadama wazirine da galadima ga chiroma, kusa dashi kuma hakimin cikin garine, daga hannun hagu kuma wani dan dattijone zaune wanda shekarunsa zasu kai na mai martaba kusa dashi kuma san turakine wato faisal aminin tafida, cikin sallama tafida yazauna yayi gaisuwa yatashi yashige cikin gida yawuce dakin inno yau bai wani jimaba yafito yashiga dakinsa yayi wanka yafito cikin bakar riga da bakin wando, yanufi lambu wanda yake girke acikin gidan, wurin yasha shukoki na kayan marmari ga wata korama daga tsakiya tana gudana can gefe wasu kujerune hadaddu aka ajiye saboda hutawa kan kujerar yaje yazauna amma ko minti 5 bai yiba yatashi yafita yanufi dakinsa yashiga yakunna tv yakamo tashar kwallo yafara ganin wasan arsenal da man u, wasan yafara kayatar dashi faisal yashigo remote ya dauka yakashe tv din domin yasan yanzu zasuyi fada saboda faisal dan arsenal ne shi kuma tafida dan man u ne gashi ancisu har 2-0 yasan idan faisal yagani yau zai sha tsiya, kusa dashi faisal yazauna.
[8:32PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣0⃣
Na UMMI A'ISHA
Kusa dashi faisal ya zauna yafara dariya ko kallonsa tafida bai yiba yadauke kansa shikuwa faisal sai dariya yakeyi, haushi tafida yafara ji yace ya isheka haka,dariya faisal yayitayi sai da yayi mai isar shi sannan yace kasan me nake yiwa dariya?

Jiya jiyan nan kagama yimun bayanin kaifa bakasan hanyar da zakabi ba awurin mace idanma aka ajiye maka mace bakasan yadda zaka bida itaba to sai gashi yanzu za abaka mace nan da sati 2,kaga ashe kenan ka kusa kasamo hanyar ko?

Wani kallo tafida ya watsa masa ni zanyi aure amma ba yanzu ba sai nan da 3years dariya faisal yakumayi kasan Allah?

Kai angone kakusa ganin hanya, wai kai waya fada maka aure zanyi ne?

Uhm abokina bazaka yarda da abinda nake fada maka ba sai kaji kira daga wurin mai martaba sannan zaka gasgata ni, tsaki tafida yayi insha Allahu kai zai yiwa aure amma baniba,ni daba dan iska ba wa zaiyi min aure yanzu?

Kai da kasan mata kake nemansu ai kai yadace ayiwa aure, dariya faisal yayi kasan Allah?

Wlh kakusa zama ango kai barima kaji dazu daka zo kasamemu da mai martaba wlh maganar aurenka akeyi kuma nan da sati biyu za ayi, cikeda mamaki tafida ya kalleshi wai dagaske kake yi?

Wlh Allah dagaske nake tafida wlh aure mai martaba zaiyi maka dazu akanka mukayi meeting da yamman nan kuma wani abin burgewar ma zaka samu virgin girl kamar yadda kake virgin boy, zumbur tafida yamike ni za ayiwa aure yanzu?

Wanne laifin nayiwa mai martaba da zai hukantani ta wannan hanyar?

Wa zai aura min?

Yaya kamanninta suke?

Girgiza kai faisal yayi wlh ban saniba abokina, to nima dai ummi Aisha ban saniba sai muci gaba da bibiyar tafida, masu karatu muje zuwa kubiyo Aisha.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [8:53PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣1⃣
Na UMMI A'ISHA
Kallon faisal tafida yayi ai kuwa wlh bazai taba yiyuwa ba nikadai ne da agidan?
Chapter 2 · 0% Book details