← Book details Akwai Lokaci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 19

Sashe 10

Akwai Lokaci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.tace bakomai bayan wannan
Bash yace karkice haka asmau nasan ban kyauta miki ba
amma Dan Allah karkice ba komai a tsakaninmu

Cikin bacin rai husnah ta kalleshi tace dan Allah malam dakata karkasake min maganar wani alaka

A ina nasanka da harwani Abu yashiga tsakaninmu bayan malami da dalibarsa

Bashir yazube gaban prof yace wallahi ba a hayyacina nafasa aurenta bansan meyake faruwaba

A lokacin ba abinda nake gani sai amina

Hakeem ya kalli husnah yace daman shine Wanda kike bani labari amina ma itace kawarki da kike bani labari

Tunda akafara maganar kuka baizowa husnah ba sai yanzu

Ta fashe da kuka data tuno da abinda suka mata

Dagudu tabar falon

Hakeem yakai kallonshi ga amina yace ke inason kifada min gaskiyar abinda kefaruwa bana son kimin karya kinsan halina

amina tafashe da kuka ta kalli bashir tace Dan Allah uncle kayafemin

Hajiya rukayya tace ke karkice komai tashi kitafi daki

Hakeem yace ba inda zakije sai kin amsa min tambayata

Cikin kuka meenat ta kwashe komai tafadamusu

Kunyar duniya hajiya rukayya da su hajiya suwaiba da laila sunshashi agun

Bashir yadago idonshi kaman garwashin wuta ya kalli meenat yace amina kuncuceni duniya da lahira

Ninasan dama duk abinda na aikata wa asmau
Ba a hayyacina na aikata ba

Ba abinda zance saidai nace Allah ya isa tsakanina dake da kakarki

Ya kalli Hakeem yace kamin aikin gafara wallahi bazan iya zama da amina a matsayin mataba

Nasaketa saki uku kuma a hayyacina nasaketa

Bana bukatar ta a ruyuwata

Ya tashi yay ficewarsa daga gidan baki daya

Hakeem yace kunga abinda kukajawa kanku ko
Yanzu wannan wani irin abin kunya ne haka

Yayi mun dai dai wannan shine hukuncin da yadace da ita

Kuma kunga dayake Allah ba azzalumin bawansaba ne kuncuci husnah kuna Ganin kunci bulus ko

To kunga aikin Ku saigashi duk abinda kuka yi nikuwa tanadi
Dan kuwa samun mata irin husnah a yanzu sai antona

Dole bash yamiki abinda yafi haka
Banga laifinshi ba Dan asarar mace kaman husnah bakaramin asara bane

Ya tashi yayi dakin husnah ya kullo kofar yanashi baiganta a faloba

Direct yawuce zuwa bedroom dinta

Ya hangota kwance kuka sosai takeyi kaman Allah ya aikota

Ya karasa yazauna dab da ita yakamo hanunta yace baby look in to my eyes

Husnah takasa kallonshi
Yace kukan mekikeyi
Tace bana son tuna abinda suka min ne

Saboda nashafesu a tarihin rayuwata
Yace idan hakane kidaina kuka

Kokinsan nigata suka min da bashir ya aureki ina zansameki baby
Kodaya banji haushin su ba
Saima godewa Allah da kuma hajiya rukayya
Duk abinda ta aikata karshe kan 'yarta yadawo

Dan haka kidaina kuka bana son kukan ki kinjiko
Tadaga kai sama yahau bed din dakyau yajanyota jikinshi yana shafa bayanta yace kokinsan bashir yasaki amina yanzu

arazane Husnah ta tashi tace meyasa zaisaketa bayan komai yawuce

Allah yabani Wanda yafishi
Baikamata yayi hakaba wannan ai cin amanar soyayya ce

Hakeem yamaida ita kan kirjinshi yace ai dama soyayyarsu bata Allah da annabi bane
Naji dadi dayawa amina wannan sakin

Hakan shizaisa tagane abinda yake dai dai
Tadaina bin zugan kakaninta Dana uwarta

Idan amina ta nutsu tagyara halinta
Zan maida ita makaranta insaku tare kucigaba da zuwa school dinku kamar yadda kuke da

Husnah tayi murmushi ta kara rungumeshi sosai tace idan kamana haka zamuji dadi sosai Allah yasaka da alkairi

Allah yakara daukaka da arziki mai amfani yakara mana lafiya yabaka ikon ciyar damu da halak
Yakara wa su mummy da daddy Nisan kwana da lafiya

Hakeem cikin tsananin son matarshi ya kara kankameta sosai a kirjinshi yace adduoinki agareni suna sani nishadi
Dani da su mummy duk muna alfaharin samun ki cikin rayuwarmu

Husnah tace Dan Allah sweet karkace zaka matasawa meenat

Kabarta na tabbatar zatayi nadama abinda tayi

Hakeem yace kedai kice kina bin bayan kawarki ko
Husnah tayi murmushi tace tun bayan rabuwata da meenat bansake wata kawaba daman nima bamai son tarin kawaye bane

Naso meenat zuciya daya itace dai tadaukeni da guda biyu

amma koyanzu takeson mucigaba da zumuncin mu
Ina son haka saboda ina son meenat sosai

Hakeem bai barta tacigaba da maganartaba yahada bakinsu guri daya

Nan fa wasa yacanja salo

Gashi ankusa kiran magriba kuma ba itace dashiba

Tayi kakorin kwatar kanta amma takasa tashiga hanun maza sosai Hakeem yafara fita a hayyacinsa yana kokarin rabata da kayan jikinta

Husnah tayi tunanin idan tabari fa ba takyauta Dan anshiga hakkin uwargida

Cikin kuka Husnah tafara wash Allah cikina cikina

Cikin sauri Hakeem yafara tambaryata meyasameta tace cikina nane yake ciwo

Dasauri yasauka daga kan bed din Dan dauko magani husnah naganin yafita ta tashi dasauri tashiga bathroom
Tasaka key

Yadawo yaga wayam bata kan bed murmushi yayi yace zan kamaki

Kifito nayi alwala kinga zantafi masallaci Husnah tace naki wayon kaje dayan bedroom din kayi acan

Murmushi yayi yasan idan zai biye mata bazata budeba

Meenat zaune gaban uwarta da kakanta kuka sosai takeyi

Laila tace duk abin ma ai kaina yadawo niyakama ta ace ina kukan bakeba

Hajiya rukayya kuwa cewa tayi share hawayenki Dan yasaki ke
ai bashine karshen mazaba

Dan haka kiyi shiru miji sai kin ce bakya so
Keda ba mummuna ba

Meenat tace wallahi ina son shi gashi harsaki uku yayi min
Yazanyi nayi rayuwa ba bashir

Husnah kincuceni bazan taba yafe miki ba sai na dau fansar abinda kika min

Laila tace dakuwa kincika 'yar halak mekishin kanta ban amince kibarta tasha ruwaba agidan nan zanso kizama kece kishiyarta baniba uwarki zan nuna mata ina da kamarki

Hajiya suwaiba tace gaskiya ne idai kujininane ban amince kubar maganar nan ba
Tunda saboda ita aka sakeki
Itama inason saboda ke ubanki yasaketa

Nan sukaci gaba da mummanar shirunsu

Hakeem yafito daga dakin husnah yayi waje batareda ya kallesuba

Husnah kuwa sai da ta tabbatar yafita kafin tayi alwala tayi sallarta hade da adduointa
Ta dauki alkuraninta tafara karantawa har aka kira isha
Kafin ta ajiye tayi sallarta

Tana idarwa ta ninke kayan sallarta tashiga bathroom tay wanka kafinta fito tashirya cikin wasu Riga da skirt din atanfa dinkin yayi matukar zama ajikinta tafesa turararukanta
Tayi parking din gashinta
Tadaura Dan kakwalin ta das kaman wacce aka dasa akanta

Tasake gyara dakinta kafin tafito falonta

Daman kafin Hakeem yakirata tagama abincinta mai rai da lafiya
Couscous ne tadafa fari da miyar kaza

Sai zobo drink mesanyi
Wanda yasha flavour masu kamshi
Da yakan kamshin

Nan tadauki plate tadeba abincinta tasa miya

Tadauki Dan karamin glass jug tazuba zobonta aciki
Taduki karamin cup tayi waje
Main falon gidan taje center table tajawo ta ajiye kayan abincin ta akai kafin tazauna zaman ci

Bakowa afalon sai TVdake kunne

Can saiga su sunfito gabadayansu kowa tanemi kujera tazauna

Husnah tace barkanku da fitowa
Duk zuba mata tsaki

Husnah ta kallesu tace to Ashe abin nan
To Allah yasauwake

Tacigaba da cin abincinta

Can sai mai aikin laila tace anty nashirya dining din

Laila tace jeki kawasu nan muna a nan zamuci

Husnah tayi murmushi batace komaiba

********

Bayan wata hudu meenat tadade da gama iddarta da kusan watadaya kenan

Kuma a kano tayi iddarta yau take shirin komawa Kaduna gidan ubanta

Dan tadau matakin datake da niyar dauka akan husnah

Tuni driver yadukota zuwa kaduna

Laila tuni tasa angyara wa meenat dakinta
Komai yaji
Ita kawai dakin yake jira

Husnah kuwa yau ta tashi da kewan gidansu ne
Tunda tayi aure sau biyu taje
Kuma bai barta takwana ba
Yau tafita girki tana zaune kusa Hakeem tana mishi rigima ita sai yabarta taje takwana biyu agida kuma yau takeson tafiya

aikin dayakeyi a computer ma kasawa yayi
Ajiyewa yayi gefe yakamota yace baby bakya tausayina kinsan bazan jure rashinki kusadani bako

Husnah tasake shagwabewa
Tace aishiyasa nace natafi yau jibi da yamma insha Allah sai na dawo

Kaga yau dagobe bani bace da kai antyna ce

Hakeem yace kedai kimin wayo ne kawai tashi kishirya
Sainasa driver yakaiki
Jibin zanzo na daukoki yau muna da meeting ne

Inkuma zaki bar tafiyar sai gobe to saina kaiki da kaina

Husnah tayi saurin cewa a a kaje meeting dinka kawai

Yayi murmushi yace wato murna kikeyi zaki barni harna two days ko

Husnah tasa hanunta a kumatunshi tace mezaisa nayi murnar barin minjina abin alfaharina

Hakeem yashafa cikinta Yakama ta muje aduba min kefa
Ina son yara baby yaushe zaki Haifa min yara masu kyau kamarke murmushi husnah tayi tace nikuma masu kaman kai nakeso su dauko

Yace dagaske kikeyi tadaga alamar a

Yace sai kidage sosai kinsan abin kokarine

Tabashi full attention dinta Dan yamata bayanin yadda kokarin yake

Yace kina son sanin yadda zakiyi 'ya'yan my suyi kama dake tace a

Yace OK yatashi yacire singled din jikinshi itadai husnah dai kallonshi takeyi da zuciya daya bata kawo komai aranta ba

Gani tayi yacire mata Dan kwalinkanta aikuwa ta gane meyake nufi
Cikin shagwaba tace wallahi nabar maka suyi kama dakai kawai

Hakeem yace a a kibarni kawai nayi kokarina Dan insamu mai kama dani kuma kice kinyafe

ai kokarin danake nufi kenan
Kibani hadin kai sosai kigani inbazaki samu masu kama dani ba

Husnah dai talura da gaske fa yake

Tace shine abinda kake bukata yace yes my Queen

Tace OK ina zuwa barinsha sha ruwa a fridge zanbaka mamaki yace really tace yes

Bani minti daya naje nadawo

Tasamu tamishi wayo tagudu shiru shiru bata dawo ba yatashi tafita zuwa part dinta

Yaga har ta fito daga wanka ma tana drying gashinta da hand drayer

Hanu yasa a kirji yace kimin lefi kinshiga min aiki tunda kinsan ina gida aikina nane namiki komai

Husnah tadago suka hada ido tasan bakaramin aikinshi bane yasata sake wanka yanzu

Karasowa tayi cikin shagwaba ta kwantar da kanta a kirjin tace na tuba my prince Dan Allah karka bata min wanka na wallahi dokin ganin umma yasa nake sauri

Hakeem yace ban yarda ba saikin min Abu daya

Tace mezanma
Yace kekisani murmushi husnah tayi tasan idan yafara haka rigima yake nema

Tace OK kan bed tahau taga Kansu yazo dai dai tahada bakinsu guri daya
Chapter 10 · 0% Book details