Sashe 33
A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan dawowar Saheen ne ya shaida masu abinda ya faru, ya sha faɗa agun Daddy da Mamy sosai, suka ce gobe ya je ya dawo da matarsa, ai ba ita ta masa laifin ba, sai dai ya basu haƙuri da cewa su yi haƙuri ba zai iya dawo da ita yanzun ba, sai Mommy ta gane kuskurenta, akan dole suka ƙyale shi domin 'mai ɗaki shi ya san inda ɗakinsa ke yoyo.'
Mimie ta yi mamaki matuƙa na jin halin shirkar da ƙanwar Mamanta ta faɗa don kawai hassada.
Ta na tausayawa makomar Mommyn tasu.
@@@©©©©
Bayan wata huɗu Sameer da Mimie su na cikin farinciki da kwanciyar hankali, aurensu abin burgewa ne da kwatance ga kowa.
A lokacin ne Sameer ya yi mata zance komawa Bk domin su nemi a mata transfer zuwa Abuja ta ci gaba da karatunta a nan, tunda dama saura shekara biyu.
Daga nan kuma sai akai twins dangin babansu su gan su.
Ta yi murna sosai da wannan tunanin na mijinta, don haka ta fara shirin tafiya ba ƙaƙƙautawa....
Follow me on wattpad@ Ummu inteesar
UMMU INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹🌹
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*RASHIN GATA*
DA KUMA
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 7️⃣5️⃣↪️7️⃣6️⃣
A ranar wata Alhamis suka je Bk ita da Sameer da kuma twins, direban Daddy ne ya kai su.
Gidan Innarmu suka sauka, domin Mimie bata da wanda ya wuce Innarmu a Bk, su kaɗai tasani.
Innarmu ta yi murna da ganin jikokin nata yanda suka yi kyau abinsu.
A can Mimie ta riski labarai kala-kala masu daɗi da akasin haka.
Ko da ta je ta tarar an aurar da Shamsiyya ga wani magidanci mai shekaru arba'in, wata biyar kenan da auren, itama Sakina ana gaf da aurenta.
Washe garin Ranar da suka sauka, suka je Jami'a domin yin abinda ya kawo su, kuma sun samu abinda suke neman, don haka suka juyo zuwa gidan Innarmu lokacin yamma ta riga ta yi.
Suna dawowa hutawa kawai ta yi ta ci abinci, Sakina ta raka ta gidan Shamsiyya don ta ganta.
Sosai Shamsiyya ta yi murnar ganin Mimie da ƴaƴan yayanta.
Mimie kuwa har da ƙwallarta don ganin irin taskun da Shamsiyya ke ciki.
Babban gida ne irin na family ɗinnan, mijinta ya na da mata biyu ita ce ta, gashi da ƙanne 'yan mata da kuma yaya matasa, sosai ƙannen mijin da kishiyoyi suke takura mata, cin mutunci har irin wanda bata san da shi a duniya ba yi mata suke, ga aiki da ake jibga mata kamar jaka.
Ganin wannan halin da Shamsiyya ke ciki ya tunawa Mimie rayuwar aurenta da ta yi a baya, da yanda Shamsiyyar ta takura ta, tabbas Allah ba azzalumin sarki ba ne, domin ga shi ya saka mata ta wannan hanyar duk da ta riga ta yafe har cikin zuciyarta.
Kallon Shamsiyya ta yi ta ce "ke kuwa Shamsiyya a haka kike jure zama da waɗannan mutanen?"
Nan fa Shamsiyya ta fashe da kuka ta na faɗar "Ki yahe min Anty Mimie, na san sakamakon abinda na shuka ne na ke girba, a baya na wulaƙanta ki yau gani ƙannen miji suna walaƙanta ni na kasa yin komi, wannan ishara ce ga masu hali irin nawa, don Allah ki yahe min."
Zancenta ya sanyayyarwa da Mimie jiki, duk sai ta bata tausayi don haka ta ce "Da ma ni tuni na yafe muku, Allah ya yaye miki damuwarki."
Ba su suka baro gidan Shamsiyya ba sai bayan magriba.
A hanyarsu ta dawowa ne Mimie ke tambayar Sakina labarin Zinnira.
Sai da ta ja dogon numfashi ta sauke, sannan ta shiga bata labarin yanda rayuwa ta dawowa Zinnira da halin da take ciki na rashin lafiya ita da mahaifiyarta.
Ta tausaya masu matuƙa don haka ta dubi Sakinan ta ce "Gobe ki shirya da wuri kafin mu wuce sai ki raka mu, mu dubo su."
Da to ta amsa haka suka cigaba da hirarsu, Sakina ta na goye da Affan a bayanta har suka isa gida.
Washe gari tun ƙarfe takwas suka shirya tare da shiga motarsu driver ya ja, Sakina na nuna masa hanya har suka isa gidansu Zinnira.
Da sallamarsu suka shiga gidan, tun a ƙofar shiga ɗakin Mimie ta toshe hancinta, saboda wani ɗoyin bala'i da ya daki hancinta.
Su na shiga suka same su akwance ita da mahaifiyarta, kallo ɗaya zaka musu ka fahimci su na cikin wani hali na azabar ciwo da raɗaɗi, jikinsu duk wasu marurai ne sun ja ruwa sun cika fam, wasu ma sun farfashe har da tsutsotsi ke zazzaga ta wani ɓangaren.
Ɗakinsu kuwa ba komai sai ledar ƙasa da alama komai nasu ya ƙare garin neman magani.
"Sannu Mama ya jiki?" Suka faɗa a tare
Kai kawai ta ɗaga masu.
"Sannu Zinnira." Mimie ta faɗa cikin tausayawa hawaye na gangaro mata.
Daƙyar Sameer ya iya buɗar baki ya gaida su, sai alla-alla yake a tashi a tafi, domin cikinsa ya fara hautsinawa saboda a zaɓar ɗoyin ruwan maruran.
Daƙyar Zinnira ta yunƙura zaune, tare da sakin wata ƙarar azaba saboda fashewar wani maruru a lokacin da take zama.
Kallon Mimie ta yi idonta na zubar da hawaye ta ce "Don Allah ki yahe muna Anty Mimie, na san wannan ciwon shine ajalin mu nida innata, domin muna girbar sakamakon abinda muka shuka ne."
Shiru ta ɗan yi na wani lokaci kafin ta cigaba "Mu at silar lalacewar farincikin rayuwar aurenki a gidan Bassam, duk abinda su Innarmu ka miki bayin kansu na ba, aikin sihiri na, wanda mu munka ƙulla shi don a hidda ke daga gidan ni in shiga, shi ma Bassam mu munka tahi wurin boka munka sa ya raba soyayyarku, sannan mun saci kuɗɗinai, waɗanda duk rabinsu naki na, amma a yau babu ko sisi duk sun ƙare wurin neman magani."
Ta na gama faɗa ta fashe ta kukan nadama, tana ƙara neman yafiya a gun Mimie.
Mimie ta tausaya masu matuƙa cikin kuka take faɗar "Na yafe maku duk abinda kuka mun na yafe, sai dai wannan ya zama ishara gareku, domin Allah ba ya yafe haƙƙin wani, kuma ya na karɓar addu'ar wanda aka zalunta, yau wa gari ya waya? Ni na yi aure na samu wani mijin wanda ya fi Bassam kamar yanda kika gani ke kuma fa?." Ta ƙarashe zancen ta na kallon Zinnira.
"Na yi hasara, na cuci kaina." Zinnira ta faɗa cikin kuka.
Kuɗi ta ciro a jaka bandir ɗin ɗari biyar, ta ajiye a gaban Zinnira ta ce "Ga wannan ku siyi magani."
Daga haka suka miƙe suka fice, dama tuni Sameer ya bar gidan ya koma mota, saboda ba zai iya jure wannan azabar ba.
A mota Mimie ta sha kukanta, dama can kuka baya mata wuya.
"Allah sarki rayuwa! Allah kenan, sarki buwayi gagara misali ikonsa ya na kan komai, wai yau ni ce maƙiyana a baya suke kuka su na roƙon gafarata?, gaskiyar 'yan magana da suka ce mai haƙuri kan dafa dutse har ya sha romonsa." Mimie ce ke wannan tunanin a fili kuwa cewa ta yi "Kai! Allah ya raba mu da aikin danasani."
Sameer ya amsa da Amin.
Su na isa kalgo suka ajiye Sakina, ta yiwa Innarmu Sallama tare da ɗaukar kayanta ta fito waje gun mota.
Har bakin mota Innarmu ta raka ta, ta na ta yiwa Sameer godiyar riƙe mata jikokinta da ya yi da amana, tare da masu addu'ar samun zaman lafiya mai ɗorewa.
"Ai duk mai son Uwa dole ya so ƴaƴanta." Ya faɗa tare da ciro kuɗi a aljihun wandonsa ya miƙa mata.
Ta karɓa ta na godiya.
Suka yi Sallama suka hau mota sai Abuja.
Bayan wani ɗan lokaci da dawowarsu daga Bk, ta koma bakin karatunta, yayin da Sameer ya ke zaune a gida zaman jiran aiki.
©©©©©
Bangaren Mommy kuwa zaman Ruma a gida ya fara damunta, yanzu kimanin wata biyu kenan ta na zaune a gida amma bai zo ya maida matarsa ba, don haka ta shirya ta je gidan Hajiya hafsat domin ta raka ta gidan malaminsu a mata aikin da Saheen zai maida Ruma ɗakinta.
Bayan sun je ne ta kokawa malamin nasu cewa wancan asirin da ya masu ya karye, kuma duk ɗan abinda ta samu daga hannun sirikin nata ta cinye, ga shi ya daina bata abinsa, har ma da guzurin saki ya haɗo 'yarta da shi.
A nan malamin malamin tsibbun nasu ke mata bayanin sai dai ta yi haƙuri, domin yanzu akwai tsari sosai a jikin ahalin gidan gaba ɗayansu, ba wanda za su iya taɓawa.
Nan fa suka yi cin mutunci tsakaninta da malamin, ta gaggaya mai maganganu, wai ya ci kuɗinta a banza, dama yasan aikinsa ba mai garantee bane don haka bata yafe ba, har da ce masa ɗan akuya, shi ko ya ce ta je za ta gani.
Haka suka baro ƙauyen da yake, Hajiya hafsat na cike da tsoro, domin kalaman malamin nata sun ruɗar mata da ciki, ta san shi sarai zai iya yin komai akan wannan maganar, sai ƙirjinta ke harbawa da ƙarfi dama kuma ita ke tuƙi, su na shigowa garin Abuja kan babban titi motar ta ƙwace mata.
Tun daga nan ba su kuma sanin inda kansu ya ke ba sai farkawa suka yi suka gansu a asibiti.
Ko da labari ya riski Ruma hankalinta ya tashi matuƙa, da kukanta ta isa asibiti don ganin halin da Mommynta ke ciki.
A asibitin ne ta kira Abbanta ta shaida masa, haka ta kira su yaya Sunil da Suhail, daga makaranta suka wuce asibitin don ganin Mommynsu.
Abbansu ma washe gari ya zo.
Su ma iyalan gidan Alhaji Salman sun girgiza, mussanman Mimie duk ta fi su shiga damuwa.
Kowa na gidan ya damu inka ɗauke Saheen domin shi kam, ko a kwalar rigarsa.