Sashe 34
A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe garin ranar da suka samu labarin, da yamma suka je asibiti don dubiya a can suka tarar da Abban Ruma, anan ne kuma asirin Mommy ya tonu, domin Abban Ruma ya tambayi dalilin fitar da ta yi ba tare da saninsa ba har hakan ta faru.
A nan Hajiya hafsat ta fallasa asirin duk wata badaƙala da ƙulle-ƙullen da suka yi tare, ta kuma roƙi gafarar Alhaji Salman da iyalansa.
Abban Ruma ya ji zafi da raɗaɗin wannan abu matuƙa, take a gurin ya sake ta saki ɗaya, domin a cewarsa ba zai zauna da mushrika ba.
Ya na sakinta ya juya abinsa, a ranar ma ya bar garin.
Ƴaƴanta sun yi kuka har sun gode Allah.
Mimie ta kira Mamanta ta na kuka, ta shaida mata halin da ƙanwarta ke ciki.
Mama ta tausayawa ƙanwar tata matuƙa, don haka ta shaidawa Mimie zuwa jibi za su zo Abujan ita da Baba insha'allah, daga nan ma sai su ga ɗakinta.
Bayan kwana biyu Mama da Baba suka zo Abuja, har lokacin Mommy na asibiti domin ta samu gocewar ƙashi a wasu gaɓɓanta.
A wannan zuwa nasu ne komai ya dai-daita, a nan asibitin Mommy ta nemi yafiyarsu, cikin Sa'a kuwa dukkan su suka yafe mata, komai ya wuce kamar bai faru ba.
Mama ta shirya da 'yar uwarta suka dawo kamar da.
Bayan kwana biyu suka koma Kano.
Mommy kuwa ta cigaba da jinyarta yayin da Ruma ke kula da ita.
A cikin zaman jinyan da take ne wata rana Saheen ya zo har asibitin ya duba jikin Mommy, ya kuma ce ya mayar da aurensa da Ruma.
Nan Mommy ta nemi ya fiyarsa ya kuma yafe mata.
Bayan wani dogon lokaci aka sallame ta daga asibitin ta koma gida.
Tun daga lokacin Mommy ta tuba, ta koma ga Allah ta na rokon gafararsa na shirkar da ta aikata a baya.
@©©©©
Mimie kuwa ta ci gaba da karatunta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa yanzu ba ta da sauran wata damuwa, duk matsalolinta sun kau, tsakaninta da mijinta kuwa sai son Barka.
Bayan shekara ɗaya Sameer ya samu aiki a ƙasar Dubai, don haka ya fara shirye-shiryen tafiya, amma ita Mimie a nan Abuja zai bar ta har ta kammala karatunta, wanda ya rage saura Shekara ɗaya.
Twins kuma yanzu shekarunsu biyu, sun yi wayo abinsu har su na magana da gudu a ko'ina.
A ranar wata Laraba Sameer ya yi Sallama da iyayensa da 'yan uwansa domin a ranar ne jirginsu zai cira zuwa Dubai.
Bayan tafiyarsa Mimie ta sha kuka, domin ganin take kamar ba zai dawo ba, tunawa ta yi da lokacin da suka rabu da Bassam lafiya ƙalau, cikin ƙaunar juna sai gashi an dawo mata da shi cikin wani mawuyacin hali kuma ya mutu a gaban idonta, wannan abun ya tsaya mata a rai sosai, duk lokacin da ta tuna shi, sai ta zubar da ƙwalla tare da masa addu'ar samun gafara.
To yau ɗin ma haka ne a bayyane ta ce "Allah ya jikan ka, Uncle, Allah ya maka rahama uban ƴaƴana, ka tafi ka bar ni da marayun ƴaƴanka, a yau wanda ke kulawa da su ma ya tafi, banda tabbacin sake haɗuwa da shi.." ta faɗa ta na rushewa da wani sabon kukan......
Follow me on wattpad @ummu inteesar
RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
DA KUMA
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 7️⃣7️⃣↪️7️⃣8️⃣
🔚🔚🔚🔚🔚🔚
Bayan tafiyar Sameer da kamar sati uku Mimie ta fara laulayi, ashe ko da Sameer ya tafi ta na da ciki wata ɗaya, sai dai duk a cikinsu ba wanda ya lura, sai yanzu ne ta lura da hakan, amma sai ta yi gum da bakinta bata faɗawa kowa ba, har shi Sameer ɗin gudun kada ɗoki ya sa ya kasa gudanar da aikinsa cikin nutsuwa.
©©©©©©
A Dubai kuwa Sameer ya na gudanar da aikinsa cikin ƙwarewa da jajircewa, ya bada himma sosai ga aikinsa, domin yanzu zaman Dubai ya na masa daɗi ba kamar da ba.
A yanzu ba yada damuwar komai, kullum ya kan yi waya da ahalinsa da kuma matarsa.
©©©©©©
A bangaren Mimie kuwa ta ci gaba da renon cikinta da kuma tagwayenta ba tare da ta nuna gazawa ba.
Mamy ce ta lura da yanda yanayin Mimien ya canza, abinka da manyan mata nan da nan ta fahimci cewa Mimie tana da ciki.
A nan fa Mamy ke cewa "y'ata ko dai mun samu ƙaruwa ne?"
Da murmushi a fuskarta ta ɗan dubi Mamy ta ce "Ta me fa Mamyna?"
Ba wai don Mimie bata gane ba ne ta yi wa Mamy wannan tambayar, a'a sai dai don ta na tsananin jin kunyarta ne.
'Yar dariya Mamy ta yi ta ce "Yata kenan, ina nufin ko kina da ciki ne?"
Ba ta amsa tambayar Mamyn ba sai ma sunkuyar da kanta ƙasa da ta yi, a nan Mamy ta fahimci hasashen ta ya zama gaskiya.
Cikin matuƙar jin daɗi ta ce "Masha'allah! Allah ya nuna mana lokacin fitowar wannan Babyn lafiya, wannan daddaɗan labari ne, kin gayawa Sam kuwa?."
Gyaɗa kai ta yi alamar a'a.
Mamy ta ce "No wonder, shiyasa ban ga ya fara zumuɗi ba, ai ko ya kamata ya sani."
Sai lokacin Mimie ta ce "Mamy na san halin Yaya Sameer ne, yanzun ana gaya masa, zumuɗi zai hana shi gudanar da aikinsa cikin nutsuwa shiyasa na yi shiru."
Daga haka suka ajiye wannan maganar suka zaro wata chapter.
A taƙaice dai Sameer bai samu labarin cikin Mimie ba sai da cikin ya kai wata biyar, a nan ma ba faɗa masa ta yi ba, shine ya lura da hakan lokacin da suke vidio call.
Shine ya ke tambayar "Sweetyna yaya kodai mun samu ƙaruwa ne?"
Bata ce komai ba sai murmushi da ta yi, a nan ya tabbatar da zarginsa, ai kuwa ya hau murna, farincikinsa ya kasa ɓuya.
Tun daga ranar baya da aiki sai jibgowa Babynsa kaya, komai ya gani mai kyau na jarirai sai ya siyi wanda zai yi dai-dai da sawar maza ko mata ya ajiye, daga wannan ranar ne kuma ya fara irgen watannin da suka rage na haihuwa sai zumuɗi ya ke.
Lokacin da cikin Mimie ya shiga wata na tara, Sameer kasa haƙuri ya yi har sai ta haihu sannan ya koma Nigeria, don haka ya harhaɗa kayansa ya dawo Nigeria zaman jiran Babynsa.
A ranar da cikinta ya cika wata tara da sati biyu, ta haifi 'yarta ƙatuwa masha'allah.
Sameer ya yi matuƙar farinciki da haihuwar nan, da yake a asibiti ne ta haihu, su Mommy da Ruma sai Mamy sune tare da ita a ɗakin bayan an gama shirya su ita da jaririyarta.
Sameer ne ya shigo ɗakin fuskarsa cike da annuri, ba ya da burin da ya wuce ya ga fuskar 'yarsa.
Cikin hanzari ya isa gun Mamy dake riƙe da 'yar a hannunta, ya miƙa mata hannu, ba ko kunya ya ce "Mamyna miƙo mun 'yata naji ɗuminta."
Harararsa Mamy ta yi, ta nuna masa Mommy dake zaune a gun da ido, alamar ya gaida ta.
Amma inah! Shi yanzu ba Gaisuwar ba ce a gabansa, 'yarsa yake muradin ji a tafin hannunsa, don haka ya yi mirsisi.
Ita ko Mamy ganin ya yi kunnen uwar shegu da nuninta sannan yaƙi janye hannunsa, ya sa ta haƙura ta miƙa masa 'yar tana mai jin kunya, "yayan zamani basu da kitsen ido." Ta faɗa a ranta.
Cikin azama ya karɓi 'yar ya rungume ta tsam a ƙirjinsa, sai ko ga hawaye shaaa!
Faɗar ya ke "Alhamdulillah! Allah abin godiya, ashe ina da rabon ganin wannan 'yar"
Matsawa kusa da Mimie da ta fito daga toilet ɗin ɗakin ya yi ya na faɗar "Sweety ashe da rabo a tsakaninmu? Ashe rabon wannan 'yar ne ya saka na nacewa soyayyarki? Shi kenan yanzu mun kuma zama jini da tsoka, dama can kina a cikin ahalinmu."
Da alama ya ma manta da mutane a ɗakin.
Ganin haka ya saka Mamy da Mommy suka bar masu dakin, Mamy na sharar ƙwallar tausayi, saboda tunawa da ta yi da rayuwar da ɗan nata ya shiga a baya.
Tun a asibitin Sameer ya yiwa 'yarsa huɗuba da sunan *Rukayya* wato sunan ƙanwarsa Margayiya Real Mimie ta ci, za su dinga kiranta da Little Mimie.
Bayan Mimie ta huta sosai aka sallame ta daga asibitin suka koma gida.
Tun ranar da ta haihu Mommy ta tare a gidan, domin acewarta ita ce za ta kula da 'yarta da kanta kafin ƙarasowar mutan Kano, da yake har lokacin Abbansu Ruma bai sauko ba bare ya mayar da aurensa.
Ana saura kwana uku suna 'yan Kano suka zo.
Ranar suna aka yi shagali sosai, Naira ta yi kuka domin kam an kasheta a sunan 'yar gata, a gurin zanen sunan ma maroƙa sun yagi rabonsu.
A wannan ranar gaba ɗaya iyalan gidan alhaji Salman su na cike da tsantsan farin ciki, kuma sun yiwa Allah godiya da ya dawo masu da walwalarsu a lokacin da basu yi tsammani ba.
Da farko ya aiko masu Zuhra a matsayin wacce za ta zama jagoran dawo masu da sumammen farincikinsu, yanzu kuma ya azurta su da samun 'yar da take kama sak da Mimiensu daga tsatsonta, 'yar kuma da ba su da a familynsu, ba abinda za su ce sai dai su ƙara godewa mahaliccin bayi mai jinƙai da Rahama ga bayinsa.
Bayan watse taron suna da kamar sati biyu, Daddy ya yi-ya yi Sameer ya koma bakin aikinsa amma ya ƙi, ya kafe shi lallai ba inda zai je sai tare da matarsa.
Mamy kuwa ta yi tsayin daka akan cewa ba inda zai je da Mimie har sai ta yi kwana tamanin da haihuwa don haka ya je kawai.