← Book details Akwai Lokaci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Akwai Lokaci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Husnah tace mummy kigafarceni amma banzan taba zama inga kina shiga kitchen

Yakamata kema kihuta Dan Allah

Tunda na taso agidan mu Nina ke abinci umma ta na hutar da ita saboda haka Dan Allah mummy kibari na ringa miki abinci kihuta kema kisan kinada yarinya a yanzu

Cike da mamakin kalaman husnah mummy tace lalle husnah kin haifu Allah ya wa iyayenki albarka dasuka miki tarbiya maikyau

Nagode da kika daukeni matsayin uwa
Allah yabaku zaman lafiya keda mijinki yazaunar daku lafiya kinjiko

Husnah kai akasa tayi shiru

Mummy tace na'amince zaki rinkawa mummy abinci amma fa mummy ma tayi alkawarin satayi sati kina cin abincin mummy kinjiko

Saboda haka kibar mummy tacika alkawarin ta

Husnah tayi murmushi kawai kafin tayi magana

Hakeem yayi gyaran murya mummy da husnah suka kalleshi

Mummy tace wato labe kake mana ko

Hakeem yayi murmushi yakaraso cikin kitchen din

Yakama hanun mummy yace haba mummy please kibar yarinki tasamu ladarki

Allah ne ya amsa adduarki yakawo mana husnah cikin rayuwar mu

Kinji mummyna

Mummy hafsat tayi murmushi tace shikenan tunda kunmin yawa Allah yayi albarka

amma bayanzu za adaura abinciba sai yamma idan anyi la'asar
Yanzu muje kawai muyi hirar mu

Mummy taja hanun husnah wacce tunda Hakeem yashigo takasa magana

Ranar dai a sashin mummy husnah ta wuni sai da ka kira isha tabar dakin mummy ganin Hakeem da daddy sunfita sallah

Mummy tace yau husnah Allah yatashemu ki huta gajiya ko

Ita mummy a tunaninta husnah zata je tashirya ne kafin mijinta yasameta

Husnah kuwa tashiga falon taga Laila da suby a zaune

Ta wuce abinta batareda ta kalli kowa ba

aikuwa suby tace ke zonan

Kojuyowa husnah batayi bare ma tasan da ita sukeyi

Ke 'yar talakwa bakiji menace bane husnah tayi banza dasu kafin suby ta karaso husnah tashige ta banko kofarta tasaka key

Direct wanka tafara kafin tayi sallah tayi karatun ta data saba

Suby tace anty anya kuwa ba wannan aljanar yarinyar bane kishiyarki kuwa

aikuwa jitayi Laila ta zabga mata mari

Suby tace mena miki anty Laila

Cikin tashin hankali Laila tace damme zaki min wannan mugun fatan

Taya za ayi yaje ya auro 'yar cikinsa

Bama hakaba idan yakasance wannan yarinyar ce ai yayi abinkuya
Nikuma nashiga uku taya zafara kishi da wannan yarinyar

Suby tace aiko dai koki kokiso itace
Dan agabanki tasa mukulli ta bude sashinta kuma dazu Dana kai mata abincin ma ita nagani kawai raina mana hankali take

Laila ta daura hanu akai tace nashiga uku ni Laila wannan ai inaganin ko meenat ma ai tagir meta
Lalle Hakeem yacuceni

Yanzu sakayya da zaimin kenan ya auro 'yar cikina inyi kishi da aita ina Sam bazaiyuba wallahi

Suby tace wallahi idan kika bari aljanar yarinyar tazauna agidan nan

Zikidawo jaka wallahi Dan abinda kike samu bazaki samu ba

Yarinya kaman ita tayi kanta Dan kyau tahada komai da d'anamiji yake bukata

Laila tace ya isa haka suby zakisa zuciyata tafashe kibarni naji da Abu daya Dan Allah

Hakeem yashigo falon da sallama Laila ta taso sannu da zuwa baban meenat

Hakeem yace yauwa yashige bedroom dinshi Dan karya taba kofar husnah yaji akulle agabasu su fahimci wani Abu

Laila tabishi har yafito Daga wanka yana yashirya ya kwanta

Laila taga bashida niyar kulata yasata ce baban meenat har yanzu fa bansan kanwartawaba

Sai kanwarta muke ta gani tana shige da fice

Hakeem yayi murmushi Dan ta tabo inda yake mishi kaikayi

Yace kanwa kuma ai bata da kanwa itadai wacce kikagani din itace amaryata

aikuwa Laila ta tashi tace amma wallahi kaji kunya Hakeem yanzu da girman ka da darajarka zaka auro 'yar cikinka wannan ma ai zubda mutuncin Kaine da zubar wa 'yarka da mutunci

Prof baki kawai yasake kallon ta
Yayi murmushi yace kinyi sake maman meenat da kika auri mijin asmau saboda yanzu nasan nima namijine kuma na auri dai dai Dani kije aduba miki nidake bamu taba dacewa ba kuma bazamu daceba

Meenat da Allah yabani na karba kuma inason 'yata
Idan tazo ruwantane taso matata ruwantane takita

amma zanfada miki wannan Kalmar mummy da daddyne kawai bazan iya rabuwa dasu ba saboda husnah

Amma bayansu zan sabama kowa akan matata so get out of my room

Cikin tashin hankali Laila tafito Daga bedroom din Hakeem

Kuka sosai taci suby nabata hankuri

****

Bayan sati uku Hakeem ya Dade da komawa aikinsa gashi aikin yamishi yawa ga kullum tunanin husnah ne da sha'warta acikin ranshi

Ba inda yake samun ganinta sai a part din umma Dan Anna take wuninta

Tana fita sallar isha zata gudu

Hakeem zaune kan kujerar office dinsa Ahmad kuma yana cike wani file's

Ahmad yace yauwa kagani ko yana nuna wa Hakeem abinda yacike
amma hankalinsa baya taredashi

Ahmad yace wai meke faruwane Prof
Hakeem yayi murmushi wallahi baby ce take bani ciwonkai

Taki bari na rabeta Sam wallahi
Bana ganinta idan ba a gurin mummy ba

Ahmad yace zanbaka shawara idankabi yau din nan kadaina damuwa

Hakeem yabada hankalinsa sosai

Ahmad yace bakace agurin mummy take wuniba prof yace a

Ahmad yace sallar ishar dazakaje yau kabari kawai kamuku jam'i

Kana shiga kacewa mummya da daddy da ciwon kai kadawo

Idan kaga zata tashi saikace jirani mutafi tare agaban mummy nasan bazatayi musu ba

Hakeem yace kuma wallahi sai dai kuma yau laila ce da kwana

Ahmad yace saikayi hakuri yau da gobe ai duk dayane yayi dariya

Hakeem yace a a baduk dayabane wallahi kai bakasan halin danake cikibane shiyasa

Ahmad yace kai haba mai mata biyu fa amma kana fadin haka ai saika kabani tsoro nakasa kara tabiyu

Hakeem ya harareshi

Husnah falonta suna waya da ummanta da ya shamsu da anty kubra

Bayan sunagama wayarne ta dauko mayafinta zata koma banngaren mummy

Sai taji Laila tana waya amma bata San dawa take ba

Laila tace dadin abinma fa yarinyar baso shi take kullum a dakinta take kwana
amma wannan aikin bokane yace bazai taba bari harya kusanceta ba

Yanzu fa kusan sati uku kenan amma suna wasan buya bata ma bari yaganta

Shikuma na mamajo kina gani shi kisan yana cikin damuwa

Can ta matse mishi kinga haka malam zaicire mishi sonta aranshi kwatata

Dan nima yace karnabari ya kusanceni har sai yarinyar tabar gidan

Kinga kuwa ai yana cikin matsala dannima bana zuwa bedroom dinsa harsai ranar da wannan aljanar yarinyar tabar gidan

Nan dai sukayi sallama da kawartata

Ta kalli suby tace insha Allah saura kiris yarinyar nan tabar gidan nan

Daga nan kuma sai mufara shirin yadda zamuyi mukasheshi idanba haka ba wallahi wata zaisake hangowa

Suby tace wallahi da dai yafikam
Dan wallahi nima inason naga munfara fantamawa fa anty

Laila tace kidai yishirunki kawai saura kiris

Husnah toshe baki tayi sai kuma wani jiri data ji yana dibanta dakyar tasamu takai kanta kan kujerarta

Tace innalillahi qainnairraihirraju'un nashiga uku meya musu suke son kasheshi

Gaskiya bazantabari kuyi nasara da yardar Allah

Kuma mijina zaisamu abinda yakeso insha Allah

Allah yakaimu gobe nashiga ukuna ni husnah wani irin zunubi na daukarwa kaina

Tabbas yaya Hakeem bai can canci wannan sakaiyar daga garaniba kayafemin Dan Allah duk da banasonka nayi alkawarin faranta maka kamar yadda kake faranta mana nida iyayena

Duk wannan maganar da husnah take yi tanayinsane itakadai

Hmmmmmmmm

Next page

Your comment is needed fan's. Love u all

Duk wacce bantaba bata page ba

Tayi comments mezafi next page natane 😘😘

📝📝📝📖📖📖
[05/05, 8:59 PM] UMMU AFAN 🌹: 🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗
🎗
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Story & written
By
The special writer

UMMU AFAN

🖊🖊🖊🖊🖊🖊📚

🌹FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION🌹

🌹🌹 (F.C.T.W.A)🌹🌹

🌹HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION🌹

🎗I DEDICATE THIS PAGE TO YOU MAMAN ISQAH Allah yabar zumunci gaskiya ina alfahari dake wajen comments keep it up d🎗

🎗AKWAI LOKACI 🎗

🎗PAGE 106 to 110🎗

Husnah ce a kitchen din mummy tana ta aikin abinci Dan yau abincin ma special ne

Sakwara takeyi da spinach soup Wanda yasha ganda

Kamshi ya kauraye koina

Sai data gama komai tasaka a flasks dama ta hada
Hadaddan zobonta meshegen dadi da kamshin kayan hadi

Ta jera komai a dining din mummy hafsat yayin da me aikin mummy take gyaran kitchen da wanke wanke

Husnah ta duba agogo taga karfe biyar dai dai ta haura sama gurin mummy

Direct dakin mummy ta wuce tasameta itama tagama shirin ta tana ma shirin saukowa kasane

Mummy hafsat ta kalleta tace
Sannu da aiki 'yar albarka ina ta sauri nasauko naga me ake girka mana gida duk ya dau kamshi

Husnah tayi murmushi tace abinda kikace min dadi yafiso shinayi yau mummy

Mummy hafsat tace sakwara kenan fa Husnah tadaga kai

Mummy tayi murmushi tace ai masu son suna dayawa harda son iyayen ci

Yau zakiga santi husnah tayi murmushi

Tace mummy ina son zanje nayi Dan gyare gyare ne

Mummy tace bakomai 'yar albarka ai kina kokari Allah yayi albarka

Husnah tace amin mummy

Husnah harzata Fita mummy hafsat tace kiwuce muku da naku can kawai tunda nasan kinyi aiki kingaji ba lalle kisamu daman dawowaba

Husnah dama abinda takeson mummy tace kenan

Tayi murmushi tace to mummy sai da safe

Mummy tace Allah yabamu alkairi

Husnah tafito tawuce part dinsu tana shiga falon taga su hajiya rukayya harda hajiya suwaiba yauma sunzo

Dan kusan kullum suna gidan

Husnah tace ina wuninku hajiya
Kosusan Allah yayi ruwan tsiranta

Ita kuwa husnah ganin ba Wanda ya amsa mata yasa ta tashi tayi ciki abinta

Direct kitchen dinta tashiga tafito da sabbin food flask masu kyau da tsada tayi part din mummy tazuba musu abinci

Tadauki jug din flask din tazubo musu zobo maisanyi Wanda dama tasaka a fridge

Harda fruit salad din data hada duk ta deba tayi part dinsu

Ganinta da flask duk suka bita da kallo tayi dakinta dasu tajerasu a dining table dinta

Kafin ta fito tasawa kofar ta key nan ma su Laila suka bita da kallo abin mamaki gani sukayi ta haura saman Abdul Hakeem

aikuwa Laila da suby suka kalli juna sukabita da kallo

Tana shiga tasa hanu ta murda aikuwa tayi sa a ba akulle bane
Tashiga wani makeken falo ta gani har yaso yafi nakasa kyau sai dai duk yayi kura Dan dagani bayasamun kulawa
Chapter 2 · 0% Book details