← Book details Akwai Lokaci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 19

Sashe 9

Akwai Lokaci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kallisu hajiya rukayya tace tabbas meenat kawata tace kamar yadda tafada muku
Sauran bayani zata muku

Tawuce abinta cikin part dinta

Daga Laila har hajiya rukayya baki sukabita dashi

Cikin kuka meenat tace kunganiko dakunganiko nafada muku kawatace
Wallahi dakun barni naje naci ubanta

Laila tace rabu da ita dole musam abinyi tunda abin yakai haka

Hakeem nafitowa daga massalaci yaga motar Ahmed
Yakarasa gurin motar

Ahmad tafito yace kaganni kenan Hakeem yayi murmushi yace ai inafitowa naga motarka

Yace mukarasa ciki mana Ahmad yace a a mushiga mota kawai muyi maganar

Nan suka shiga Hakeem yaba wa Ahmad labarin komai zuwan meenat

Ahmad yasauke numfashi yace kasan mena fahimta a wannan labarin
Hakeem yace saika fada

Ahmad yace Husnah tasan meenat zai iya yuwuwa kawartace kaman yadda meenat tace

Akwai dai dalilin dayasa husnah taki nuna tasan meenat

Yakamata ka lallabata tafada maka komai

Hakeem yace hakane nima naso nafahimce hakan

amma maizaisa meeanat ta dage ita saina saki matata

Akan husnah zansaba mata wallahi daga ita har uwarta dansu suke Dada bata min yarinya

Ahmad yace a dama aibazaka rabuda matarka saboda
Wannan daliliba
amma inaso kasani fa akwai takaici kawarka ta auri mahaifinka

Dole meenat zataji ba dadi

Hakeem yace kuma husnah bata taba sanin nineahaifin meenat ba sai ranar dataga ta a hoto

amma naga tayi murmushi Dana tambayeta murmushin metake tace min bakomai

Ahmad yace ganiba tabbas akwai wani Abu

Hakeem yace kwarai kuwa amma nasan yadda zanyi zangano koma menene

Nan sukayi sallama da Ahmad
Shikuma Hakeem yatsaya a massalaci don sallar isha

Husnah tashirya cikin wasu arnar kayan bacci masu matukar kyau tafeshe jiki ta da turare
Takoina yadau kamshi ta hada gashinta guri daya da ribbon

Kafin tabude fridge din kitchen dinta tadau fruit salad din data hadawa mijinta tadauki dogon hijabinta tasaka

Tadauki abinda zata dauka tayi waje tayi sama abinta cikin farin ciki

Hakeem yadawo daga massallaci yabi wajensu mummy

Mummy tace Dan Allah kaba wa husnah hakurin abinda tagani yau

Mutanan basuda imani fa
Ni anya bazan fasa tafiyan nan bakuwa

Hakeem yace saboda mezakifasa mummy

Mummy hafsat tace sunban tsoro ne ai karama susata agaba
amana ce fa a hanunmu idan muka bari wani Abu yasameta Allah bazai barmu ba
Yarinyace karama

Hakeem yace karkidamu mummy
Insha Allah ba abinda zaifaru mummy

Mummy tace shikenan Allah yadada karewa yace ameen

Mummy tace tashi kaje gurin matarka kabarta itadai

Yama mummy saida

Yana Shiga falon baiga kowaba
Ya wuce saman shi

Yanashiga kamshin ta yadaki hancinsa

Tana zaune kafanta daya kan daya
Rigar mesharara ce sai yana da siririn hanu sannan kuma dai dai cinyarta yatsaya ba abinda ba gani a jikinta

Ga sambala balan cinyoyinta masu tsantsi da laushi
Da kuma daukar ido

Cikin yanga da Jan hankali ta taso tarungumshi
Hakeem sumane kawai baiba saboda gaskiya shigar ya kayatar dashi sosai

Nan da nan kwadayinshi yatashi akanta

Sosai ya matseta ajikinsa
Yana shin shinnanta yamata rada akunne tayi murmushi tace saikaci abincinka

Yace ai nakoshima Ganin wannan wanka ma ai wadatar dani sosai

Husnah takama hancinsa tace naki wayon ta matsa cikinshi tace ji cikinka bakomai kaman wani silipas

Shima dariya yayi yashafa cikin nata yace harkura zatace wa kare maye
Ji cikin kifa

Tace aini hallittace duk abinci da zanci cikina bazai tashi amma kaifa idan kaci abinci sosai katoto cikin ka yakema

Hakeem yayi murmushi yadauketa cak dining dakanta tayi feeding dinshi
Shima yabata kafin suka tashi zuwa bedroom wanka suka fara

Indai suna tare komai tare sukeyinsa
Shiyasa wani shakuwa metsanani yashiga tsakanin su takama idan baranar kwananta bane

Hakeem cikin kunci da kewa yake

Sosai yasamu abinda yakeso agurinta tacire mishi duk wani damuwar dasu meenat da uwarta suka sashi

Sai da komai yakammala sannan Hakeem yadawo hankalinshi
Cikin tsananin son matarshi yarungumeta

Shikanshi yasan tana kokari dashi sosai bata taba hanashi kantaba

Duk da yasantana wahala sosai danshi din yasan Jan gwarzo ne

Yana rumgume da ita ya kalli beautiful face dinta ya manna mata kiss abaki

Nan yashiga tunanin abinda yasa husnah taki amincewa tasan meenat
Yasan tabbas akwai wani Abu haka kawai husnah bazata nuna mata haka
Kuma yana da tabbacin husnah ce da gaskiya

Dan yasan halin 'yarshi sarai

Agogo yaduba yaga time shabiyu darabi nadare
Badama yakira ya shamsu yanzu amma zaibari zuwa gobe yakirashi yamishi tambaya

Yarungemeta sosai ajikinta sosai ahaka bacci yayi awungaba dasu

Dasafe bayan husnah da Hakeem su shirya cikin shigata alfarma
Cikin wani rantsatstsan less
Maroon colour yayi matukar kyau tasaka farin mayafi da farin takalmi

Shima Hakeem cikin dark maroon shadda
Yayi balain karbarshi

Husnah kuwa ta maka wata dambareriyar sarka tasaka na zinari

Tare suka fito zuwa kasa

Meenat suka hada ido husnah tasakar mata harara
Itakuma husnah tasakar mata murmushi

Meenat tace ina kwana daddy
Yace lafiya qalau
Suby ma tagaisheshi ya amsa yace wa meenat bataga antynta bane bazata gaisheta ba meenat tayi shiru

Husnah tayi sauri tace Dan Allah sweet kabarta bakomai wallahi watarana zata gane

Hakeem yafita abinshi

Husnah takalli Laila tace mama zamuje kai mummy air port sai mundawo kafin suyi magana tafita

Laila kuwa inbanda kallon takaici ba abinda take bin su dashi
Shiyasa ma Hakeem yayi banza da ita sukayi waje zuwa part din mummy

Mummy tace ina suke subazasuzo muyi sallama ba

Hakeem yace muje kawai mummy Daddy yace a a ke 'yata kiramin matata muyi sallama

Husnah tayi murmushi tace to daddy
Tasan meenat yake nufi kenan

Tawuce zuwa falonsu tace amina Hakeem daddy na kiranki kafin amina tace wani Abu husnah tajuya abinta

Meenat tace wallahi mummy idan nabar yarinyar nan nacutu

Laila tace kedai kwantar da hankalinki kije kiji medadin zaimiki kidawo
ai nata yazo karshe agidan nan

Meenat tana zuwa falon daddyn Hakeem yace haba amaryata shine bazakizo nagankiba muyi sallama

Meenat ta kakalo murmushi tace yahakuri grand wallahi kaina yake ciwo yace asha kinsha magani kuwa meenat tace nasha yace to Allah yakara sauki ko

Wannan in Allah ya dawo damu lafiya
Zanzo hargidan ki kinji ko 'yar albarka

Meenat tace to grand Allah yadawo daku lafiya yaciro cheque yayi signed yabata na zunzurutun kudi jar 1 million

Sosai meenat tayi godiya tafita
Dan bata San Ganin husnah da ubanta

*****
Da yamma Hakeem nazaune shikadai a falonshi yakira ya shamsu a waya suka gaisa

Hakeem yace Dan Allah ya shamsu wata yar tambaya zanmaka

Koka kasan wata kawar husnah mesuna amina wacce sukayi makaranta tare

Ya shamsu yace kwarai inajin sunan sosai agurinta sai dai bamu taba haduwa daitaba

Hakeem yace nagode kwarai
amma har suka bar school suna tare kuwa

Ya shamsu gaskiya a a saboda natambayeta akan dalilin dayasa suka rabu taki sanar dani

amma lafiya kuwa yallabai kake wannan tambayar

Hakeem yace lafiya qalau karkadamu nagode sai anjima sukayi sallama

Shigowar Laila kenan yanagama wayar

Ta kalleshi sannu da hutawa daddyn meenat Hakeem yace yauwa

Yau itace da oga shiyasa take ta rawar kai itaga memiji

Hakeem yacigaba da aikin dayakeyi a computer

Laila tace na hado ma coffee ne yace no karkidamu
Barshi kawai

Ya tashi zuwa bedroom yana waya
Bashir sirikinsa yake kira

Yadauka cikin girmamawa yagaida Hakeem

Sannan yamishi yajiki Hakeem yace jiki kuma ni

Saikuma kawai ya wayance
Yace idan bazaka damuba inason ganinka yau din nan

Bashir yace bakomai insha Allah zanzo Allah yakara maka lafiya

Hakeem yace ameen ameen nagode sosai yakashe wayar harcikin ran Hakeem yanason bashir sosai saboda baya rainashi kokadan baya duba bawani shima ba wani girman shi yayi

Dan zai girmi bashir da shekaru irin biyar zuwa shida

Laila tashigo cikin dakin tace baban meenat kai dawaye haka kace kanason ganinshi yau

Hakeem yace idan yazo zakiganshi

Wajen karfe biyar na yamma YOUNG PROF yasauko cikin jallabiyarsa yagansu gaba dayansu a falon yau harda hajiya suwaiba da hajiya rukayya duk sunzo

Meenat ce bata falon yace sannunku da zuwa hajiya

Nan suka washe baki ganin yasake musu

Zama yayi cikin daya cikin kujerun falon ya kalli suby yace ke kiramin amina

Suby ta tashi taje takira amina

Meenat tazo cikin doguwar rigar abayanta tazauna gaban daddynta tace gani daddy

Ya kalleta yace kinci abinci kuwa tayi shiru

Suby tace takicin komai tunsafe
Hakeem yace jeki debo min abincinta

Suby taje takawo yakarba yace wa meenat zakici nasa arike minke namiki dure ko yakarasa yana murmushi

Wanda hakan yasanyaya ran amina da uwarta dama duk Wanda kefalon

Amina takarba abinci taci agabanta daddyn ta yabude ruwa maisanyi dakanshi yazuba mata tasha

Sallama suka ji Hakeem ya amsa yace karaso ciki malam bashir jin sunan daya ambata cikin meenat yabada wani kulululu

Bashir yashigo yagaida mutan falon sannan yazauna yana fuskantar prof

Hakeem yadauki phone dinshi yayi dialing number husnah dake cikin dakinta yace

Baby fito falo kugaisa da bako ko tace OK sweet Ganin zuwa

Fitowar husnah daga part dinta yayi dai dai da dagowar
Bashir daga sankuyon dayayi dakai

aikuwa a razane yatashi yana nuna ta da hanu

Next page

Your comments is needed fan's

Love all 😘😘😘😘😘😘😘

📝📝📝📝📖📖📖📝📝📖
[05/05, 10:18 PM] UMMU AFAN 🌹: 🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗
🎗
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Story & written
By
The special writer

UMMU AFAN

🖊🖊🖊🖊🖊🖊📚

🌹FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION🌹

🌹🌹 (F.C.T.W.A)🌹🌹

🌹HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION🌹

🎗I DEDICATE THIS PAGE TO YOU FATIMA SUNUSI SANAYA ina alfahari dake wajen nice comments wallahi Allah yabar zumunci keep it up page saboda kina kara min kwarin gwiwa sosai😘😘😘😘😘😘🎗

🎗AKWAI LOKACI 🎗

🎗PAGE 141 to 142🎗

HAKEEM yakai kallonshi ga Husnah data nuna kaman bata sanshi

Bashir yace mene ke gani asmau
Mekikeyi anan

Husnah tayi murmushi takaraso tazauna a hanun kujerar da Hakeem yake zaune tace uncle bash
Anzo lafiya ya hanyar

Bashir kawai yasake baki yana kallonta yadda kasan ba komai a tsakaninsu

Hakeem yace kasanta ne bashir yadaga kai da sauri yace sosai ma dalibatace itada meenat da ita zan aura

Laila da suby suka dau salati suna kallon kallo

Hajiya rukayya kuwa zufa yajikata sharkaf
Saboda rashin gaskiya

Hakeem yayi murmushi gefen baki
Ya kalli husnah yace baby kinsanshi daman tace a copper ne a school dinmu

Yace daga bawani Abu takalli bash ta kalli meenat da jikinta yake bari
Chapter 9 · 0% Book details