← Book details Akwai Lokaci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 19

Sashe 3

Akwai Lokaci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakuna biyu ta gani cikin tabude nafarko taga nan ma wani hadaddan bedroom ne amma Daga ba anan yake kwanaba

Tabude dayarma tagashima yahadu iyahaduwa
Kuma dagani nan yake rayuwa

Shiga tayi harta kan bed dinma ba agyare yake ba
Kuma bata ga laifinsaba zaiji da office ne kozaiji da da gyaran gidanshi

Nan dai duk wasu kayanshi datake tsammanin yasaka tahadasu a gefe Dan bazaka gane dattin ba saima kamshi dasuketashi Daga miki su tana cikin binko kayansa wani Dan akwati ta gani yamata kyau sosai

Garin ta gyara mashi zama sai yafafo kayan ciki cuka zubo

Ba abinda tafara gani sai fuska(masks)/kuma da ya mu'alim yake kama sak abin har yaso yabata tsoro zata gudu idonta yakai kan nokia yarsa wacce tasha dauri da roba

Cikin tsananin mamaki husnah tace badai ya Hakeem shine ya mua'allim dina bansaniba

To meye hujarsa na boye kansa
Tasake bincika kayan taga zoben data bashi Wanda sukayi canji yabata tabashi

Nan tasake tabbatarwa kanta ya Hakeem shine ya mu'allim

Taga wani diary kamar yadda taga anrubuta a bayan littafin

Nan ta hau karanta abinda ke rubuce

Nan ta tababbatar Abdul Hakeem shine ya mu'allim dinta

Kukan dadi suka gangaro mata

Sosai tayi kuka ammafa na murna ne
Tace meyasa zaka cutar da kanka har haka meyasa baka fada minba kabari har na dauki alhakinka ya mua'llim

amma bakomai insha Allahu zakasan kayi auren soyayya
Ya Allah ka karemin mijina Daga sharrin wadan nan mutanen tabas a labarin dake rubuce cikin diary dinshi mummy hafsat da daddynsa sunbata tausayi

Dole ya mua'llim yayi taka tsan tsan gurin sake Neman matar
Baka da laifi kuma na tabbatar kosu umma da ya shamsu bazasu zargekaba idan sukaji Kaine ya mua'llim kuma suka ji dalilinka

Wani irin son mijinta yadawo sabo fil azuciyarta tareda tausayinsa Dana iyayensa tashare hawayenta tashiga yin abinda yakawota cikin farinciki da dokin dawowar mijinta

Acikin mitoci kadan daki yakoma kaman bashiba kafin tashiga bathroom dinsa ta wanke mishi kayansa tsaf da kananun kayansa na ciki

Taje farandar saman shi ta shanyasu tsaf tasaka abin kamawa ta kamasu karsu fadi kasa

Tagyara bathroom dim ma tasaka kayan kamshi koina ya San anayi

Kafin kuma ta koma falon tagyara tsaf yadawo kaman bashi ba sai sanyayyar kamshin dake tashi akowani lungu da sako na falon

Sai da ta tabbatar ba inda bata gyara ba kafin tafito key din dake jikin kofar tacire ta cire ta kullo saman abinta

Ta wuce da keyn har yanzu su Laila suna inda tabarsu

Zata shige dakinta hajiya rukayya tace ke zonan yanzu agidanku haka kikewa manyanki

Husnah tadago ido takallesu

Batayi magana ba tayi shiru Dan taga ba abokan yinta bane

Suby tace ke 'yar marasa kunya ba magana akemikiba

Husnah ta kalle suby sama da kasa tace kekuma fa 'yar masu kunya ya akayi

Laila tace kutuman uba lalle yarinyar nan ma kinsamu guri

Uban me yakaiki saman dakin mijina

Husnah ta tashi tsaye ta kalli Laila sama da kasa tayi dariya
Tace ai gwamma da kika nuna min kece matar gidan Dan gaskiya na kasa tan tancewa acikin Ku hudun nan
amma yanzu kinga nasani

Maganar miji kuma point of correction mujimmu zakice please kina saka munjaye idan zaki furta kallma kamar haka

Kafin ta kalli suby ta banka mata harara tace kekuma 'yar cin arziki banda lokacinki

Tabuga tsaki tashige part dinta ta banko kofar

Cikin tsananin tashin hankali Laila tace me yàrinyar nan take nufi da wai bata San matargidan acikin muhuduba

Hajiya rukayya cikin takai ci
Tace abinda kunnenku yabiya muku shitake nufi harda mukenan namuke nan ai mu hudu

Suby ta yashi tana haki tayi kofar husnah tashiga bugawa da karfi

Tace kifito Dan ubanki kiga yadda ake rashin kunya karamar 'yar iska yar talakawa kawai shasha

Ita kuwa husnah ko jima batayi ba saboda tana bathroom tashiga wanka

Hajiya suwaiba da tsufa yakamata sosai tace kai kai kedawo nan bakuda hankali ko

Duk abinda kuka mata za ace mu ne muka saku

Kuma kunga zasugane ba tuban Allah mukayiba

Abinda nakeso daku kibari sai randa bama nan bamuzo ba sai Ku hadu kumata shegen duka dakanta zata gudu

Kunga idan mukazo sai murufeku da fada sosai akan abinda kukayi Baku kyauta ba

Hajiya rukayya tayi murmushi tace kai hajiyata Ashe haryanzu da sauranki a tunani kuma wallahi wannan shawarar tayi dari basa Dari

Suby tace ai gaskiya idan nakama yarinyar nan saina fasa mata baki wallahi wai nice 'yar cin arziki

Nan dai sukata gulmacensu

Husnah kuwa wanna tafesa cikin wani tsadaddan material Wanda ummanta ta kawo mata Daga Sudan

Ya hadu iya haduwa gashi dinkin ya kwanta ajikinta Daga tundaga samanta a matse yake

Sai Daga kasan gwaiwarta aka sake irin dai dinkin amare idan zasu dinner

Ta gyara gashinta cikin mayuka masu kamshi da dadawa

Tasaka ribbon tadauki sarka ta metsada tasaka

Rabin kirjinta awaje suke amma cikin net Wanda akayi ado dashi har wuyanta Wanda akecewa high neck

Sai da tagama komai tay sallar magriba Dan taji anata kira

Ta dauki tiren abinsu tayi waje saida ajiye akasa tasaka ta kullo sashinta kafin tayi saman mijnta

Dining din saman tajera komai cikin wayewa da Jan hankalin mecin abincin

Kafin ta dauko remote din TV kunna ta dauko tasaka tashar sunna TV

Kafin ta fito bayan ta kullo kofar da key guri tasamu itama zauna a falon ganin ta zauna yasa duk suka dawo da kallonsu kanta

Itakuwa husnah bata San Allah yayi ruwan tsiransu ba

Tadauki wayarta tana watspp tashiga group din mutuniyarta wacce tazama mata kamar roll model dinta wato ummu afan

Wani littafi ake turowa maisuna 'YAN BIYU NE kuma husnah tana bin novel din daki daki

Tana balain son NANA DA SAMHA jarumar cikin novel dinne
Gaskiya itadai zata iyacewa novel biyune sukamata a rayuwarta Daga 'YAN BIYU NE

Sai kuma 'YAR MAKARANTA wacce ficacciyar marubuciyar nan ta rubutashi wato UMMY KHALEEL
Gaskiya mutanen biyu tana matukar alfahari da littafinsu

Tana ta karatunta na novel dinta inda Nana tama Hussain karyan rashin sallah

Sai kawai taga ankarbi wayar an rada da kasa

Husnah tabi wayar da kallo kafin ta kalli wacce ta karba wayar

Laila ce tsaye tana karkada jiki tace nafasa kozaki yi magana nane

Husnah tayi murmushi tace kodaya abinda baninasayaba

Wanda yasai wannan shizaisaje sayan wani kinga kuwa ai basai nayi magana bako

Laila tayi tsaki saiya saya mugani ai wallahi bai isa yasai miki waya a gidan nan ba saidai kizauna haka ba wayar

Husnah tace to Allah yakawo sauki

Kafin Laila tace wani abu prof yayi sallama yashigo

Idonshi direct kan babynsa suka sauka itakuwa Husnah ta shi tayi cikin tafiyanta mai kara rikitashi

Ta isa gurin prof ta fada kirjinshi
Cikin tsananin mamki Prof ya ajiye jakar hanunshi shima ya rungumeta da kyau yana ajiyar zuciya

Husnah tadago kai tace sannu da dawowa

Kasa amsawa yayi saboda mamakin Husnah

Itakuwa husnah ganin haka yasa ta sunkuya tadauki brief case Dan daya yar takama hanunshi shikuwa prof binta kawai yake harzasu haura sama husnah tace sweet baka gaidasu hajiya ba

Har ga Allah prof bema san da mutane a falonba

Laila datayi suman tsaye baki kawai tasake da ido tana kallon ikon Allah

Hakeem yayi murmushi yakalli su hajiya suwaiba da hajiya rukayya ya ce sannunku hajiya hankalina yayi gaba bangankuba Sam

Hajiya rukayya tace inazaka ganmu
ai hankalin ka baya taredakai

Nan ya gaishe su kaman karsu amsa amma dai gudun tuhuma yasa suka amsa mishi

Suby tsabar haushi ko gaishe shi batayiba bare uwar gayya datakasa magana

Kota Kansu baiyiba yajuya zai haura sama saiyaga wayar Husnah a tarwatse akasa

Yace garin yaya kuma wayarta yafashe

Caraf hajiya rukayya tayi tace ai da gangan tafasashi munata mata magana tace ai tagaji dashi tana ce Kasai mata wata zaka saya

Shine fa Laila ta mata magana akan abinda tayi fa almubazzaranci ne shine fa tahau zagin Laila

Laila zatayi magana nace tabarta yarinya ce ai

Tana gama was Hakeem wannan bayani

Yayi murmushi yace oh baby rigima aidata fada ma da nataho matadashi

amma bakomai barin ci abinci nayi wanka saimuje nasaya mata wani

Ya kalli Laila yace kekuma data zaga kiyi hakuri kamar yadda hajiya tabaki hakuri Dan yarinyace

Ya kalli suby yace ke tashi kigyara wajen data fasawayar

Yayi haura sama abinshi Dan tunda yatsaya gaisuwa husnah tashige da brief case dinsa

Yana shiga falomshi nasama yaji wani sassanyar kamshi mai ratsa zuciya

Tabbas yasan aikin husnah ce wannan Dan tunda aka zuba kujerun falon nan yana jinma ba ataba share waba duk da ba azama sosai amma ai yana bukatar gyara

Yana shiga bedroom nan ma mamaki yakasheshi ganin yadda komai tas

Ya kalli koina fes

Husnah tafito Daga bathroom din shi tanufo shi tashiga cire mishi takallmimsa da cire mishi bottle din suit dinshi

Har neck tied ita tacire mishi

Shidai Abdul mamakinta yakeyi kuma yakasa magana saida yarage saura farin naciki da wandon suit din

Ta kwashe Sauaran ta ajiyesu Indayakamata

Kafin tace kashiga wanka kafito kacin abinci

Tana fadar haka tayi hanyar kofa

Hakeem yayi wuf yakamota
Suna fuskantar juna ya kureta da ido takam takasa kallonshi

Yakai bakinshi kun nan ta yace thanks my wife

Husnah dai kanta a kasa yazaunar da ita bakin gado yace bana son kitashi kijirani harsai na fito OK

Husnah tadaga kai

Ya sumbaceta kafin yashige bathroom

Husnah tana dubawa kan side bed taga phone dinshi

Tadauka tahaye gadon tana kallon hotuna duk yawancin hotunan natane abin ya matukar bata mamaki yaushe yasamu wadan nan hutunan Dan itadai bata san lokacin daakayisuba

Ganin hotunan meenat taredashi ranar graduation dinsu

Abin yamatukar bata mamaki

Kardai AMINA ABDUL HAKEEM itace 'yar shi

Caf ai idan haka ta kasance zanji dadi duk wani masoyina dole yaji min dadin wannan Abu

Tana ta murmushi itakadai har prof yafito Daga wanka yaga tana kallon wayar tana dariya koba fada mishiba hotuna take kallo

Karasowa da ruwan jikinshi ya hauro gadon ya kwanto da ita akan kirjinshi
Yace meyabaki dariya baby

Tace bakomai

Ta budo hoton amina tace wannan fa kasantane

Yayi murmushi yace kice kinga kawarki ko

Maganar taba husnah mamaki daman yasan amina kawarta ce

Husnah tace muna dai gaisawa amma bakawata bace

Sai ta wayance tace kasanta ne
Chapter 3 · 0% Book details