← Book details A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 36

Sashe 10

A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai ta ji haushin hakan a ranta ta ke cewa "Ku ji mun wannan mutum na saka shi a inuwa ya na ƙoƙarin tura ni rana, tun da ya ga alkhairi ya doso ni ta dalilin y'arsa shi ne zai mun baƙin ciki, to wallahi ba ka isa ba Habu, in ka san wata ai ba ka san wata ba." Dogon tsaki ta ja ka na ta bar gun cike da ɓacin rai.

®®®®®®®®®®®

"A'ah! Sam me ka ke yi tsaye agun? Ƙaraso ciki mana."

Ƙarasowa ya yi da fara'a sosai a fuskarsa ya na faɗar "Good Morning Mamyna."

"Morning dear Sam, dafatar ka tashi lafiya."

"Alhamdulillah, qlau na ta shi Mamyna." Ya faɗa tare da mayar da dubansa ga Zuhra fuskarsa cike da murmushi mai ƙayatarwa ya ce "Barka da Safiya Sweet sis."

Murya a kasalance ta karɓa masa da "Barka dai." Saboda yanayin yanda ta ga ya ƙura mata ido ba ya ko kyaftawa.

Daga jiya zuwa yau ta lura cewa ya fi kowa tsinannan kallo duk a gidannan.

Kafin ta gama zancen zucinta ta tsinto muryarsa ya na faɗar "Sweet sis me ku ke jira ne har yanzu ba ku yi break ba."

"Uhmm! Za mu yi yanzun." Ta amsa masa.

A lokacin ne kuma Ruma ta gyara zamanta ta na faɗar "Ina kwana yaya Sameer, na ga kamar ka manta da ni saboda ganin sisternka?" Ta faɗa ta na dariya kaɗan-kaɗan.

Firgigit ya yi tamkar wanda ya farka daga dogon barci kallon ta ya yi ya ce "Yi haƙuri y'ar uwarmu, ba wai na manta ki ba ne dama... Dama....ina so ne na..." Ya na maganar idonsa na kan Zuhra duk sai ya daburce ya rasa ma me zai ce.

Dariya sosai Ruma ke yi yayin da Mamy ta yi murmushi ta ja hannun Sagir ta ke kan cinyar Zuhra za su fice daga ɗakin domin ta fara ɗago jirgin ɗan nata, har ta kai ƙofa ta juyo ta na faɗar "Mimiena don Allah ku sauko ku ci abincin ka da ya yi sanyi, don Allah ka da ku bari na dawo na samu ba ku ci ba, shiyasa na saka aka kawo maku har nan domin ku fi sakewa." Ta na gama faɗa ta juya ta fice still ta na riƙe da hannun Sagir da ke ƙoƙarin ƙwace hannunsa daga riƙon da ta masa.

Mamy na ficewa shima ya bi bayanta a daburce ganin an fara yi masa dariya, ba ya so ayi saurin kwaɓo jirginsa shiyasa ya fice, saboda ya tabbatar muddin ya na ganin Mimie a gabansa ba a bunda ba zai iya aikatawa ba, saboda ƙaunarta da ta masa dirar mikiya a zuciya.

@@@@@@@@@@

Bayan kwana biyu da zuwan Zuhra gidan Alhaji Salman, ta saki jiki sosai domin ta sakankace cewa su ma su ƙaunarta ne, ko da iyayenta ne sai haka su na ririta ta sosai, haka y'an samarin gidanta su na matuƙar son ta ita kuwa ta na girmama su sosai.

Fatarta ta murje ta yi kyau sosai acikin kwana biyun nan saboda canjin cima da kuma hutu da ya zauna mata, ko Ruma da ta ke y'ar rakiya ta ƙara kyau sosai har bata so su bar gidan.

®®®®®®®®®®®

Shi kuwa Sameer wata irin ƙauna mai zafi ce ta shiga zuciyarsa, sosai wutar soyayyarta ke ruruwa a zuciyarsa.

A ranar ne kuma Mommy ta kira Mamy a waya ta ke tambayarta "Yaushe ne su Zuhra za su dawo?" "A yau ne ya kamata su dawo domin kwana biyu ki ka ce."

Anan Mamy ta kuma roƙarta da ta ƙara ma su kwana biyu don Allah.

"Hmmm! Hajiya ba na so na ce miki a'a, amma ya kamata su dawo haka kin ga yarinyar nan saura kwana biyu ta koma gida akwai shirye-shiryen tafiya a gabanta." Mommy ta faɗa.

"Hajiya ka da mu yi haka da ke don Allah ki ƙara haƙuri, ba ki ga yanda iyalan gidan nan ke cikin farin ciki ba saboda dawowar Mimie cikin rayuwarmu, da son samun mu ne ma a bar mana ita anan gaba ɗaya amma na san da wuya iyayenta su amince, amma ki ƙara haƙuri don Allah, insha'allah nan da kwana biyu za su dawo."

"Uhmm! Shikenan Allah ya kai mu amma gaskiya dan ke ce kawai shiyasa zan bar su su kuma kwana."

"Shikenan Nagode sosai Hajiya, ki turomin da account number na ki yanzu." Ta na gama faɗa ta yanke kiran.

Mommy kuwa murna duk ta gama cikata, har hannunta na ɓari gun tura account number ɗin, don ta tabbatar kuɗi ne za'a turo mata.

Can kamar bayan mintuna biyar da turawar sai ga alert ya shigo wayarta daga account ɗin Mamy.

Naira dubu hamsin ne, sai da ta yi y'ar ƙara kaɗan don murna a bayyane ta ce "Hmmm! Lallai ma Habu, wato wannan arziƙin ne ka ke mun baƙin cikin samu?, Kar ka ji komai ni na san me zan yi a kai." Ta ƙarashe zancen, leɓenta ɗauke da wani busasshen murmushi wanda ita kaɗai ta san fassararsa, ƙwafa ta yi tare da jan dogon tsaki, ta nemi guri ta zauna ta na ayyano abubuwan da ya kamata ta yi, domin ta shiga cikin dukiyar Alhaji Salman ta wataya.

®®®®®®®®®®®

A can Kano kuwa mama ce ta ji shirun ya yi yawa, Mommy ba ta kuma kiran ta akan maganarsu ba, hakan ya sa ta ɗaga waya ta kira ta.

Har ta tsinke ba ta ɗaga ba, ta kira ta ya kai sau uku amma ba ta ɗaga ba, mamaki ne ya cika ta me wannan matar ke nufi da ƙin ɗaga wayarta? Ko dai ta na fushi ne?, To me aka yi na fushi?.

Mama ta shiga jerowa kanta tambayoyin da ba mai amsa mata su, hakan ya sa ta haƙura ta ajiye wayar tare da komawa kan aikin sana'arta ta ɗan wake da ta ke.

®®®®®®®®®®®

Ita kuwa Mommy ta na sane ta ƙi ɗaga wayar domin dukkansu haushi su ke ba ta har yayar Tata tun da sun hana mata riƙon y'arsu.

A ranta ta ce "Jibi-jibin nan zan tattaro ma ku y'arku na maida ma ku, Nagode Allah da ya sa nima ina da tawa y'ar, da ba ni da ita ne abun zai fi yi mun ciwo, dama shi talaka tsiyarsa kenan ka saka shi a inuwa ya yi ƙoƙarin turaka rana."

Ƙwafa ta yi sannan ta ce "Za ku sha mamakina, domin wannan karon ko kwanɗalata ba za ta yi ciwo ba gurin hidimarku da ta y'arku, za ku san kun yi da khadijatu." Ta ƙarashe zancen ta na huci.

A ranar ne kuma Sunil da Suhail su ka dawo daga tafiyar da su ka yi.

Mommy na ƙoƙarin yi ma su sannu da zuwa, su kuwa ko wannensu ƙoƙarinsa ya ga Zuhra sai raba ido su ke.

A tare su ka haɗa ba ki gurin faɗar "Mommy wai ina Zuhran? Ko har ta koma ne?.

Harara ta zuba ma su ta na faɗa "Bansaniba, wannan wane irin iskanci ne ina ma ku sannu da zuwa amma ku na tambayar wata can dabam."

A tsorace su ke kallon mahaifiyar tasu, fuskarsu ta bayyanar da mamaki ƙarara, to yaushe Mommynsu ta sauya haka? Ita ce fa ta koya ma su ɗokin y'an uwansu tun su na yara, amma yanzu don sun nuna kuma sai ta yi fushi?, Tabbas da wani abu a ƙasa, ruwa baya tsami banza.

Daga haka su ka ba ta haƙuri su ka wuce ɗakinsu don watsa ruwa..

A dai-dai lokacin ne kuma kiran Zuhra ya shigo wayarta.

Kallon wayar ta yi tare da zubawa screen ɗin harara kamar dai Zuhran ta ke gani a ciki, har ta tsinke bata ɗaga ba, domin zancen gaskiya ita yanzu har Zuhran haushi ta ke bata matuƙa, ta matsu su dawo ta tattara ta ta mayar gidan faƙiran iyayenta kowa ya huta.

®®®®®®®®®®®

Washe garin ranar Sameer ne ya farka daga barci a razane duk ya ruɗe sai maimaita faɗar "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Ya ke, kallo ɗaya za ka masa ka gano cewa a gigice ya ke, da alama ya yi wani mummunan mafarki ne, gaba ki ɗaya ya gama jiƙewa da gumi duk da a.c da ya ke ƙure a ɗakin nasa.

Cikin hanzari ya sauka daga kan gadon ya nufi banɗaki don watsa ruwa.

A ransa ya ke cewa "Ya zama wajibi a gare ni, na sanar da Mimie yawan ƙaunar da na ke mata kafin ta tafi gobe, domin gujewa faruwar abinda na gani a wannan mummunan mafarki."

Ko me Sameer ya gani a mafarki?

Me zai faru tsakanin Mommy da y'ar uwarta bayan komawar Zuhra garinsu?

Hmmmm! Sai ku tare ne a page na gaba don cin amsar Waɗannan tambayoyin.

Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼

_08109634202_

Domin na maku bayanin yanda za ku biya.

Follow me on Wattpad @ummu inteesar.

Vote, share & Comment.

UMMU INTEESAR CE❤️💛💚💙💛💚💛
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*A SANADIN KAMA*

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*

*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*

Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal.

Ga mai buƙata sai ya tura kuɗin ta wannan account ɗin.

Account name: Rukayya Ibrahim lawal
Account no:0431343346
Gt bank.

KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE ZA KA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL.

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

Free Page 2️⃣5️⃣↪️2️⃣6️⃣

A daren ranar Mamy ce Zaune a gefen gado, yayin da Daddy ke kwance akan gado da shirin barci da alama ya fara jin barci.

Mamy ce ta ce :Alhaji gobe ne fa yarinyar nan za ta koma gidan Mommynta Saboda jibi za ta koma gida, ya kamata ka yi wani abun, gidan nan kowa na cikin damuwa saboda tafiyar da za ta yi." Da damuwa a fuskarta ta ke zancen.
Chapter 10 · 0% Book details