← Book details A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 36

Sashe 15

A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin kuwa Zuhra ta na Ss3 a shekarar za ta yi candy, har yanzu dai ta na nan a makarantar y'an mata ta gandun albasa, ba yadda Daddy bai yi ba ta bari a canza mata makaranta amma ta ƙi, acewarta ko a makarantar gwamnati mutum ya ke zai iyayin karatu idan ya so."

Zahirin gaskiya ba ta so a raba ta da ƙawarta Raliya da su ka ta so tare tun ƙuruciya, sosai Zuhra ke son Raliya ta na kyautata mata, barin yanzu da su ka fara samun abun duniya komai ta kwasa Raliya ta ke kaiwa, ba ƙaramin daɗi Raliyan ke ji ba, domin su ma sun shaida cewa su Mimie sun samu.

Ko da yaushe Daddy da Mamy cikin turawa Zuhra kuɗi su ke a account domin yanzu sun ƙara shaƙuwa fiye da da, domin a shekaru biyun da su ka gabata duk hutu a Abuja ta ke yinsa, sai hutu ya ƙare ta ke dawowa kano.

Saboda haka yanzu koda yaushe tana cikin yin vidio call da su yaya Saheen da Salim a laptop ɗinta ko a wayarta.

Lokacin da ya rage baifi saura sati uku ba afara weac a lokacin ne kuma yaya Sameer ya tayar mata da ƙayar baya akan zancen aurensu, shima Daddy a lokacin ya tuntuɓe ta don son jin shawarar da ta yanke, a bangare ɗaya kuma ga Bassam sai zumuɗi ya ke akan alƙawarin su ya kusa cika harma ya sanar da iyayensa domin su zo neman aure.

Nan fa hankalin Mimie ya tashi ta rasa yanda za ta yi, gabaki ɗaya hankalinta a tashe ya ke gashi har zuwa lokacin ta kasa samun mafita.

Ana cikin wannan halin ne wata rana da daddare iyayenta su ka yi kiranta zuwa falon Baban nata domin su nusar da ita akan wannan lamari.

Zaune ta ke a ƙasa kan carpet ta sunkuyar da kanta ƙasa yayin da Baba ya fara magana kamar haka:Zuhra ina so ki nutsu sosai ki saurare ni, lokaci ya yi da za ki sanar mana wa za ki aura acikin manemanki biyu, kin sani dole ɗaya za ki aura don haka wa ki ka zaɓa?"

Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa idonta ya fara tara ƙwalla ta na tunanin ita ta ina ma za ta fara?

"Muna sauraron ki" mama ta faɗa.

Buɗi baki ta yi daƙyar ta ce"Baba ni.........

Follow me on wattpad @Ummu inteesar

UMMU INTEESAR CE❤️💔💛

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*A SANADIN KAMA*

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*

*DA KUMA*

A SANADIN KAMA

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 3️⃣3️⃣↪️3️⃣4️⃣

Daƙyar ta ce "Baba ni a gaskiya gani na ke kamar idan ban auri Bassam ba na yaudare shi kuma gaskiya ni...." Maganar ce ta laƙe a kasan maƙogwaronta ganin a gaban iyayenta ta ke.

Baba ya tari numfashinta da cewa "Ai dama tun farko ba mu mai alƙawarin cewa za mu ba shi ba, kuma ba mu ƙarbi komai nasa ba, don haka ba yaudara, zan kira sa na bashi haƙuri."

Ɗago kai ta yi zuciyarta na rawa ta ce "Amma Baba gaskiya ni fa kallon yaya na ke yiwa yaya Sameer ba zan iya aurarsa."

Mama ce ta cafe zancen da cewa "Yaro man kaza, idan bakya sonsa yanzu, a hankali idan kuna tare za ki so shi amma da kunya, mu gayawa Alhaji cewar ba za ki auri dansa ba, don haka ki haƙura kawai."

Hawaye mai zafi ne ya fara bin kuncinta ganin ana neman raba ta da mutum da ta shaqu dashi sama da kowa, kuma mutumin da ta shafe shekara biyu wutar ƙaunarsa na ruruwa a ranta, gaskiya ba za ta iya ba.

Ta na ganin za ta ajiye kunyar nan kawai ta fito musu da abinda ke ranta.

Gyara zamanta ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce "Baba, Mama ku yi haƙuri ka da ku ce na maku rashin kunya, Amma gaskiya Ni dai Bassam na ke so shi kaɗai zan iya....."

Mama ce ta katse mata zance yayin da ta ke cewa "La'ilaha ilallah! Malam ka ga yaran zamani koh?" Ta faɗa ta na tafa hannu tare da kallon baba.

Numfashi ya ja "hmmmm" sannan ya kalli Mimie ya ce "Zuhra! Ɗago idonki ki kalleni."

Ba musu ta ɗago madai-daitan idanuwanta masu haske ta zuba mi shi su.
Ya ce "Zuhra kin sani cewa mu iyayenki ne, mu muka haife ki muka sha ɗawainiyar rainonki tun kina jinjina har kawo yanzu da ki ka zama budurwa, kin sani cewa ba yadda za'a yi mu zaɓa maki abinda zai cutar da ke saboda muna sonki sosai."

Ɗan tsagaitawa ya yi yana kallonta don ya ga ya ta ƙarbi zancen.

Sai dai ita tuni ta sunkuyar da kanta ƙasa hawaye na cigaba da yin sintiri a kumatunta.

Bai damu da hakan ba ya ci gaba da cewa "Sau tari Kakan so abu ya kasance ba alkhairi bane a gareka, ko ka ƙi Abu ya kasance shine alkhairi a gareka, shiyasa ake so duk lokacin da mutum zai yi wani abu makamancin wannan to ya yi istikhara ya mayar da lamarinsa ga Ubangiji. Don haka a matsayina na mahaifinki ina mai ba ki shawara da ki auri Sameer ko don karamcin iyayensa a garemu, idan ki kai mana haka zamu ji daɗi sosai ni da mahaifiyarki kuma kin mana biyayya, amma zaɓi ya rage na ki ba zan maki auren dole ba."

Ya na kai nan ya yi shiru alamar ya kawo ƙarshen zancensa.

Tun lokacin da ya fara maganar ta ke jin kanta ya na mata masifar ciwo kamar zai fashe, kalamansa sun matuƙar gigita ta da bata mamaki har ta fara zargin iyayen nata kodai...?

Don haka ko da ya kai ƙarshen zancensa miƙewa kawai ta yi tare da dafe kanta ta fashe da matsanancin kuka yayin da ta ke barin gun ta na faɗar "Ni dai wallahi uncle Bassam na ke so, za ku iya rasa ni idan....." Bata ƙarasa zancen ba sakamakon kukan da ya ci ƙarfinta.

Da mamaki iyayen nata ke Binta da kallo abun na ba su mamaki da tsoro ace wai y'arsu ce a gabansu ta na gaya masu haka? Yarinyar su mai matuƙar kunya, ladabi da biyayya ita ce yau ta ke faɗa masu haka a gabansu?
Tabbas akwai aiki ja a gabansu.

®®®®®®®®

Ita kuwa bayan shigewar ta taƙinta anan ƙasan tiles ta sulale ta na kuka mai cin rai, "Meyasa su Baba za su yi mana haka? Anyah! Sun ɗauko hanyar adalci kuwa? Meyasa su ke son rabani da Bassam bayan su da kansu su ka ba mu damar zama masoya? Da ba su yarda za su basa ba ai da ban faɗa tarkon sonsa harna shaƙu da shi haka ba? Sai yanzu da na kai ƙoluluwa a kan bishiyar ƙaunarsa za su nemi yado ni ƙasa? Wannan abun ba zai taɓa yiwuwa ba wallahi, ba zan yi biyayya wa wannan maganar ba, indai akan Sameer ne na san yanda zan yi."

Ta na kai nan a tunanin zucinta ta rarrafa ta janyo wayarta da ke kan bedside drower ta shiga neman layin Sameer don yau so ta ke ayi ta ta ƙare domin ba zata taɓa saɓuwa ba bindiga a ruwa.

Har ta ƙaraci burarinta bai ɗaga ba, nan fa ta ƙara ƙuluwa a bayyane ta ce "aikin banza wai a hakan ka ke so a baka ni, bayan ka kasa kula da wayarka ma bare ni. Su ƴaƴan ma su kuɗin nan me su ka ɗauki kansu ne?"

Ta na cikin wannan mitar ne sai ga shi ya biyo kiran, ɗagawa ta yi a gadarance ko sallamarsa ba ta tsaya amsawa ba ta ce .......

Ku yi haƙuri da wannan kun san daga tafiya na ke so agajiye na ki wallahi shiyasa, don kawai na ga shirun ya yi yawa na ce bari na maku.

Follow me on wattpad @ummu inteesar

UMMU INTEESAR CE❤️💔💛💔❤️

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*A SANADIN KAMA*

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*DAGA ALƘALAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*

*DA KUMA*

A SANADIN KAMA

WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE DON ALLAH IDAN KA SAN BAKA BIYA BA KADA KA KARANTA MUN.

IDAN MA KA BIYA DON GIRMAN ALLAH KADA KA FITARMIN DA SHI DOMIN KUƊIN KARATU KA BIYA HAƘƘIN MALAKA NAWA NE

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

*BISMILLAH RAHMANIR-RAHIM*

Page 3️⃣5️⃣↪️3️⃣6️⃣

Ta ce "Don girman Allah Sameer ka yi haƙuri ka janye maganar aurena da ka ke so ka yi, tun kafin haɗuwata da kai an tsayar mun da miji amma soyayyarka ta na neman zame mana Barazana a rayuwar soyayyarmu..."

Saurin dakatar da maganar ta ta yi gudun ka da ta yi kwaɓa.

Sameer kuwa tsikar jikinsa ce ta fara tashi, hankalinsa ya dugunzuma ba ki na kakkarwa ya ce "Ke ma don girman Allah ki yi haƙuri Sweety wallahi ba zan iya rayuwa ba ki ba, ban san cewa kina da wanda ki ke so ba, da na yi yunƙurin hana zuciyata faɗawa tarkon soyayyarki, amma yanzu ba ni da zaɓi da ya wuce aurenki ina matuƙar sonki ba zan iya rayuwa ba ki ba."

"Nima haka Sameer ba zan iya rayuwa ba Bassam ba soyayyarsa a gare ni bata da iyaka, ko da na aure ka ba zan iya kallon ka a matsayin miji ba, sai dai yaya don haka ya na da wuya na iya maka biyayyar aure, ka ga kuwa zan rayu cikin halaka ne don Allah ka yi haƙuri ka sanar da Daddy ka janye."

Jikinsa ne ya soma kakkarwa bakinsa na ɓari zuciyarsa cike da damuwa ya ce "Sweety Wallahi ina son ki ban san yaushe na kamu ba, amma na sani cewa idan ki ka guje ni rayuwata za ta zama mara amfani, idan ma na rayun kenan, amma ba damuwa idan haka ne zai sakaki farin ciki zan yi ƙoƙarin aikatawa, domin ki rayu cikin farin ciki zan iya haƙura da nawa farin cikin"

Daga haka ya kashe wayar zuciyarsa cike da ƙunci ya zube kan tiles tare da dafe saitin zuciyarsa.

®®®®®®®®®®®
Chapter 15 · 0% Book details