Sashe 9
A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon Ruma ta yi ta ga ko motsawa ba ta yi ba bare ta saka ran za ta tashi, saukowa daga kan gadon ta yi ta nufi bathroom, wankanta ta tsala sa'annan ta fito.
Sai dai me? Ta yo wankan amma ba ta san ina za ta samu kayan da za ta saka ajikinta ba, tun da ba su zo da shirin kwana anan ba.
Ta na nan a tsaye ta na tunanin mafita ko dai kayanta za ta mayar? Kawai ta ji an turo kofa an shigo, ga shi iya towel ne a jikinta, saurin durƙusawa ta yi ta ƙanƙame jikinta ta na kyarmar sanyi saboda sanyin a.cn da ke ratsa ta.
Cikin hanzari su ka ƙaraso kanta a ruɗe su na faɗar "Rankiyadaɗe lafiya dai? Da fatan ba ki ji ciwo ba."
Sai a lokacin ta ɗago ta na faɗar "Bakomai qlau na ke, don Allah ku nemo mun kayan da zan saka."
Ai tun ba ta gama rufe bakinta ba, Maryam ta fice da sauri, can bayan mintuna Kamar biyar sai ga ta ta dawo riƙe da wata leda ta miƙa mata.
Wani tsadadden material ne aciki, ficewa su ka yi daga ɗakin dan su haɗo mata abincin break, kafin su dawo kuwa ta saka kayan.
Duk wannan bidirin da ake Ruma bata ma sani ba barcinta ta ke sha, dama ita haka ta ke Allah ya yi ta da mugun son barci ita ko ƙasusuwanta ma ba sa ciyo saboda kwanciya.
Bayan sun ajiye mata sun tabbatar bata buƙatar komai su ka fice daga ɗakin.
Nan fa Zuhra ta tada kai ta dubi girman ɗakin da ake kira da nata, da kuma kyau da tsaruwarsa, da yadda ake tarairayarta a gidan.
Ta kuma tuna yanda gidan iyayenta ya ke da yanda ita ce mai kula da duk wa su aikace-aikacen gidan, anan kuma ga shi ita akewa hidima.
Dogon numfashi ta ja ta sauke, a bayyane ta ce "Alhamdulillah, Allah nagode ma ka da irin wannan baiwar da ka mun, Allah ka ƙaro mun daga falalarka."
Shiru ta yi na ɗan lokaci komai ta tuna oho, sai ganin na yi ta miƙa hannu ta ɗauko wayarta.
Numbersa ta kamo ta danna masa kira, har ta tsinke bai ɗaga ba.
A ranta ta ce "kodai
Bai tashi daga barci ba ne.."
Kafin ta ƙara sa zancen zucinta ta ga kiran shi na shigowa wayarta, ɗagawa ta yi ta na faɗar "Amincin Allah ya tabbata ga angona farin cikin zuciyata."
Murmushi mai sauti ya yi kafin ya ce "Ameen tare da ke mai sona, ya ki ke ya kwana biyu? shiru ake jin ki Hajiya Mimie, kin yi kuɗi kin ɓoye."
Y'ar dariya ta yi ta ce "Lah! Ka ji Uncle ban son sharri fa, ni ce na ɓoyen?."
Shima dariyar ya yi ya canza ma su salon hirar da cewa "To ya abujan ya su Mommy da Ruma?"
"Qlau su ke Mommy na gidanta, Ruma kuma ga ta a kusa da ni barci ta ke." Ta amsa masa.
Da mamaki a fuskarsa ya ce "A'ah bangane ba ku ku na ina ne?, Ki na nufin bakwa gida?."
"Eh haka na ke nufi, mu na gidan Daddy ne ko ince Alhaji Salman daga zuwa kawo ma su Ziyara su ka riƙe mu sai Mommy ce ta koma gida, ba ka ga yanda su ke nan-nan da ni ba, ko Ni ce Real Mimie ɗin sai haka, gaskiya su na son Margayiya Mimie da yawa, anyah! Kuwa za'a samu iyayen da su ke son y'arsu sama da su a duniya kuwa?"
"Hmmm! Ikon Allah, ke kam Allah ya kashe ya baki, kin ji daɗinki." Ya faɗa sannan ya ɗora da cewa "Wai sai yaushe ne za ki dawo?"
"Saura kwana biyar, kai fa.?" Ta mayar mai da tambaya.
Ya amsa da cewa "Ai ni tuni na dawo Kano, sati ɗaya na yi a gida saboda yanayin aikina, kuma na gaya maki, ina ga daular da ki ke ciki ne ta mantar da ke." Ya ƙara sa zancen ya na dariya.
A haka su ka cigaba da firarsu a waya har zuwa lokacin da su ka yi Sallama, sai a lokacin ne kuma Ruma ta farka.
Kallonta Zuhra ta yi ta ce "Barka da tashi sarauniyar barci ta duniya, da girman kujerarki, ga break fast nan tun ɗazu ke ya ke jira."
A dai-dai lokacin ne Sagir ya faɗo ɗakin da gudunsa tare da yin tsalle ya ɗale cinyar Zuhra ya na faɗar "Good morning my lovely sister."
Murmushi ta yi ta na faɗar "Morning sweet bro." Tare da shafa sumar kansa don haka kawai ta ji yaron ya na matuƙar burge ta, ya shiga ranta nan take.
A dai-dai lokacin ne kuma Mamy ta ƙaraso ciki ta na faɗar "Wai miye haka ka ke yi Sagir? zo mu je, ka da ka takurawa Yayarka."
Jin haka ya saka ya ƙara lafewa a jikinta kamar wata mage.
Mayar da dubanta ta yi ga Zuhra ta ce "Barka da safiya daddy's girl, dafatar kin tashi lafiya, don Allah ki yi haƙuri ya zo zai takura ki koh? Wallahi tun da asubar fari ya farka ya saka rigima, shi sai a kai sa gurin Sisternsa, daƙyar Sady ta lallaɓa sa ya koma barci."
Murmushi ta yi ta ce "Ayyah! Mamy, ai bakomai shi ai ƙanina ne."
Ba su an kara ba kawai su ka ji motsi daga ƙofa, Mamy ta juya don ganin ko waye yayin da Zuhra ta ƙura masa ido domin itama bata ankara da zuwansa ba sai yanzu, amma da alama ya jima tsaye agun.
®®®®®®®®®®®
Ita kuwa Mommy tsaye ta ke a gaban gas ta na Shirya break fast, Amma kallo ɗaya za ka mata ka fahimci hankalinta baya kan girkin, ta yi nisa a tunani.
Mafita kawai ta ke nema ta yanda za ta yi ta zaunar da Zuhra anan domin tsakani da Allah ba ta so wannan daular ta fita daga hannunta, "to ko zan riƙe ta anan ne idan ya so sai ta ci gaba da karatunta anan?"
"Shawara mai kyau" wata zuciyar ta faɗa mata nan da nan ta kashe gas ɗin ta kwashe dankalinta da ta gama soyawa, wanda ke cikin man kuwa anan ta bar shi ta yi waje don kiran yayarta a waya.
A falo ta dire kayan tare da ɗaukar wayarta ta dannawa Mama kira.
Mama na ɗagawa su ka gaisa sosai cike da fara'a sannan ta fara inda-inda ta na son ta roƙe ta su bar mata Zuhra, amma ta na jin tsoron ka da su ƙi amincewa.
Can dai ta dake ta yi ta maza ta ce "Am, Yaya dama ina so na roƙi wata alfarma Allah ya sa zan samu."
"Insha'allah, indai zan iya kuma bai fi ƙarfina ba zan miki."
Murmushi ta yi ta ce "Yaya dama ina so na roƙi Alfarmar ku bar mun Zuhra a hannuna, na yi ma ku alƙawarin zan kula da ita sosai tamkar yan da za ku mata."
"Khadija me ki ke nufi da mu bar ma ki Zuhra? Kin san dai ta na karatu anan koh? Kuma bata riga ta kammala ba, ta ya ki ke ganin za mu bari ta rasa karatun da daƙyar da taimakon Allah mu ke ɗaukar nauyinsa?"
"Uhmm! Indan wannan ne ba damuwa yaya ni zan saka ta makaranta mai kyau anan, ina mai tabbatar mi ki za ta samu ingantaccen ilimin da za ta taimaki Rayuwarku gaba ɗaya anan."
"To na ji ba ma wannan ba Khadija, kin san yarinyar nan fa ta na da miji, ta na gama sakandare aure za mu mata, kafin wannan ma ita kaɗai ce ta rage mun y'a mace a gabana ita ke taimaka mun gun ayyukan gida da sauran su, idan ki ka ɗauke ta ya zan yi?"
"Ka da ki damu yaya Ni zan iya ɗaukar maki y'ar aikin da za ta taya ki aiki a gida, ni dai buƙatata kawai ki bar mun Zuhra don Allah, don Allah yayata, ni da ke fa duka abu ɗaya ne."
Jikin Mama ya yi sanyi sosai, haka kawai ta ji ta kasa amincewa da Khadijah tabbas da kwai lauje acikin naɗi tun da har Khadija ta dage haka, amma sai ta ce "Shikenan ki kira Babanta a waya ki sanar mai, duk yan da ku ka yi da shi ki sanar min." Ta na gama faɗa ta kashe wayar ba tare da ta tsaya saurarar godiyar da ƙanwar tata ke mata ba.
Murmushin cin nasara Mommy ta yi ta ce "Habah! Ko ke fa khadijatu? Amma ta ya yarinya za ta samu arziƙi ta dalilinki ki bar ta ta tafi ta kai wani gurin dabam, ina ai ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa."
Wani murmushin ta kuma yi wanda ita kaɗai ta san fassarar kayanta sa'annan ta zauna ta fara cin abinci ta ta na ƙissima irin abubuwan da........
Ga mai buƙata sai ya tuntubeni ta whatsapp numberna 👇🏼 _08109634202_
Domin na masa bayanin yanda zai biya.
Follow me on Wattpad @ummu inteesar.
Vote, share & Comment.
UMMU INTEESAR CE💚💙💛❤️💚
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal.
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin.
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL.
MASOYA NA A DUK INDA KU KE INA MATUKAR K'AUNAR KU,ALLAH YA BAR ZUMUNCI.
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Free Page 2️⃣3️⃣↪️2️⃣4️⃣
Ta fara cin abincinta ta na ƙissima irin abubuwan da za ta yi da zarar burinta ya cika na riƙon Zuhra.
Bayan ta kammala ne, ta kira Baban Zuhra a waya ta sanar mai da buƙatarta.
Kai tsaye ya nuna mata rashin amincewarsa ba wani nuƙu-nuƙu.