← Book details A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 36

Sashe 25

A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rarrashinta ya shiga yi kafin daga bisa ni ta ce "Komai ya faru dake ke ki ka ja Mimie, da kin karɓi zaɓin mahaifanki ina da yaƙinin da baki shiga wannan tashin hankalin ba, amma ba damuwa zan dinga taya ki da addu'a, ke dai abinda na ke so dake ki ci gaba da haƙuri kuma ki nemi yafiyar iyayenki akan saɓa musu da kika yi."

A haka suka cigaba da tattauna matsalar ta na bata shawarori har tsawon wani lokaci kafin su katse kiran.

®®®®®®®®®®
Bayan kamar rabin shekara da tarewar ta gidan abubuwan su ka ƙara tsananta a gare ta domin yanzu Uncle har zagin ta ya ke tas, kuma baya ganin laifin y'an uwansa akan duk wulaƙanci da suke mata.

A bangaren Sameer ma ya na can cikin wani mawuyacin hali mai wuyar fassarawa, kuma ya ci gaba da shaye-shayensa ba tare da sanin iyayensa ba, Allah dai ya kare duk abinda ya ke baya neman matan banza.

DAWOWA DAGA LABARI

Bayan komawar Innarmu ɗakinta, ya ci gaba da rarrashin matarsa har ta ware, to kun san tsakanin mata da miji sai Allah, nan da nan ta sauko su ka dawo kamar ba abunda ya faru.

Da ya ga hankalinta ya kwanta ne ya shirya ya fita, ya bar ta anan ta na tunanin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki.

Ita yanzu ga baki ɗaya auren ya fice a ranta, ba wai don ba ta son mijinta ba sai don damuwar da take ciki, tunawa da ta yi cewa aure ibada ne kuma zaman bautar Allah take da neman aljannarta a gidan, hakan ya sa ta haƙura ta cigaba da daurewa.

Idan ta je makaranta ne ma take samun sassauci domin a can ne za ta haɗu da course mate ɗinta ai ta taɗi ana dariya, amma tana dawowa gida shi kenan ƙuncinta zai dawo.

Akwai wata course mate ɗinta (Samiha) da suka shaƙu sosai ita ce ta lura da yanayin damuwar da ƙawar tata ke ciki, ta taya ta jimami kuma ta ba ta shawarwari gwargwadon yanda za ta iya, haka ta cigaba da takatsan-tsan a zaman gidan don ma tana da juriya sosai.

®®®®®®®®®®
Lokaci ya sha kwanaki sun shuɗe bayan shekaru biyu, zaune take a ɗakinta abin duniya ya dame ta gorin haihuwa kawai ake mata, Innarmu faɗar ta ke Mimie ta ƙi yarda ta haihu ne saboda karatunta da yabawa muhimmanci akan komai.

A haka ta duƙufa da addu'a kullum dare ta na kai kukanta a gurin mahaliccin bayi ta na neman sassauci da mafita a gunsa.

Kallo ɗaya za ka mata ka ɗauke kai domin duk ta ya mutse ta lalace abinka da zaman ƙauye ga kuma uban aiki da take sha ba hutu.

A shekarar da ta gabata Mamy da Daddy sun zo don duba lafiyar y'arsu, yanda su ka same ta ba ƙaramin ɗaga musu hankali ya yi ba, a haka su ka koma su ka bar ta a gidan mijinta don ba yanda za su yi, amma Mamy ta sha kuka, ko da suka koma Abuja ma hankalinta bai kwanta ba, saboda haka ta duƙufa da yiwa Mimie addu'a, domin ta na jin soyayyar yarinyar har cikin jininta.

Shima Daddy ya saka malam ana ta yiwa Mimiensa addu'a da roƙon Allah a kan ya kawo mata sauƙi a cikin rayuwarta, domin duk da ba ta faɗa masu komai ba, a yanayin da suka ganta ma ya isa shaidar cewa ta na cikin tasku.

®®®®™™™

Bayan dawowarsu daga Birnin Kebbi ne Daddy da Mamy suka shirya don zuwa dubo Sameer, saboda tun lokacin da ya tafi hankalinsa Daddy ya ƙi kwanciya, ga shi har ya gama masters ɗinsa shekara uku amma ya ƙi ya dawo gida sai ya cigaba da zamansa a Dubai, inda Daddy ya yi-ya yi ya faɗa masa dalilin hakan amma ya ƙi sai cewa da ya yi, ya ji daɗin zaman ƙasar ne shiyasa.

Wannan dalilin yasa suka shirya yi masa zuwan bazata, dama already sun san ya na Abu-Dhabi kuma sun san address ɗin gidan don haka su na sauka kai tsaye suka wuce can ba tare da saninsa ba.

Abin da su ka tarar ya matuƙar ɗaga masu hankali, wani irin shork ne ya kama su to yaushe rayuwar ɗan na su ta gurɓace haka ba su sani ba?

Ƙarasawa su ka yi cikin falon kai tsaye, idanun Daddy su ka ƙanƙance, cike da masifa ya dubi su Zaroon da ke zaune rungume da y'an matansu su na aikata masha'arsu tare da shan barasa, ya daka masu tsawa tare da Faɗar "Get out from here nonsenses."

Su kuwa kamar ba da su ya ke magana ba don ko kallonsa ba sa yi, abinda su ka saka agaba kawai suke yi.

Ran Rajbir ne ya yi mugun ɓaci ya buɗi bakinsa ya ce "Who Are you?, Kai wanene da za ka zo ka na yiwa mutane shouting aka?"

Sameer da ke gefe riƙe da kwalbar barasa ya na sha, shi ne ya taso ya na layi irin na y'an maye ya ce "Your highly welcome my Dad, Mamy i miss You alot." Cikin Muryar mashaya ya ke zancen har ya ƙara so gun su, Daddy ne ya kife shi da wani wawwan mari, luuu ya yi ya faɗa jikin Mamy sharaf, ya na mashalo Mamy kuwa sai hawaye take wani na korar wani, tsananin tausayin ɗan nata ne ke ratsa ta, a haka ta riƙe shi gam! Sai hawaye ya ke.

Daddyn ne ya juya ya fatattaki su Rajbir da y'an matansu su ka bar gidan ya na ja masu Allah ya isa tare da yi masu gargaɗi akan kada su sake shiga rayuwar ɗansa.

A buge su ka bar gidan ba arziƙi, ya juyo ga Sameer ya ce ".......

Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number
08109634202

Follow me on wattpad@ummu inteesar

UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*A SANADIN KAMA*

👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻

*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*

DA KUMA
*A SANADIN KAMA*

WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL

GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202

DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

Page 5️⃣9️⃣↪️6️⃣0️⃣

Ya ce "Sameer yaushe ka lalace haka?, Wannan ita ce tarbiyyar da muka baka? Ka ban kunya Sameer! Ka ban kunya!!"

Ya na gama faɗa ya zauna shirim kan kujerar falon ya na share gumi da handkerchief ɗin da ya ciro a aljihunsa, sai maimaita kalmar "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un ya ke."

Mamy kuwa ƙara rungume ɗan nata ta yi sosai a jikinta tare da neman guri ta zauna shima ta zaunar da shi, ta saka hannunta ta na share ƙwallar dake idonta.

Shiru ya ratsa na ɗan lokaci baka jin komai sai sanyin a.c haɗe da warin giya dake tashi a ɗakin.

Can Sameer ya zabura da ƙarfi ya miƙe ya na dube-dube har ya kai ƙofar falon ya leƙa waje, sannan ya dawo ya na tangaɗi cikin Muryar maye ya ce "Mamy ina ku ka baro mun ita? Ta ƙi ta shigo ciki, ki ce ta shigo in gan ta ko na ji sauƙi."

Shiru ba wanda ya tamkasa duk sun yi jugum-jugum dasu.

Dawowa ya yi kusa da Mamyn ya zauna ya na kuka kamar wani ƙaramin yaro, acikin kukan ya ke cewa "Mamy ku gayawa y'arku Allah ina son ta, idan ban aure ta ba zan iya mut..tuwa ma, kawai ku aura min ita zan daina abunda nake na rantse."

Ya na gama zancen ya langaɓar dakai kan cinyar Mamynsa, kai daga ganin yanayinsa ba sai anga yama a buge yake ba.

Daddy ne ya miƙe ya je pridge ya ɗauko gwangwani madara ya hude, ɗaga bakin Sameer ɗin ya yi ya tsiyaye masa, ba musu ya shanye ta tas.

Shanyewarsa ke da wuya barci ya yi awon gaba da shi.

Ɗora shi suka yi akan three-sitter sa'annan suka gyara masa kwanciyarsa, Mamy ta miƙe jiki a saɓule ta shiga gyaran falon da ya yi dagaja-dagaja da datti yayin da Daddy ya fita harabar gidan cike da damuwa.

Bayan dawowarsa cikin hayyacinsa ne suka saka shi gaba da faɗa, su na yi masa nasiha a kan rayuwa tare da tsorartar da shi daga azabar Allah.

Cikin kuka ya ke ba su haƙuri tare da jaddada masu cewa shima ba laifinsa bane damuwa ce ta masa yawa da kuma zugar mugayen abokanansa da suka ɗora shi a kan hanyar da bata ɓullewa.

To dama an ce tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah, nan take suka yafe masa tare da jaddada masa ba za su bar shi a nan ba, domin idan su ka bar shi ba susan wane hali zai shiga ba, bayan shaye-shaye da neman mata da yake.

Anan ya rantse masu a kan baya neman mata shaye-shayen ma ƙaddara ce ta saka.

©©©©©©©™™™™

Mimie na cikin wannan halin ne, Cikin iyawar Allah wata rana sai ta tashi da laulayi sai amaye-amaye take, komai ta ci sai ya dawo mata, nan take Innarmu ta fahimci ciki ne da ita.

A can cikin zuciyarta ta na farin ciki za ta samu jika amma a fili sai ta nuna rashin damuwa, domin zahiri soyayyar Zinnira ta mamaye zuciyar Innarmu(ko da yake aikin asiri ne) da yake shekara ɗaya baya kenan da Bassam ya auri Zinnira sai dai ba'a ƙauyen take zaune ba, ta na birni gidan da ya yi burin rayuwa da Mimiensa a ciki, anan a ka kai ta domin tun da lokacin bikin nasu ya ƙaraso ya sallami y'an haya ya sake gyara gidan tsaf don sanya amaryarsa.

Bayan auren ba irin rawar kan da su Shamsiyya ba su nuna ba, baƙar magana da habaici kam ta sha su, a ranar da za a kai amarya gidan ya cika maƙil da y'an biki, Mimie ce ta zo wucewa cikin dakakkiyar shaddarta bowa sai ƙamshi ta ke zubawa.
Chapter 25 · 0% Book details