Sashe 28
A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shamsiyya ta matso da ɗayan kusa da na farkon yadda zai iya ganinsu sosai, shi kuwa sai murmushi ya ke a ransa ya na ƙara godewa Allah da wannan kyautar da ya masa ya na gaf da barin duniya, domin ya na ji ajikinsa cewa tasa ta zo ƙarshe.
Sosai ya ke jin ƙaunar yaransa na ratsa shi, da yake yaran duka da shi suke kama, komai da komai nasu iri ɗaya, ba inda suka bar shi har a kalar fata.
"Allah ya maku albarka." Shi ne kaɗai abinda ya faɗa ya na ta famar murmushi.
Bayan sun tabbatar da ya ga yaran da kyau, suka janye daga gun.
"Matata fa?" Ya tambaya.
Sakina ce ta je ta ƙara matso da Mimie daf da shi, dai-dai inda zai iya hangotan daga kwance.
Kallon ta ya yi ido cikin ido, sannan ya fara magana a wahalce ya na neman gafarar ta faɗar ya ke "Ki gafarta min uwar ƴaƴana, haƙiƙa na san na cutar dake, na ci amanar soyayya a baya lokacin da sihiri ke ɗawainiya da ni, ki yafe mun ki roƙa min gafarar su Abba da Alhaji Salman, ga amanar ƴaƴana nan na bar miki, na san za ki ba su tarbiyya mai kyau, don Allah ka da ki ce za ki rama abinda muka miki a kan ƴaƴana, pls ki yafe mun, Ni tawa ta zo ƙarshe."
Ya na maganar numfashinsa na sassarƙewa, sheɗarsa na yin sama da ƙasa.
Kuka take sosai ta ɗago da rinannun idanunta ta kalle shi ta ce "Na yafe maka Uncle, na yafe maka uban ƴaƴana, na yafe maka...."
Murmushi sosai ya yi a dai-dai lokacin da sheɗarsa ta zo daf da maƙogwaro ya ce "La'ilaha illallah, Muhammadu Rasulullah......"
Ya na zuwa nan rai ya yi halinsa.
Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Tashin hankali ba a sama ka rana, nan fa Mimie ta haukace, ta kai hannu tana jijjiga shi ta na faɗar "Uncle! Uncle ka tashi, wallahi na yafe maka ka tashi Uncle, ka tashi mu shimfiɗa sabuwar rayuwa mai cike da farin ciki tare da ƴaƴanmu.
A ɗimauce take zancen, ganin baya motsi kuma idonsa ya kakkafe yasa ta juyo ga Innarmu wacce take ta faman salati ta na kuka ta ce "Inna ki ce ya tashi wallahi na yafe, ki faɗa masa."
Sosai innar ta ji tausayin Mimien na ratsa ta, kawai sai ta zo ta rungume ta suka ci gaba da kukan.
Shamsiyyan ce ta yi ƙarfin halin zuwa ta kira likita itama ta na kuka sosai.
Ya na shigowa ɗakin ya ga abunda ke faruwa, kawai sai ya shafe masa fuska tare da jan mayafi ya rufe masa fuska.
Ai kuwa Mimie na ganin haka ta tabbatar ya mutu, kawai sai ta kuma saka ihu tare da sumewa a kan kujerar da take....
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202
Follow me on Wattpad @ ummu inteesar
UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
DA KUMA
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 6️⃣5️⃣↪️6️⃣6️⃣
Iya tashin hankali Innarmu ta gani a ranar.
A haka suka tura keken tare da mayar da Mimie ɗakin da take jinyar a ciki, likitanta suka kira don ya duba ta.
Ko kafin ta farfaɗo har an wuce da gawarsa can gida don masa sutura.
Dogon suma ne ta yi, don haka bata farfaɗo ba sai wajajen tara na dare.
Bayan ta dawo hayyacinta ta cigaba da kukanta cikin dasasshiyar murya, rayuwar soyayyarsu ta baya da farkon aurensu kawai take tunawa, duk ta fita a hayyacinta.
Innarmu dake zaune gefe kusa da ita rungume da hassan, ita ce ta dubi Shamsiyya ta ce "Ɗauki wayatta ki kira min innatta, ya kamata su san halin da a ke ciki."
Ba tare da budurwar ta amsa ba ta miƙa hannu ta ɗauko wayar tare da miƙawa Sakina, da ido ta mata nuni da ta kira.
Da yake Sakinan ita ce mai ɗan dama-dama, sai kuwa ta shiga jerin numbobin ta na dubawa.
Can ta gano number da a ka rubutawa *Mamata* ai kuwa ta danna mata kira.
Bugu biyu a na uku a ka ɗaga kiran, sallama ta yi, bayan ta gaishe da maman.
Cike da mamaki Maman ta tambaya "Wacece? Ina Mimien?" A ɗan tsorace take zancen.
Cikin matuƙar ƙarfin hali Sakina ta ɗan yi busasshen murmushi ta ce "Mama! Sakina ta ƙaunar Bassam, dama na kira na in sanar miki Anty Mimie ta haihu ɗazu da rana, amma c.s anka mata."
Sosai mama ta yi murnar jin wannan labarin duk da ba komai take ganewa ba, saboda Hausar Sakinan ba ta kanawa ba ce.
Cikin rawar baki Mama ta ce "Kai masha'allah, me a ka samu?"
"Y'an biyu maza." Ta ba ta amsa.
Nan fa murnan Maman ta daɗu, amma da ta fahimci kamar akwai yanayin damuwa a tattare da Muryar Sakinan, sai ta ce "Masha'allah! Allah ya raya, amma ina Mimien ban ji ta ba, ko da wata matsala ne, na ji muryanki wani iri."
Guri ta nema ta zauna ta na matsar ƙwalla ta ce "Ita dai da dama, ga mu nan asibiti domin ta jiggata Sosai, amma kuma yayan ne...."
Sai kuma muryarta ta fara rawa.
Cikin tashin hankali Mama ta ce me ya sami yayan naku Sakina?"
Cikin kuka ta ce "Bayan haihuwarta, ko awa ɗaya ba a yi ba, yaya ya rassu."
Duk da cewa ba a son ranta a ka yi auren ba, amma ta girgiza sosai da wannan mutuwar.
Cikin tashin hankali ta ce "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Allah ya jikansa da rahama, yanzu ina Mimien? Don Allah idan ta na kusa ki ba ta wayar."
Tashi ta yi ta je bakin gadon Mimie dake kwance cikin wani yanayi ta na sauraron wayar ta su, ta miƙa mata wayar.
Karɓa ta yi amma bata iya cewa komai ba, ta na jin maganar Maman tata kawai sai ta fashe da matsanancin kuka.
Lallashin duniyar nan Mama ta yi, amma kamar zuga ta take, duk yanda ta kai da son su yi magana Mimie bata ce uffan ba, sai kuka a kan dole ta kashe kiran, cikin wani irin yanayi na rashin jindaɗi.
®©©©©©©©©
Kano
Ƙarfe goma na dare Baba ya shigo gidan nasa, ya samu matarsa cikin wani yanayi na jimami.
Tambayarta ya yi "Lafiya dai Maman Zuhra? Me ke damun ki?"
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Mimie ta sauka ɗazu, an samu y'an biyu maza."
Da fara'a a fuskarsa ya ce "A'ah to ai wannan abin farinciki ne, miye abun tada hankali a nan?"
Cikin raunanniyar murya ta ce "Allah ya yiwa mijinta rasuwa bayan wasu mintuna da haihuwarta."
Sosai ya ji wani shock ya ja shi, amma gudun kada ya karyar mata da zuciya sai ya ce "Allahu akbar! Allah ya jikansa da rahama."
Ameen ta faɗa.
Ya ce "Addu'a za ki yi masa Maman Zuhra, yanzu addu'ar mu kawai yake buƙata, amma damuwa ko kuka duk ba su da amfani."
Da haka ya samu ya ciwo kanta, a nan suka zauna hira, cikin hirar ne suka yanke lokacin tafiya birnin Kebbi.
Washe gari Mama ta kira Mamy ta sanar da ita abinda ke faruwa da kuma ranar da za ta tafi, a nan Mamy ta ce ta bari su tafi tare ranar talata a maimakon ranar Litinin da ta saka.
Bayan ta gama waya da Mamyn ne ta kira Mimie, wannan karon Mimien ce da kanta ta ɗaga suka gaisa, don yanzu an samu ta daina kukan sai dai kukan zuci da ba ta tunanin za ta iya daina shi har ko yaushe.
Sosai Mama ta mata nasiha, tare da janyo hankalinta a kan ta yi haƙuri da rayuwa a duk yanda ta zo mata.
Bayan ta gama ne ta nemi da a haɗa ta da Innarmu a waya ta mata Gaisuwa tare da Barka.
Mimie ta yunƙura ta zauna tare da miƙawa innar waya ta ce "Innarmu ga Mamana za ta miki gaisuwa."
Jiki a sanyaye innar ta karɓa, don yanzu wata irin kunyar yarinyar da iyayenta take ji, saboda sanin abinda ta aikatawa yarinyar a baya.
Gaisawa suka yi sannan ta mata gaisuwar mutuwar da kuma barkar haihuwar sannan ta kashe wayar.
©©©©©©©
Haka kuwa a ka yi ranar talata tun safe Mamy ta taso zuwa garin Kano, da misalin ƙarfe sha biyu ta iso, abinci kawai ta ci suka ɗau hanyar zuwa Bk.
Sai dare suka isa, kai tsaye asibitin da a ka kwatanta masu su ka nufa.
A can suka tarad da yaran cikin ƙoshin lafiya sai abinda ba a rasa ba, domin innarmu da ƴaƴanta su na iya ƙoƙarinsu gurin kula da Mimie da yaran.
Mimie ta ji daɗin zuwan Mamanta da kuma Mamynta sosai, hakan ya ɗauke mata wani ɓangare na damuwar da take ciki.
Kwanansu biyar a asibitin a ka sallame su, ganin jikin nata ya yi kyau, Innarmu da kanta ta bawa su sakina maƙullan gidan Bassam na birni suka buɗe shi tare da gyarawa, a ka kai Mimie can don yin wankan jegonta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.
©©©©©©©
Ranar juma'a su Baba, Alhaji Salman da Saheen suka zo don suna da kuma yin gaisuwa.
Kalgo suka fara zuwa suka yiwa Innarmu da y'an uwanta gaisuwa sannan suka dawo gidan Mimie.
yau ta kasance ranar Asabar a yau ne kuma za a yi sunan y'an biyu, tun da sassafe Innarmu ta je bayan gida inda turken dabbobinta ya ke, ta saka a ka kamo manyan raguna biyu tare da madai-daicin santa wanda ta ƙwallafa ranta a kansa, ta bayar a ka yankawa jariran tare da masu suna.
Yara sun ci sunan Aliyu da Bassam wanda Mimie da kanta ta zaɓawa yaran suna.
Hassan shine Aliyu wato takwaran baban Bassam, sai kuma Hussain wanda ya ci sunan mahaifinsa, amma ana masu inkiya da *Affan* da *Afeef*