← Book details A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 36

Sashe 11

A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar numfashi ya sauke cikin alamun fara jin barcin ya ce "Haba Mamyn yara ki daina damun kanki a kan wannan, ni na san me zanyi, Ni da kaina zan maida ta gida Kano jibi idan ya so sai na roƙo alfarma gun iyayenta ko za su bar mana ita na ɗan wani lokaci."

Ganin jikin Mamyn ya yi sanyi qlau, ya saka shi miƙewa zaune ya ce "Haba my wife, ki kwantar da hankalinki, ki kwanta yanzu ki yi barci, na miki alƙawari komai zai tafi dai-dai insha'allah."

Ba ta ce komai ba sai ajiyar zuciya da ta sauke ka na ta kwanta akan gadon cike da tunani iri-iri.

®®®®®®®®®®®

Kashe gari wuraren ƙarfe goma Sameer ya ɗauko ƙasa cikin shigar ƙananun kaya jins da red t-shirt, ba hula akansa anma ya yi matuƙar kyau da ya ke shi fari ne sai kayan su ka amshe fatarsa sosai.

Kai tsaye ɓangaren Mimie ya nufa, don tun da ya ga ba ta falon ya tabbatar ta na ɗakinta.

Tarar da su yay su na fira ita da Ruma, ga tulin tufafinsu da su ka samu a gidan su na jerawa a akwati.

Da sauri ya ƙaraso ciki baki na ɓari ya ce "me kuke haka?"

Bai jira sun amsawa ya ware murya ya na kwalawa su Maryam kira "Maryam! Maryam!! Fariha! Fariha."

Daga can ƙasa su ka jiyo ana ƙwala ma su kira da gudu su ka hauro sama har su na yar rige-rige.

Cikin fushi ya kallesu ya ce "Wannan ba aikinku ba ne?" Yay tambayar ya na nuna masu kayan hannun Mimie da yatsa.

"Eh ranka yadaɗe." su ka faɗa baki na ɓari."

"Shine kuma dan ku na isassu ku ka bar ƙaramar yarinya da aiki irin wannan?."

"Ayi haƙuri yallaɓai wallahi ba mu san za ta yi ba ne." Su ka faɗa tare da ƙarasawa gunta su ka janye akwatin su ka fice daga ɗakin domin ba za su iya tsayawa gu ɗaya da oga Sameer ba saboda kwarjininsa.

Zuhra da Ruma kuwa tun lokacin da ya shigo ɗakin su ke kallonsa cike da mamakin abin da yayi yanzun.

Guri ya nema ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da ke ɗakin sannan ya dubi Zuhra ya ce "My sister akwai Magana mai muhimmanci da na ke so nu yi da ke."

Jin hakan ya sa Ruma ta miƙe ta nufi hanyar fita daga ɗakin.

"A'ah! Ina za ki kuma sister?" Cewar Mimie.

Murmushi ta yi sannan ta ce "Zan sauƙa ƙasa ne gun Mamy." Daga haka ta yi ficewarta ba tare da ta sake cewa komai ba.

Shi ko Sameer Sosai ya ji daɗin abinda Ruma ta yi, haƙiƙa kanta na ja tun da har ta fahimci cewa ya na son kaɗaicewa da Mimie, haka kawai sai ya ji ta burge shi.

Bayan fitarta Zuhra ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na wasa da y'an yatsun hannunta, yayin da ta ke zaune a kan carpet.

"Sweet sister!" Ya kira ta cikin sanyayyiyar muryarsa.

Ɗagowa ta yi ta na kallonsa.

Shiru ya gifta na wani ɗan lokaci, can ya ce "A yau ɗin nan zan sanar da ke sirrin zuciyata, na sani kin riga kinsan cewa Margayiya Mimie ƙanwata ce uwa ɗaya Uba ɗaya kuma ina matuƙar ƙaunarta, amma ina so ki sani soyayyar da na ke mi ki ta na da banbanci da tata."

Da sauri ta ɗauke idonta daga na sa ta kuma Sunkuyar da kanta ƙasa.

Bai damu da hakan da ta yi ba ya ci gaba da cewa "Daga zuwanki zuwa yanzu na tabbatarwa kaina cewar na faɗa soyayyarki, saɓanin yanda na ke tunani daga farko, a farko na ɗauka cewa soyayyar y'an uwantaka na ke maki, sai a yanzu na tabbatar cewa, Soyayyar aure na ke ma ki."

A razane ta ɗago idonta ta na kallonsa da mamaki a fuskarta, bakinta sai motsi ya ke alamar ta na son yin tambaya amma ta kasa.

Murmushi ya yi ya ce "Ƙwarai da gaske, ina matuƙar sonki, ina ji a raina idan ban same ki ba Zan shiga wani mummunan yanayi, ki taimake ni ki so ni Mimie, ina so ki dawo cikin ahalinmu har abada."

Ganin ba ta da niyyar ba da amsa ya sa ya miƙe ya bar ɗakin cikin wani irin yanayi da mutum bai isa ya fassara sa ba, shin farin ciki ne ko akasin haka."

Zuhra kuwa ta shiga ruɗanin jin maganganunsu, tabbas ta na cikin wani yanayi, yanzu ya za ta yi kenan?

A haka Ruma ta shigo ta Same ta.

®®®®®®®®®®®

Da Azahar driver ya ɗauke su zuwa gidan Mommy.

A ƙofar gidan ya sauke su sa'annan ya fito ma su da akwatinsu daga but ɗin motar tare da wasu kayan arziƙi da Mamy ta haɗosu da su.

A falo su ka sami Mommy zaune ta na kallo cike da mamaki ta ke kallonsu, wai yaranta ne su ka yi kyau haka? Lallai hutu abu ne na musamman.

Da sauri ta taso ta rungume Ruma ta na faɗar "Oyoyo my daughter."

Su ka rungume juna su na murna.

Zuhra ce ta ƙarasa jikin Mommy ta na faɗar "Oh! Mommy ta Ruma kawai ki ke kin manta da y'ar lelenki Zuhra."

Mommy zame jikinta ta yi daga na Zuhra ta na taɓe baki, ba ta ce komai ba, ta ja hannun Ruma ta zaunar da ita kan kujera su na cigaba da hirarsu.

A ranar Abbansu Ruma ya turowa Mommy kuɗi dubu talatin ya ce abawa Zuhra ta yi kuɗin mota kamar yanda ya saba idan ta zo.

Amma saboda tsabar hassada irin ta Mommy ta kuɗurce a ranta ba zata bata kuɗin duka ba, tunda ita Habu zai yiwa haka.

Daga Zuhra har Ruman mamaki su ke irin wannan sauyin hali da Mommy ta yi lokaci ɗaya, "To me ya faru bayan tafiyarsu?"

Ranar dai a haka aka kwana cikinsu ba wanda ya gane kan Mommy.

Shigowar su yaya Sunil da dare ne kaɗai ya rage mata damuwar da ta ke ciki.

Washe gari

Tun bakwai na safe Mommy ta tattarowa Zuhra Komai nata ta ajiye a falo, sannan ta wuce ɗakin Ruma don ta da Zuhra.

Bayan ta shirya Mommy ta ba ta dubu biyar wai ta yi kuɗin mota.

Cike da mamaki Zuhra ke kallonta can ta ce "Uhmm! Mommy da kin barsu kin manta tare da Daddy zamu tafi?"

Ba musu ta kwashe kuɗinta ta mayar jaka, dama ba da niyya ta bayar ba don kawai ka da duniya ta zarge ta da rashin kirki ne ta gwada bayarwar.

Shiru-shiru har takwas da rabi Daddy bai zo ba, Mommy ce ta yi gajin haƙuri ta ce "Wai nikam sai ƙarfe nawa ne za ku tafi?"

"Uhmm, nima bansani ba Mommy bari na kira shi." Zuhra ta faɗa ganin ana mata kora da hali.

Wayarta ta ciro ta danna mai kira bayan sun gaisa ta ce "Yawwa Daddy na ce ƙarfe nawa ne tafiyarki? Na fa shirya."

Murmushi mai sauti yay ya ce "Yar gidan Daddy kenan, Sarkin zumuɗi, to ki ƙara haƙuri kaɗan nima shirin na ke nan da 30mins za ki ganni."

"Ohk Daddy sai ka zo."

Daga haka ta kashe wayar.

Mommy kuwa sai taɓe baki ta ke ta na wurga mata harara.

Ita dai bata kuma magana ba domin daga jiya zuwa yau jinta ta ke kamar kan ƙaya, gidan yayi mata zafi saɓanin da, da ba inda ya fi mata daɗin zama sama da nan.

Sai ta ke ganin kamar Mommyn ta tsaneta, kuma bata san me ta yi mata ba.

®®®®®®®®®®®

A can gidan Daddy Kuwa da misalin 9:12am ya fito a shirye tsaf domin tafiya zuwa garin Kano.

Iyalansa ne gaba ɗaya su ka yo ma su rakiya cike da alhinin tafiyar Sisternsu.

Har zai shiga Mota Sagir ya rugo da gudu ya riƙe babbar rigarsa ya na faɗar "Daddy ni dai zan bika, ka kaini gun sisterna."

Mamy ta je ta janyo shi jikinta ta na lallaɓasa, amma fur ya ƙi daga karshe ma ya saka ma su kuka, shifa lallai sai an tafi dashi gidansu yayarsa.

Ganin ya ƙi daina kuka da rigimar ya sanya Daddy ya ce Mamy ta je ta haɗo masa kayansa, ai kwana biyu ne kaɗai zai yi ya juyo.

Shi ko Sagir faɗawa motar ya yi ya na murna yayin da Mamy ta shiga ciki don cika umarnin mijinta.

Sameer sai kallon autansu ya ke ya na murmushi sai ya ji inama ace shi ma ya na da dama irin ta Sagir, tabbas da ya aikata hakan.

Can bayan wani ɗan lokaci sai ga Mamy janye da akwatin Sagir, aka saka ma su but, drivern Daddy ya ja su ka bar gidan.

Sai ɗaga ma su hannu su Saheen ke yi.

Kai tsaye su ka wuce Area 1 don ɗaukar Mimie.

A ƙofar gidan su ka faka ya kira ta a waya sai gata ta fito su Mommy harda to mata rakiya.

Ta ƙarasa gaban motar Daddy ta na mishi sannu da zuwa tare da Faɗar "Alhaji mun gode da karamci, Allah ya ƙara girma mun gode, mungode, Allah ya kai ku lafiya."

Kuɗi ya ciro bandir ɗin 500 guda ɗaya ya bata, ba kunya ta amshe ta na washe haƙora........

Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼

_08109634202_

Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin.

Follow me on Wattpad @ummu inteesar.

UMMU INTEESAR CE❤️💛💚💙💔💛

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*A SANADIN KAMA*

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR:*
*SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*

*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*

Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal.

Ga mai buƙata sai ya tura kuɗin ta wannan account ɗin:

Account name: Rukayya ibrahim lawal
Account no:0431343346
Gt bank.

KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE IDAN DUKA BIYUN KA KE SO A SANADIN KAMA DA ƘURUCIYAR SAPNAH TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200.

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

*BISMILLAH RAHMANIR-RAHIM*

Free Page 2️⃣7️⃣↪️2️⃣8️⃣

Ɗaga Zuhra hannu ta ke ta na faɗar "Ki gaida gida da iyayen naki, Allah ya sauke ku lafiya."
Chapter 11 · 0% Book details