Sashe 8
A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira N200 kacal.
Ga mai buƙata sai ya neme Ni ta whatsapp numberna👇🏼
_08109634202_
Domin na maku bayanin yanda za ku biya.
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYU KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL.
________________________
________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Free Page 1️⃣9️⃣↪️2️⃣0️⃣
Bayan ya gama bayanin ne Mommy ta ɗora da bayanin kanta da matsayin Zuhra a gunta ta ce "Ni sunana Khadija musa, ni ƙanwar mahaifiyar Zuhra ce uwa ɗaya Uba ɗaya, nice na ke bin Yaya A'isha,ina da yara guda uku, wannan ita ce y'ar Autata Rumaisa'u, sauran bayanin kuwa nasan Zuhra zata maku acikin zaman da zata yi anan."
Da haka aka kammala jawaban, Mommy ta miƙe ta na faɗar "Ruma tashi mu tafi, Hajiya sai watarana saduwar alkhairi."
Har Ruma ta miƙe ta kamo hannunta ta riƙe gam ta na faɗar "Mommy don Allah ki barmun y'ar uwata anan idan har ki na so nima na zauna, idan ba haka ba sai dai mu tafi tare."
Jin wannan zancen ne ya saka cikin sauri Mamy ta ce "Me ya yi zafi haka Mimiena, ki yi haƙuri zata ta yaki zaman ko da ace ba zata yi hakan ba sai an biyata kuɗi to ina mai tabbatar miki da cewa ko nawa e zamu iya sadaukarwa saboda farin cikinki."
Juyawa ta yi ta kalli Mommy ta ce "Ina neman alfarma ta biyu, don Allah ki taimaka ki bar Ruma anan su zauna tare zata fin jin daɗin zama tunda ga y'ar uwarta anan zata fi sakewa."
Shiru ta yi na yan wasu daƙiƙu kamar mai tsoron wani abu .
Mamy ce ta kuma cewa ki yarda damu Hajiya ba zamu cutar da yaranki ba, mu ba macuta bane hasalima soyayyar da muke yiwa y'ar mu Mimie ba zata bari mu iya cutar da duk wani mutum makusancinta bare wacce ta ke tamkar ita."
Dogon numfashi Mommy ta sauke kana ta ce "Hmmmm! Ba fa haka nake nufi ba Hajiya, kawai ina tunanin idan na barsu su biyun anan ni wa zai ɗebe man kewa agida Ni kaɗai tamkar mayya."
"Ki dai ƙara haƙuri Hajiya." Ta faɗa ta na juyawa zuwa cikin Bedroom ɗin ta can bayan wasu mintuna sai gata ta fito hannunta riƙe da wasu zungura-zunguran ledoji guda biyu ta miƙa hajiyar ta na faɗar "Ga wannan Hajiya ki gaida gida mungode sosai Allah ya bar zumunci."
Shima Alhajin hannu ya saka a aljihu ya ciro bandir na ɗari biyar-biyar guda biyu ya miƙa mata, ba musu ta karɓa ta na ta zabga godiya ga wani lallausan murmushi kwance a fuskarta, aka saka driver ya maida ta gida.
®®®®®®®®®®®
A mota ta ke ta zancen zuci ita kaɗai ta na faɗar "Kai Alhamdulillah, gaskiya wannan yarinyar Zuhra Allah ya zuba mata farin jini ga shi tun zuwan ta sai alkhairai na ke ta samu, Haka Musaddiq ya ta kawo mana abun arziƙi saboda ya na sonta, ita kuma ta ƙi fahimta, yanzu kuma ga alhajin nan da alama za'a shana, ko ni da ba don kada su ga rashin hankalina ba, ai da ni za'a yi kwana biyun na more, na gode Allah ma da Zuhra ta buƙaci zaman Ruma a tare da ita ko ta nan na rage zafi tunda y'ata zata moru."
Sauke ajiyar zuciya ta yi ta cigaba da zancen zucinta "Ga shi yarinyar nan ta kusa tafiya bai fi saura kwana biyar ba ta koma Kano, inama-inama ace Ruma ce ta samu wannan gatan tabbas da na fantama nima, amma yanzu ta ya zan iya hana Zuhra komawa gida tunda acan ta ke karatunta?, Kuma tabbas idan ta koma duka wannan kulawar da arziƙin da na ke samu a dalilinta kan iyayenta zai koma."
A haka ta wanzu ta na ta tunani kala-kala har drivern ya sauke ta a gida ta shiga.
®®®®®®®®®®
Su Zuhra kuwa ana nan baje a falo, sai hira mutanen gidan ke mata amma har zuwa lokacin bata sake jiki da su ba, sai Ruma ce ta ke tamkasu, gata kam sun sha shi, ko motsi su ka yi sai ɗaya daga cikin mutan gida ya matso don jin ko lafiya.
A ranar dai yara mazan gidan ba inda su ka tafi duka su na falon ana hira sun tasa ta a tsakiya har wuraren 11:00pm na dare, kowa idon shi na kanta musamman yaya Sameer da ko kyaftawa ba ya yi ya na jin ƙaunarta har cikin jinin jikinsa.
Fara mitsittsika ido ta yi alamun ta fara jin barci, yayin da Ruma ta fara gyangyaɗi, su ko mutan gidan ba su da niyyar tashi, tuni Sagir ya yi barci a cinyar Mamy.
Ganin haka ya saka Mamy ta kalle samarin na ta ta ce "Ku tashi ku je ku kwanta dare ya yi kun ga ƙanwarku ta fara mitsitsika ido."
Miƙewa su ka yi a tare dama sun fara jin Alamun barci Saheen da Samar su ka haɗa baki gurin cewa "Good night Mamy& Daddy." Su ka haura sama zuwa ɗakunansu, Shi ma Salim miƙewa ya yi ya bi bayan su, Sameer ne kaɗai ba ya da niyyar tashi agun.
Mamy ta kalle shi yayin da ta ke ƙoƙarin tada su Zuhra su je su kwanta, ta ce "Kai ba ka jin barcin ne ka tsaya a nan?."
Sosa ƙeya ya yi sannan ya ce "Uhmm! Dama zan tashi ne ina jira ne Lovely sis ta farka na mata sai da safe sannan na tafi."
Murmushi kawai Mamy ta yi ta lura cewa Sameer duk ya fi su zaƙewa gurin nuna soyayyarsa wa sabuwar Mimiensu.
Tada su ta yi a hankali Ruma ta buɗe idonta yayin da Zuhra har ta miƙe tsaye kasancewar lokacin ne barcin ya fara surarta bai yi nisa ba.
Kallonta Sameer ya yi ya ce "Good night lovely sis."
Daƙyar ta iya buɗar ba ki ta ce "Good night." tsabar barci da ke idonta.
A haka su ka watse kowa ya nufi sashensa, Mamy ta raka su ɗakin da ta saka aka gyara masu...
®®®®®®®®®
Shi kaɗai ne kwance a ɗakinsa kan makeken gadonsa, amma barcin ya ƙi ya ɗauke sa, da ya rufe idonsa ita ya ke gani tana gifta masa fuskarta ɗauke da murmushin da ke ƙara ruɗar da shi, sai juyi ya ke ya rasa yanda zai haƙiƙa so ya masa Shigar sauri, domin abinda ya ke ji akanta ya tsarce soyayyar yan uwantaka, sai dai soyayyar aure, domin a lokacin da Real Mimie ta ke raye ba ya jin irin wannan feelings ɗin akanta......
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na masa ƙarin bayanin yanda zai biya.
Ka da ku manta N200 ne kacal.
Follow me on Wattpad@ ummu inteesar.
Vote, share & Comment.
UMMU INTEESAR CE❤️💛💚💙💔💚
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal, ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na masa bayanin yanda zai biya.
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL.

Free Page 2️⃣1️⃣↪️2️⃣2️⃣
A haka Sameer ya kwana cike da mafarki iri-iri akan Zuhra.
Washe gari da tun da safe ma su aiki su ka kammala komai na break fast su ka gyaggyara guri kamar dai yanda aka saba.
Mamy ce ta fito Sanye da wa su kayan barci riga da wando ma su kyau da tsadar gaske, cikin hanzari ma'aikatan su ka zube a gabanta su na kwasar Gaisuwa.
Fuskarta cike da fara'a ta amsa ma su tare da kallon biyu daga cikinsu ta ce "Fariha da ke da Maryam ku je ɗakin Mimie ku kai mata break fast ɗinta acan, sa'annan bayan sun tashi ku gyara ɗakin, daga yau ku ne ma su hidimarta har zuwa lokacin da zata tafi kun ji koh?"
Waɗanda aka ambata da waɗannan sunayen su ka ɗaga kai sama alamar gamsuwa su ka ce "Insha'allah Hajiya za'a yi yanda ki ka ce mun gode sosai."
Cike da zumuɗi su ka miƙe za su nufin ɗakinta, domin sun tabbatar kakarsu ta yanke saka tun da aka mayar da su ma su kula da y'ar gatan gidan sun san za su fantama, albashinsu ma ninkuwa zai yi.
Har sun fara tafiya Hajiya ta dakatar da su da cewa "Ku dakata."
Tsayawa su ka yi cak, tare da juyowa su na jiran umurni.
"Idan ku ka same ta bata tashi daga barci ba kada a tayar da ita ba na so a takuramin yarinya, ku tabbatar kun faranta mata ta hanyar yin duk abinda ta umurce ku da yin abunda ta ke so."
Ɗaga kai su ka yi alamar gamsuwa su ka ce "insha'allah, wannan shi ne aikinmu." juyawa su ka yi su ka nufi cikin, yayin da Hajiya ta juyo ga sauran ta ce "Ku duka kowa ta san aikinta ba sai na jaddada ma ku ba, abu ɗaya na ke so ku sani shi ne kun dai ga ga y'armu Mimie Allah ya dawo mana da ita a karo na biyu, ku tabbatar ba ku yi abun da zai baƙanta mata rai ba, domin idan haka ta faru kun san kwanan zancen ba sai na gaya ma ku ba, ku tashi ku tafi."
Miƙewa su ka yi jiki a saɓule su ka fice kowaccensu a ranta ta yi fatar ace ita ce mai kula da Mimie.
®®®®®®®®®®
A cikin ɗakin kuwa Zuhra ce ta fara farkawa da misalin ƙarfe bakwai da rabi na safe, dama ita bata fiye nauyin barci ba, kuma da lokacin Sallah ya yi komai barcin da ta ke za ta tashi ta yi, mussanman sallar asuba bata taɓa wuce ta ba, bayan ta gama ne ta koma barci shi ne sai yanzun ta farka.