← Book details Akwai Lokaci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 19

Sashe 13

Akwai Lokaci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakeem yadaga kai yakalli su meenat datake kuka kamar ranta zaifita ga jikinta yayi rudu rudu da dukar mahaifinta suby kuwa ta gudu gurin uwarta tana kuka acan

Laila kuwa tayi shiru ne tana kukan zuci

Kaman daga sama Laila taji Hakeem yace nasakike saki uku kamar yadda aka wa 'yarki

Wani gigitaccen ihu Laila ta fasa
Hajiya rukayya da hajiya suwaiba sukasa salati

Sukace yanzu sakamakon dazaka mana kenan Abdul saboda mace aiko ba aure a tsakaninku kai me rike
Laila ne

Hakeem ya watsa musu wani mugun kallo yace karna dawo nasameku a gidan nan

Yadaga waya yakira DPO na police yace yace yanason yaturo mishi yaransa zasu taho da masu laifi yanzu nan

Dayake DPO amininsane sosai batareda tambaya ba yace OK nan gidanka zasu kenan Hakeem yace a atakaice

Meenat ta rarrafo takama kafan daddynta tace daddy na tuba Dan Allah kayafemin

Wallahi daddy Sharron shaidan ne bazan sakeba daddy kayafemin

Cikin tsawa Hakeem yace sakemin kafa kafin na nakara miki mugun duka yanzun nan

Ahmad yace kayi hakuri karka hadasu da hukuma ai abinsai yai yawa

Hakeem yayi murmushin takaici yace duk abinda zanmusu bazaikai na asarar da suka sa nayiba

Hajiya rukayya sukasa baki suna ta bada hakuri akan karyakira police

Laila kuwa kuka take sosai tana bawa Hakeem hakuri

Yace nayi danasanin sanainki a rayuwata Laila
amma yaudai Allah ya kawamin karshen zamana danadake daga ke har iyayenki mata Allah ya isa tsakanina daku

Laila suna kuka suna rokonshi da yayi hakuri amma ina kokallonsu baiba

Haka sunaji suna gani aka tusa keyarsu zuwa police station

Hajiya rukayya tace Ashe baka da mutunci abdulhakeem harda mu zaka hada ka kulle baka dubi girmanku a matsayinmu na iyayenkaba

Ahmad zaiyi magana Hakeem yadaga mishi hanu

Yace a kwashesu a tafidasu

Suna ji suna gani aka kwashesu zuwa police station

Hajiya suwaiba kawai akabari itama din Ahmad yace a barta

Hajiya suwaiba ta tashi tafita driver din ta yabude mata kofar mota

Tace kawuce dani katsina daman yasaba zuwa dasu gurin bokansu shiyasa tana ce mishi katsina yagane Inda zasu

*****

Husnah sai datayi kwana biyu a hospital kafin ta war ware amma fa ita keda ciwon amma zafin Hakeem ne mejinshi

Dan a can yake kwana mummy ma tare suka zama acan sai dare yayi daddy zaizo sukoma gida

Mummy ta kalli Hakeem tace son yakamata afada wasu ummanta cewan tayi bari ko
Kaga yanzu kosunzo zasuganta da kyau bakaman shekaranjiya ba

Hakeem yace hakane nan yakira wayar ya shamsu yasanar dashi

Ya shamsu ya jajanta sosai kafin yace yanzu baya gida amma zaikoma kida yasanar da umma

Nan sukayi sallama

Mummy ta kalli Husnah dake bacci hankalinta kwance tace Allah yasaka miki abinda suka miki

Duk da ba kekadai abinyataba ba amma aikece kwance gadon asibiti

Mummy tace wai ni inasukayi ne kanon suka gudu ko suna gidan hajiya suwaiba

Hakeem yace suna police station mummy ta dafa kirji tace subhanalla police station kuma Son

ai baikamata ba sai duniya ta zageka

Kafin Hakeem yayi magana sai daddy dake shigowa yace kamin dai dai son Allah yamaka albarka
Inasane da hukuncin daka dauka akansu kuma yayi dai dai

Yanzu haka suma suna nan hospital din
Mummy hafsat tace waye balafiya daddy yace abin badadi

Hajiya suwaiba tayi hatsari a hanyar katsina tun shekaran jiya da abin yafaru

Driver din ta atake ya mutu ikuma aka rasa 'yan uwanta akayi da ita general hospital katsina to anan aketa bincike a gidajen TV dake ina zaune a office nagani shine mukaje muka dauko ta

Babu kafafuwanta ba hanu daya ga wani wari dake fita daga jikinta

Sai yanzu take fada min inda zata wai gidan boka zata takai Abdul Hakeem a tufe bakinsa kar yasake maganar yasaki Laila

Mummy tasaki salati tace idan ba a mutuba za asha kallo aduniya
Yanzu har yanzu matar nan bata rabuda dazancen boka da malamn tsubbu ba

Hakeem yasaukar da ajiyar zuciya yace Allah mungode maka daka nuna musu tun aduniya

Daddy yace wanann kadai ya ishesu ishara idan masu shiryuwane

Daddy yace ganin tanan rai hanun Allah yasa naje nayi Berlin su suzo sugana tanemi gafararsu

Kuma kutashi kuje kuyafe mata
Cikin sanyin jiki Hakeem yakalli husnah dake bacci

Mummy tace muje mudawo kafin ta tashi Allah yarufa asiri

Ahmad yashigo da shida a Aisha da kulan abinci

Mummy tace a a Aisha wato bakya jin magana ko kina fama dakanki nace kihuta da kawo abincin nan kinki ko

Aisha tayi murmushi tace bakomai mummy ai bana jin komai
Mummy tayi murmishi tace to Allah yaraba lafiya 'yar albarka

Nan Ahmad suka gaisa da su daddy

A tare suka je can dakin da aka kwantar da hajiya suwaiba

Suna shiga suka ga ba abinda takeyi sai tonawa kanta asiri tare da cisge cisgen gashi da hanun daya rage mata

Duk Wanda ke dakin kuka yakeyi na wannan abin mamaki da al'jabi

Hakeem yabisu da kallo daya bayan daya yaga tabbas sun ji jiki

Lokacin dayaga meenat zaune gefe tana kuka gashi tayi baki tayi duhu Dan duk da meenat da uwarta take kama amma fa hasken babanta ta kwaso meenat farace sosai ba sarki amma kwana biyun dasukayi a daure yasata koma kaman bata da gata take tausayin 'yarsa yakamashi yayi tur dasu hajiya rukayya dasuka bata mishi tarbiyar gudan jininshi

Zai yafe was meenat amma sai ya tabbatar tagyara halinta tazamo mutum

Bai ankaraba yaji wata kara
Dubawan dazaiyi yaga duk sun rufu akan hajiya suwaiba Wanda rai yayi halinsa
Da razanan nan ihu tacika

aikuwa suka hau koke koke

To jama a yaufa ga karshen hajiya suwaiba nan kungani
Allah yarabamu dason zuciya irin na hajiya suwaiba

Next page

Your comments is needed fans

Love you All 😘😘😘😘

📝📝📝📝📖📖📖📖
[05/05, 10:18 PM] UMMU AFAN 🌹: 🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗
🎗
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Story & written
By
The special writer

UMMU AFAN

🖊🖊🖊🖊🖊🖊📚

🌹FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION🌹

🌹🌹 (F.C.T.W.A)🌹🌹

🌹HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION🌹

🎗I DEDICATE THIS PAGE TO YOU AGAIN UMMU FARHAN ina alfahari dake wajen nice comments wallahi Allah yabar zumunci keep it up dole nasake Baki kyautar page Dan kin can canta sosai 😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘

🎗AKWAI LOKACI 🎗

🎗PAGE to 147 to150🎗

HUSNAH zaune acikin lambunsu
Kafarta cikin ruwan sweemingfull dinsu

Hakeem yana cikin ruwa yana wanka

Husnah tana watso mishi ruwa

Tana dariya yace niko barin zo kiga wallahi sai kin shigo ruwanan

aikuwa tana jin zai kamota cikin ruwa ta tashi

Tagudu shikuwa tana ganin yafito daga ruwa yabita harzuwa part dinsu

Tagama gudunta yakamata yace wanakama tace natuba Prince

Yace bazanyi hakuriba saikinzo munkoma munyi wankar tare tazaro ido cikin tsoro tace kasan fa inatsoron ruwa

Yace nasani sosanke tsoron yafita a ranki karfin yakai karshen maganarsa wayarsa ta daukara

Yaduba yaga Ahmad ne yayi sallama Ahmad yace albishirin ka

Prof yace goro Ahmad yace kayi 'dafa

Cikin farin ciki Hakeem kai haba yaushe kenan Ahmad yace gamunan mundawo gida ma

Hakeem yace naji dadi wallahi Allah yaramana shida imani

Gamunan zuwa yanzu insha Allah

Nan sukayi sallama ya kashe wayarshi

Husnah ciki murna tace anty Aisha ta haihu ko Hakeem yace a maza kishirya muje muga baby ko
Husnah tace to tare sukayi wanka yashiryata itama tashiryashi

Husnah cikin duguwar Riga maron colour da adon bakin flowers ajiki

Tayi rolling baki mayafi tayi kyau sosai yarintar ta dada fitowa yayi sosai

Hakeem yashirya cikin kananan kaya yasaka bakin wando da T shirt maron colour sun balain karbarsa sosai

Husnah tace gaskiya kayi kyau sosai bana son 'yan mata su kalle min kaifa kasan 'yam matan nan bakunyace ta ishesu ba

Hakeem yayi murmushi yace kedakinga kanki aini Bakomai bane
Shiyasa inzamu fita tare nake kokarin ganin nayi kyau sosai Dan kar mutane su dauka driver dinki

Husnah tayi murmushi dimple ta yalotsa sosai Hakeem yasa hanun yace yauwa kingani ko
Banyarda idan munje kiyi murmushi ba saboda karkowa ya kallemin wannan two beautiful point dina
Yanuna dimple dinta

Husnah tayi murmushi tace ai sai idan magana ne bazanyi tunda duk yadda bakina yamutsa sai shima ya lotsa

Hakeem yace zan nanesu kuwa idan yazama daga nisai ke saina daye

Husnah tayi murmushi tace wallahi sweet idan nabiye naka baza mutafi ba fa

Yace gaskiya kigoge jambakin nan
Saboda yamiki kyau sosai

Husnah cikin shagwaba tace haba sweet kaga fa jambakin kalan kayanane maroon kuma dankai nasaka

Yace mai wayo kawai mutafi amma kirage murmushi

Atare suka shiga part din mummy hanun su a hade da juna

Wacce suka gani zaune kan carpet din mummy

Da alamu mummy fada take mata ga akwatin kayanta nan da alama dai yanzu tazo

Meenat kenan tana ganin shigowar daddyn ta

Ta tashi taje ta tsuguna gabanshi tana kuka tace daddy Dan Allah kayafemin bazan sakeba
Natuba da zuciya daya daddy Hakeem tsaki yayi

Ya karasa gurin mummy Husnah har cikin ranta bata ji dadin abinda yafaru ba
Ga mamakinta meenat ta rike rigarta tace Dan Allah asmau kiyi hakuri kiyafemin wallahi nayi nadamar abinda yafaru bazan sake kwatan tawaba da izinin Allah

Husnah tayi saurin sa hanu takamo hanun meenat dake kuka kaman ranta zaifita tace Dan Allah meenat karkisake tsuguna min wallahi na Dade da yafe miki tun tuni daman ina rokon Allah yakawo lokacin dazaki fahimci gaskiya
Kuma gashi Allah yanufa nayafe miki duniya da lahira my besty na
Nima kiyafe min idan nabata miki rai

Meenat tayi murmushin jin dadin yafiyar data samu daga aminiyarta

Tace wallahi baki min komai ba anty na nasan kuma bazakitaba min badai dai ba saboda nasan kyakkyawar zuciyarki fari tas

Husnah tayi murmushi tace nagode da kwarai da yabonki agareni

Husnah taja hanunta sukayi falon mummy tace gaskiya husnah kina da kyakkyawar zuciya Allah yamiki albarka yasa kamiki dagidan aljanna

Hakeem yace ameen

Hakeem yafada wa mummy haihuwar Aisha mummy tace kai amma naji Allah mungode maka

Me aka samu yasanar da ita
Tayi musu addua

Tace zuwa gobe nasa driver yakaini Hakeem yace kitaso muje kawai mummy

Mummy tace a a kudaiyi tafiyarku nisai Allah yakaimu gobe

Nan sukayi sallamawa mummy husnah ta kalli meenat ta mata rada akunne meenat to Allah yadawo daku lafiya
Ta kalli daddynta tace daddy saika dawo
Chapter 13 · 0% Book details