← Book details Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 27

Sashe 16

Alheri Danko Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

In dai faisal shine tafida to yan matansa naga.
[7:04PM, 11/25/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗
7⃣2⃣
Na UMMI A'ISHA
Tafida daban faisal daban amma ni banida wasu yan mata faisal ne mai yanmata, sai dai nima nakusa nayi budurwa acikin makarantar nan, kallonsa hanfa tayi tafara kokarin kwace yan yatsunta daga hannunsa ai ya halatta kayi tunda an baka dama kayi mata 4 babu laifi, sake damke hannunta yayi yace ni bazanyi 4 ba amma zanyi 2 shine ra'ayina murmushi hanfa tayi duk kuwa da cewa kishi ya tuketa, Allah yabaka ikon yin adalci amin uwar gida yafada yana murmushi, kinga wata fine baby can ko da ita zanyi miki abokiyar zaman?

Waiwayawa hanfa tayi ta hango mami wata yar room 4 tana karantar midwifery bazata fita a haifeta ba yar kano ce daidai lokacin tazo kusa dasu, sauke glass din tafida yayi yace yanmata ji mana, babu musu mami tadawo tace gani, kallon hanfa yayi tayi kicin kicin ta hade girar sama data kasa, yi hakuri dama sako zan baki amma barshi kawai, ok babu matsala amma da ka fadi sakon naka, ki barshi nagode yafada yana daga glass din sama, kallon hanfa yayi kema haka kike da kishi?

Dubawa zakayi sai kagani tafada tana kawar da kanta, to ai gashi naduba nagani kinada kishi, meye abin kishi?

Ni indai ta nine ka auro mata 3 banida damuwa, karya kike kawai dai kin fada ne, amma dagaske fa yarinyar nan kyakkyawa ce, da sauri ta jiyo ta kalleshi dagaske fa kace, to ko dagaske auran nata zakayi?

Eh ai na fada miki aure zan kara sai ku tare lokaci daya, shiyasa kake so kayi min ciki saboda zakayi sabuwar amarya?

Sai kuma hawaye yafara bin kumatunta cikeda mamaki ya kalleta meye abin kuka?

Nifa da wasa nake miki jawota jikinsa yayi ya rungumeta yafara lasar lebenta kidaina kuka wlh wasa nake miki kuma duk kyanta kinfita kyau bata da wani kyau ma, ki kwantar da hankalinki ni ke kadai kin isheni rayuwa kuma wlh banida wasu yan mata, dariya tayi bata shirya ba saboda jin abinda yafara yi mata, sakinta yayi yana dariya wannan dan karamin cikin naki yakusa zama babba, fuskarta ta dauke daga kallonsa ta kalli window,idan kinje kiyiwa zarah sannu kinji, zataji hanfa ta fada tana kokarin bude kofar motar, kayanta yafito mata dasu ta dauka ta tafi hostel.
[7:22PM, 11/25/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗
7⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Juyawa tafida yayi yatafi yana cike da kewar matarsa ya nufi asibiti domin yanada theatre.

Ita kuwa hanfa hostel tashiga hannunta dauke da kaya niki niki lokacin zarah har ta dan warware shewa zarah tafara yi dakyau mrs tafida muma mun zama yan gayu mun daina amfani da stove mun dawo girki da gas, zama hanfa tayi tana dariya kwarai kam, ai ke kam kinyi sa'a tafida yana ji dake ban san me kika bashi haka ba yabi ya rude, ke kika sani kuma hanfa tafada tana murmushi domin ita kanta tasan tafida yana sonta saboda abubuwan da yake yi mata kadai sun isa su tabbatar da hakan, lumshe idonta tayi ta fara hango soyayyarsa mai dadi da tsayawa arai, haka tayita gudanar da abubuwanta cikin nishadi da annashuwa amma tun daga ranar tafida bai kara shigowa school dinsu ba saboda wai baya so yazo yaganta tayar masa da hankali zata yi alhalin kuma tana fashin salla ba wani abune zai gudana a tsakaninsu ba, haka yayita daurewa amma kullum yana yi mata waya ta wayar zarah.

Ana igobe zata fara salla tashirya tayi tafiyarta disina bayan sun gama waya da tafida amma bata sanar dashi zata tafi gida ba saboda tasan idan tafada masa zaiyi amfani da karfin ikon igiyoyin aurensa dake kanta ya hanata tafiya tunda yanzu a karkashin ikonsa take, haka taware abinta batare da saninsa ba shi kam tafida alla alla yake jibi tayi domin lokacin yasan tagama period yaje ya dauketa amma koda dare yayi yakira zarah yace tabashi matarsa sai zarah tayi mamaki tace bata fada maka dama zata tafi disina ba?

Gabansa yaji yafadi yaushe ta tafi?

Wlh da safe lokacin da kuka gama waya ta tafi, amma da nasan bata fada maka ba wlh da nafada maka, yaushe zata dawo?

Sai nan da 3 weeks wlh, to zarah nagode sai da safe yafada cikeda damuwa.
[9:06AM, 11/26/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗
7⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Ajiye wayar tafida yayi cikeda bacin rai, har tayi tafiya bata sanar dani ba ina matsayin mijinta?

Yayi mata kyau yafada afili nan ya kwanta yana mai cikeda kunar rai ahaka faisal yazo ya riskeshi awannan halin shi dai agaskiya yanada bukatar matarsa dan haka gobe ko jibi zai je disina koda kuwa mahaifin hanfa zai koroshi haka ranar yayi bacci cikin damuwa.

Wayewar garin ranar bai samu yaje disina ba saboda patients din da ya wuni yana dubawa dan haka washe gari yashirya tsaf cikin shadda mai tsada fara yasa hula yasha turaren active man yatafi disina shi kadai yatafi bai tafi da kowa ba domin acewarsa sirrinsa zai je yagano.

Karfe 11:30 ya isa gidansu hanfa yana yin packing yafara tunanin ta yadda zai tunkari gidan, ta maza yayi sannan yafito yashiga gidan yana sallama baban hanfa ne yafito yana ganinsa ya murtuke fuska yafara tambayarsa me kadawo yimin agida?

Ban gaya maka kar nasake ganin kafarka agidana ba?

Maza maza ka fice min daga gida kar nasake ganinka agidana har abada sannan kuma ban yarda kasake koda magana da yata ba bare har kabita makaranta, cikeda damuwa tafida yace dan Allah baba kayi hakuri, ka fitar min agida nace kuma ko kofar gidana ban yarda kasake zuwaba, zubewa tafida yayi yafara rokonsa amma bai saurareshi ba haka ya koreshi fata fata nan fa idon tafida yakada yayi jawur yafita yashiga motarsa yatafi, gudu yake shararawa bana hankali ba ga faisal yanata yi masa waya amma bai dauka ba daf da zai shiga garin misau wata tirela tayi gaba da motarsa ji kake taratsatsatsa tafida bai tashi ganinsa ba sai agadon asibiti, gasu faisal da mai martaba tsaye akansa inno kuwa da momcy sai kuka sukeyi, ya bugu sosai ya karye a hakarkarinsa na dama gashi hatta harshensa ma ya tsage gida biyu banda daddaujewa da yayi, wani likita ne ya shigo yaduba shi anan yace ana bukatar za akara masa jini, jinin faisal akaje aka diba aka kara masa, gaba daya kamanninsa sun canja ko magana baya iya yi duk wanda yaga motar daya yi accident din da ita kuwa bazai yi zaton ya rayuba saboda yadda tayi kwatsa kwatsa, shi kansa faisal duk dauriya irin tasa sai da ya zubarwa da tafida hawaye.
[9:12AM, 11/26/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗
7⃣5⃣
Na UMMI A'ISHA
Lokacin da labari yajewa gidansu hanfa iyayenta suka taso sukazo dubashi alokacin baya gane wanda yake kansa hakuri baban hanfa yafara bashi tareda cewa yabashi hanfa ko yau yake son kawota gidansa yaje yadauko ta,har suka tafi tafida bai san abinda ake yi ba, bayan tafiyarsu da kwana 2 iyayen hanfa suka ce tashirya tazo tayi jinyar mijinta babu musu ta shirya ta taho saboda dama kawai dauriya take amma tana cikin damuwa, asibitin tafara zuwa itada zarah sulaiman anan tasamu faisal da mai martaba da momcy, sunyi murnar ganinta sosai tareda jajantawa juna, lokacin dataga tafida kuwa kawai kuka ta fara saboda yana jin jiki.

Kwananta 2 a asibitin yafara gane komai har yana dan bude baki yayi magana dayake an cire dinkin da aka yiwa harshensa, zarah kuwa kullum tana zuwa dubashi daga sch, ko abinci ta ruwa ake bashi amma jikin nasa yadanyi sauki.

Kwananta 5 yafara magana radau, tana zaune agefen gadon yabude idonsa babu kowa adakin sai su 2 magana yafara yi mata ahankali, hanfa nasan mutuwa zanyi amma ko namutu faisal kawai na yarda ki aura domin shine dan uwana kuma aminina sannan abokina kiyi hakuri hanfa yana fada yana hawaye, cikin hawayen itama tace bazaka mutu yanzu ba tafida insha Allahu ba yanzu zaka mutuba bakinta tasa akan nashi tafara yadda yasaba yi mata duk lokacin da suka hadu wato zagaye lips dinta da harshensa, hanfa mutuwa zanyi nafada miki rungumeshi tayi ba mutuwa zakayi ba tafida ko kamanta da abinda ka fada min?

A kunnensa ta rada masa so kake ka mutu ba kayi min cikin ba?

Murmushi tafida yayi itama murmushin tafara yi ga hawaye kuma akan kumatunta hannunsa yasa acikin rigarta yafara shafa cikinta zaki haifa min baby?

Kai tadaga cikeda jin kunya, ganin wasan nasa zaiyi yawa yasata tashi taje tasawa kofar dakin key tadawo, kokarin cire rigarta yafara yi da hannunsa guda daya mai lafiya, taimaka masa tayi tacire rigar nan fa yafara sarrafata da hannu daya.

Sai da ya nishantu sannan ya rabuda ita, jin ana kwankwasa kofa yasa hanfa tashi tasaka rigarta da hijab dinta ta nufi kofar dakin tabude, faisal ne yashigo shida wata bakuwa suna shigowa faisal din yafita ita kuma bakuwar takarasa ciki daidai lokacin tafida yafarka yabude idonsa akan kujerar dake gaban gadon tazauna tana fadin sannu baby, cikin sauri hanfa ta kalleta baby kuma?

Hmmm wai nidai ummi Aisha nayi nan.

Ausar!

Ausar!
Chapter 16 · 0% Book details