← Book details A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 36

Sashe 35

A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasa-wasa ƙaramar magana ta zama babba domin yanzu kusan wata ɗaya kenan amma Sameer ya ƙi ya koma, daga gun aikin nasa ma sai kiransa ake a na buƙatar ya dawo amma ya ƙi.

Ganin haka ya saka watarana da yamma Daddy ya sami Mamy akan maganar, ya ce "Mamyn yara, ki yi haƙuri ki bawa Sam matarsa ya tattara ya tafi, domin wannan al'ada ce ba fa addini ba, kuma ma ai ta yi arba'in ɗaya, idan ma baki amince da hakan ba, sai Mommynta ta shirya su tafi tare hakan zai fi mana kwanciyar hankali."

Da farko Mamy ta so ta yi gardama, amma kasancewar wannan ba dabi'arta ba ce yin musu da maigidanta, don haka ta haƙura ta ce "Shikenan Alhaji tun da ka faɗi haka, sai a nemawa Mommyn nasu visa ta bi su can, tun da ma ai batada miji a yanzu."

Da wannan shawarar suka kawo karshen maganar tafiyar, kowa ya fice zuwa yin sabgar gabansa.

Da dare Mamy ta kira Sameer ta shaida masa shawarar da suka yanke ita da Daddynsa.

Bai Musa ba, saboda shi ma zai so matarsa da 'yarsa su samu kulawar da ta dace a wannan stage ɗin, wanda shi ba zai samu damar yin hakan ba saboda aikinsa.

"Nagode Mamy Allah ya ƙara girma, sai a gayawa Mommyn ta shirya da wuri koh?"
Ya na gama faɗa ya miƙe don zuwa makwancinsa.

Alhaji Salman da kansa ya nemarwa Mommy visar, ta kuwa shirya tsaf, bayan sati biyu ta yi Sallama da ƴaƴanta ta bi su ƙasar Dubai.

Da yake zuwa lokacin Mimie ta kammala digirinta, ta yi komai ta haɗa takardunta kawai ta bi mijinta ƙasar Dubai.

%©©©©
Bayan saukarsu a Dubai, Rayuwa mai daɗi suka shimfiɗa cike da so da ƙaunar juna, ganin twins sun yi baki sosai domin yanzu shekarunsu uku, hakan ya saka Sameer ya nemo masu makarantar nursery mafi kusa da gidansa a can, ya saka su.

Bayan wani ɗan lokaci, Mimie ta shiga jami'ar da ya kammala, don yin masters ɗinta A nan.

Su Mommy an zama mutanen Dubai sai shanawa take abinta, a zaune take ta na tunani "Allah karimun, yau gata a cikin dukiyar Alhaji Salman ko ta ce ta ɗansa ta na watayawa yanda ta so, tabbas da ta san da zuwan wannan ranar da ba ta yi gangancin faɗawa shirka ba, ashe gajin haƙuri ta yi, ta fitar da maitarta a fili, ashe wannan lokacin da take fata har ta kauce hanya akansa zai zo mata cikin sauƙi da ta kwantar da hankalinta.

"Astagfurullah! Astagfurullah!! Allah ka yafe mun haƙiƙa a baya ina cikin ɓata mabayyaniya." Ta faɗa a fili.

©©©©©%%%

Bayan kamar wata uku da komawarsu Dubai wani tashin hankali ya Kunno Kai acikin rayuwarsu.

Bakomai ba ne ya ɗaga hankalin dukkanninsu face rashin lafiyar Sameer, a hankali ciwon ya fara shigar shi, abun ya fara mai da yawan kasala, wasa wasa ciwo sai daɗa gaba ya ke, domin yau kusan satinsa biyu kenan ba ya fita aiki, sai dai ya ba da uzurinsa akan cewa ba shi da lafiya ne.

Duk da cewa a zahirin gaskiya ba wannan ne karo na farko da Sameer ya fara fuskantar irin wannan matsalar ba, tun bayan tafiyarsa Dubai a karo na biyu bayan aurensu kenan ya fara jin wannan yanayin, sai dai a tunaninsa ko gajiyar aiki ce da sauran abubuwan da ba a rasa ba.

Amma zuwa yanzu ya tabbatarwa kansa cewa akwai wata cutar da take addabarsa, don haka ya yanke shawarar zuwa ganin likita.

Ya na daga kwance kan gadonsa ya kalli Mimie dake zaune a gefensa ta na sharar hawaye ya ce "Ki daina kuka Sweety, cuta fa ba mutuwa ba ce, yanzu dai dauko wayata ki kira mun Abokina doctor Sadeeq, ki ce na ce ya zo ya kai ni asibiti." Ya ƙarashe maganar daƙyar da alama ya na shan wuya sosai.

Hawayenta sun kasa tsayawa, bata iya cewa komai ba, sai janyo waya da ta yi ta dannawa doctor Sadeeq kira.

Bugu biyu ana uku ya ɗaga, ta shaida masa saƙon abokinsa, cikin hanzari ya fito daga asibitin ya nufo gidan Sameer.

Ganin yanayin Sameer ɗin ya ruɗar da shi saboda haka ba jinkiri ya saka shi a mota, Mimie ma ta faɗa motar hankali a tashe, Sadeeq ya tada motar cikin hanzari ya nufi asibitinsu.

Yayinda suka bar Mommy a gida ita da yara sai masu aikin gidan.

Gwaje-gwaje da aune-aune aka hau yi masa, sannan aka shiga ba shi agajin gaggawa, kafin fitowar sakamakon binciken.

Hankalin Mimie a tashe yake ta kasa tsaye ta kasa zaune, sai zarya take a harabar asibitin ta na kuka, gani take kamar za ta rasa shi kamar yanda ta rasa Bassam a rana mai kamar ta yau.

Bayan wani lokaci sakamakon gwaji ya fito nan take aka gano cutar hapatatis a jikinsa(wato ciwon Anta) a nan doctor Sadeeq yake mata bayanin hakan ta faru da shi ne sakamakon shan giya da ya ɗau lokaci ya na yi a baya.

Hankalin Mimie idan ya yi dubu ya tashi, miƙewa ta yi daga kan kujerar office ɗin da take zaune, ta fara kai-kawo a filin ɗakin ta na kuka, doctor na ƙoƙarin mata bayanin mafita amma ina! Bata saurare shi ba sai ci gaba da kukanta ta ke ta na faɗar faɗar "Shikenan, yanzu kai ma yaya Sameer haka zan rasa ka kamar yanda na rasa Uncle? A baya na rasa uban ƴaƴana, yanzu kuma zan rasa wanda ya tarairaye su kamar ƴaƴan cikinsa, kuma zan rasa uban 'yata a karo na biyu? Ka da ka mutu kabarni a ƙasar da ba ni da kowa sai kai da ƴaƴana, Ya Ubangijina kada ka ɗora min ƙaddara da ba zan iya cinyewa...." Kuka ne ya ci ƙarfinta ta kasa ƙarasawa sai komawa da ta yi ta zauna a inda ta tashi daga farko.

Anan doctor Sadeeq ya shiga rarrashinta, daƙyar ya ciwo kanta da kalaman tausasa zuciya domin ya tausaya mata matuƙa.

A nan ya tabbatar mata cewa akwai mafita, mafitar kuwa ita ce a yanzu za'a ɗora shi akan magani domin cutar bata riga ta yi nisa ba, idan ya shanye maganin bai ji sauƙi ba za'a masa aiki.

Ta ɗan nutsu amma ba don hankalinta ya kwanta ba, ranar a asibitin ta kwana, duk da doctor Sadeeq ya shaida mata su na masu kula da mara lafiyar ta je gida kawai, amma haka ta kafe sai da ta kwana, sai dai ta yi waya ta shaidawa Mommy halin da ake ciki, ita kuwa Mommy ta kira Mamy da Mama ta shaida musu domin su taya su da addu'a.

©©©©©©

Hankalinsu Daddy ya tashi fiye da tunani, a lokacin da labarin rashin lafiyarsa ya riske su daga nan suka duƙufa da addu'a ba dare ba rana.

Daga ƙarshe Daddy kasa haƙura ya yi sai da ya shirya shi da Mamy suka je Dubai don duba lafiyar ɗan nasu.

Alhmdulillah sun same shi jikin da sauƙi, amma hankalin Daddy bai kwanta ba don haka ya saka hannu kawai don a yi masa tieter, tunda wannan ita ce mafita ta ƙarshe da ake hangowa kafin abin ya yi nisa.

Daddy da Mamy ba su baro Dubai ba sai da suka tabbatar an yiwa Sameer aiki ya ji sauƙi, da yake a can suna da kwararrun likitoci, an ɗora shi akan magani ya na sha, likitoci suka tabbatar masu da cewa insha'allahu cutar ta tafi kenan, muddin zai tsare magani don dama kaɗan ta fara kama hantarsa.

A tare suka juya zuwa Nigeria da Mommy bayan ta share watanni a can.

Bayan Sameer ya ji sauƙi rayuwar ta komo kamar da mai cike da annashuwa.

Ruma ma ta kuma haihuwa ta biyu, ta samu ɗa namiji da ya ci sunan Salman ake masa inkiya da (Ashraf).

©©©©©©©©©©©

Bayan Shekaru biyar Sameer ya zama ƙwararren likita a ɓangarensa, a wajen Mimie ma haka ne tuni ta gama masters ɗinta ta fara aiki a asibitin da mijinta ke aiki, kowannensu ya yi kyau abinsa, duniya ta zamar masu sabuwa kamar basu fuskanci wani ƙalubalai ba a baya.

Mimie ta sake haihuwar ɗa namiji wanda ya ji sunan Abubukar Sadeeq suna yi masa inkiya da (Abba) kasancewar sunan babanta aka sakawa yaron.

Affan da Afeef sun girma sun zama 'yan samari, yanzun su na cikin shekara ta tara kenan a rayuwarsu, su na primary4 amma wayon yaran ya wuce na shekarunsu, a lokacin ne kuma Little ta cika shekara biyar ta na nursery 2 yayin da Abba yake da wata tara a duniya.

Sameer ya zama magidanci mai shekaru arba'in da ɗaya a rayuwarsa yayin da Mimie take da shekaru 31, kamar yanda gangar jikinsu da shekarunsu ke ƙaruwa haka kauna, soyayya da shakuwarsu take ƙaruwa.

Ko waye kai idan ka ga iyalan Sameer dole su birge ka, don kuwa Sameer ba ya nuna bambanci tsakanin ƴaƴansa da na Bassam, duk da cewa ya na tsananin ƙaunar little a rayuwarsa sai ya ɓoye hakan a ƙasan ransa, domin a zahiri ya fi nuna ƙaunar 'yan biyu, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yake yiwa Mimie ba.

Da yammacin wata ranar Lahadi dukkanninsu su na gida kasancewar ranar hutu ce.

Alhaji Sameer ya na zaune a falo ya na karatun jarida, Mimie kuwa ta na kitchen ta na girkin rana, Affan ne ya shigo ɗakin da gudu yayin da Afeef ke binsa a baya, ƙarasowa yayi gaban Sameer ya zauna ya na faɗar "Dad don Allah ba ni ne Aliyu B. Aliyu ba, shi kuma Bassam B. Aliyu?" ya ƙarashe zancen yana nuna hausaininsa.

Murmushi manya Sameer ya yi kana ya daga kai alamar tabbatarwa ya ce "Hakane."

"Yawwa Daddy wai to me yasa a makaranta ake kiran little da Rukayya Sameer amma mu sai a ce mana B Aliyu?, Ga shi kuma kai sunanka Sameer ko Dad?" Afeef ya watso masa tambayar da ba zato ba tsammani.

Jikinsa ne ya yi sanyi ƙalau, hakan ya saka ya miƙe tare da ajiye jarida ya shige ɗakinsa ya rufo ba tare da ya ba su amsa ba.
Chapter 35 · 0% Book details