← Book details A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 36

Sashe 30

A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi kawai Sameer ya yi bai kuma cewa komai ba, ya juya ya cigaba da kallon gabansa, domin ya fahimci y'an uwan nasa su na so su saka masa rai ne da samun abinda zai yi wuyar samu a gare shi.

Lokacin da ya ke saurayi mai ji da kyau da ƙuruciya ga Naira ma ba ta so shi ba, sai yanzu da duk ya yamutse kuma ya ƙara shekaru?

A haka ya ci gaba da saƙe-saƙensa har suka ƙarasa gida.

Rashin Mamy a gidan ya saka Sameer ya ji gidan ya yi wani iri, amma duk da haka ya ji daɗi sosai da ya dawo ya riski ɗan ɗan uwansa kuma takwaransa, wato Sameer ƙarami ɗan Ruma da Saheen."

Kasancewar Sameer Ya na matuƙar son yara hakan yasa kullum Sam ƙarami ɗan 3months ya na cinyarsa ya na wasa da shi.

Ko da Mamy ta dawo Abuja ta sami Sameer a gidan, sosai ta ji daɗin ganin yanda ya samu nutsuwa kuma da alama ya shiryu ya daina halayyarsa ta baya wato shan giya.

©©©©©©®®®
Har zuwa lokacin Mommy bata bar Saheen ya huta ba, kullum ta na cikin ƙwaƙule masa aljihu, ga shi tun da ya auro Ruma ku san kullum ta na gidan, kasancewar Abbansu Ruma ba mazauni ba ne, kullum ya na hanyar wani gari ko wata ƙasa don kasuwancinsa.

Duk wannan abun Saheen ba ya ganin aibun Mommyn kuma duk abinda take so shi a ke yi, da yake dai aikin asiri ne shiyasa.

Sosai a bun ke damun Ruma yanda mahaifiyar tata ke takura masu, amma ba yanda ta iya dole ta yi haƙuri, domin dai duk yanda ta lalace ita ce dai mahaifiyarta kuma bata da madadinta a duniya.

A haka ta cigaba da haƙuri da halayen mahaifiyar tata, kullum ta na roƙa mata shiriya a gurin Allah.

©©®®®©©©©

Mimie ta zazzaga dangi na uwa da uba da kuma gidan yayyenta duk ta kai masu ziyara, ba wanda bai yi murnar ganinta ba, ga twins Allah ya zuba masu farin jini duk inda ta je kamar alashe su saboda ƙaunar da a ke nuna masu.

Bayan wata ɗaya da zuwan Mimie Kano, hankalinta ya kwanta ta murmure jikinta ya yi kyau, haka ma Affan da Afeef sun yi kyau abinsu.

A ranar da suka cika Wata uku a duniya, Mimie ta shirya ta je Abuja gidan Daddynta don kai masu ziyara.

Murna a gun iyalan gidan ba a magana, Ba ma kamar Sameer da yake jin kamar ya haɗiye ta ita da jariranta saboda ƙauna.

Ruma ma ta yi matuƙar farinciki da zuwa y'ar uwar tata a karo na farko bayan aurenta.

Nan fa suka shiga murnar ganin junansu.

Ita kuwa Mimie kunyar yaya Sameer take ji sosai, shiyasa muddin ta ji motsinsa a falo ba ta fitowa sai ya bar gun.

Lura da hakan ya saka wata rana Yaya Sameer ya rutsa ta a ɗakinta dake gidan.

Ta ɗan tsorata da ganinsa, su na haɗa ido ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na wasa da hannun Afeef dake kwance kusa da ita a kan gadon.

Matsowa ya yi ya na murmushi ya ce "Mimienmu sannu da zuwa."

Shiru ta yi bata ce komai ba.

Faɗaɗa murmushinsa ya yi ya ce "Da ma na zo ne na miki sannu da zuwa, tun da na ga alamar kunyar yayan naki kike ji."

Ita dai ba baki sai kunne kuma har lokacin bata ɗago ba.

Sunkuyowa ya yi ya ɗauki Affan dake kwance ya na wasarsa, ya ɗaga shi sama ya na murmushi ya ce "To ni bari na je, dama ina son ganin ƴaƴana ne, kuma kin ɓoye man su a ɗaki kin ga ko dole kenan na biyo sahu."

Daga haka ya nufi ƙofar fita riƙe da yaron a hannunsa, ya na faɗar "Idan kin gama jin kunyar ki sanar da ni akwai maganar da na ke so muyi.."

Ƙirjinta ne ya fara bugawa da ɗan ƙarfi, a ranta ta ce "Na shiga uku, me kuma zai faɗa yanzun?...."

Follow me on Wattpad @ummu inteesar

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*A SANADIN KAMA*

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*

DA KUMA
*A SANADIN KAMA*

WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL

GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202

DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

Page 6️⃣9️⃣↪️7️⃣0️⃣

Haka ta ci gaba da tuna abinda ta yiwa yaya Sameer a baya har tsawon wani lokaci kafin ta tashi daga gun.

@@@@##

Bayan sati biyu da zuwan ta Abuja, wata rana da misalin ƙarfe goma na safe Sameer ya sauko daga sama ya same ta a falo ita kaɗai sai waya riƙe a hannun ta na karatun wani novel mai suna cikin waye? na marubuciya Fatima sunusi Rabi'u (Ummu Affan) sai share hawaye take kasancewar jarumar littafin ta bata tausayi matuƙa.

Matsowa ya yi daf da ita ya tsaya, ya yi kusan minti biyar tsaye a kanta ya na kallonta, amma bata ko san yana yi ba,saboda ta yi nisa a karatunta.

Da ya ga alamar idan bai yi magana ba ba za ta san da tsayuwarsa agun ba, ya saka ya tafa hannayensa guda biyu.

Firgigit ta yi ta kalle shi a ɗan razane domin bata ji isowarsa gun ba.
"Kukan na mene sweet sis?" Ya tambaya.

Share hawayenta ta yi ta ce "Ba komai Bro, jarumar littafin ce kawai ta ban tausayi."

Guri ya nema ya zauna a lokacin da yake faɗar "Da ma sistern tawa ta na da tausayi, amma ta kasa tausayawa yayanta a lokacin da yake tsananin buƙatar hakan?"

Sunkuyar da kai ta yi wani hawayen na gangarowa yayin da shi kuma yake kallonta ta ce "Ka yi haƙuri yaya a wancan karon soyayya ce ta rufe min ido na kasa hango girman kuskuren dake cikin abinda na aikata, haƙiƙa na maku butulci, amma insha'allah wannan karon a shirye nake da aikata duk abinda zai gyara kuskurena na baya."

Wani sanyi ya ji a ransa, ya na ganin lokaci ya yi da zai shigar da buƙatar a karo na biyu.

Wani lallausan murmushi ya yi ya ce "Ki share hawayenki sister ni na yafe miki, kuma a yanzun ma za ki iya gyara kuskurenki idan kin so."

Da sauri ta ce "gaya min abinda zan yi don tabbatar da hakan."

Ƙara murmusawa ya yi sannan ya ce "Za ki gyara shi ne ta hanyar karɓar soyayyata a karo na biyu, za ki gyara shi ne ta hanyar yarda da ni a matsayin mijinki na sunna.."

Sai da gabanta ya faɗi da ta ji kalamansa, amma bata fatar ta kuma aikata wani kuskure a karo na biyu, saboda haka ta ce "Ashirye na ke da gyara kuskure na, don haka na yi maka alƙawarin zan wanke maka dauɗaɗɗiyar zuciyarka da na yi silar ɓatawa da ruwan zallar soyayya, zan shafe maka ita da ƙyallen ƙauna domin dawo da ita a asalin yanda take kafin na gurɓata ta."

Ba ƙaramin farinciki Sameer ya ji ba, ya ma kasa magana sai bakinsa dake rawa daƙyar ya buɗi baki ya ce "Alhamdulillah!"

A yau wani irin farinciki yake ji wanda rabonsa da jin makamancinsa tun kafin shekara biyar da suka gabata.

Gyara zama kawai ya yi a gun yana ta kallon ta, har ta ji ta tsargu ta tashi ta gudu zuwa ɗaki.

Sai ranar ne kuma Sameer ya gabatar mata da tsarabarsa da ya yo masu a saudia ita da yaran.

A wannan ranar Sameer bai kwanta ba sai da ya shaidawa Daddy halin da a ke ciki, shima Daddy a ranar ya samu Mimie a ɗaki ya tambaye ta, ta tabbatar masa da hakan, ya yi farin ciki matuƙa don haka a ka yanke cewar da ta gama iddarta za a sanar da iyayenta sai a yi maganar auren.

Bayan wata biyu da rabi Mimie ta kammala iddarta, a ranar kuma ta juya zuwa Kano, tun kan ta isa kanon Daddy ya kira Baba ya shaida masa halin da a ke ciki, shi ma Baba ya yi murna sosai ya na ta sakawa Mimie Albarka.

Bayan sati ɗaya a ka biya sadaki da komai na aure a ka saka rana nan da sati uku masu zuwa.

A cikin satin farko a ka kawo lefen Mimie a Kano, lefe ne na gani na faɗa akwati goma sha biyar Sameer ya danƙaro mata, irin wanda ko a aurenta na fari bata samu irinsa ba.

Mutane sun yi ta al'ajabin wannan abun,
Ita kanta Mimie ta yi mamakin irin wannan kayan duk da ta san akwai abun yin fiye da haka, amma sai da ta kira Sameer ta na tambayarsa "Yaya miye haka?"

Ya ce "name fa?"

"Irin wannan kayan haka sai kace za ka auri wata budurwa?." Ta tambaya.

Murmushi yayi mai sauti ya ce "Sweetyna ai kin fi wata budurwar a gurina, matsayinki baya da misali, shiyasa ma na yi zaman jiranki har zuwa wannan lokaci."

Da alamun mamaki a fuskarta ta ce "To yanzu da ƙaddara bata ɗauke Uncle Bassam ba sai ka yi yaya kenan?"

"Da a haka zan cigaba da zama har zuwa lokacin da tawa mutuwar za ta riske ni, domin ba zan iya rayuwa da ko wacce 'ya mace ba bayan ke."

Jinjina kai kawai ta yi bata ce komai ba.

A haka suka cigaba da hirar har zuwa lokacin da suka kashe wayar.

©©©©©©

A bangaren ango shirye-shirye suke sosai, domin wannan shi ne karo na farko da za su aurar da babban ɗansu, bugu da ƙari kuma auren za a yi ne da 'yar lelensu, don haka dole a yi biki mai ƙayatarwa.

Ranar da ya rage saura kwana biyar bikin, wasu daga cikin dangin Mamy da Daddy na kaduna suka je Abuja don taya murnar wannan auren.

Bangaren Mimie ta ce ita ba wani shagali da za ta yi saboda ita a yanzu ba budurwa ba ce.

Jin hakan ya saka Mamy ta turo wasu daga cikin 'yan uwanta zuwa Kano a ka ɗauki Amarya zuwa Abuja don gudanar da shahararren shagalin da suka shirya a can.
Chapter 30 · 0% Book details