Sashe 23
A Sanadin Kama Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan kwana biyu ya na shirye-shiryen komawa Kano Innarmu ta kira shi zuwa gida, da ya je ne ta ke ce masa "Dama ba komi yassa nikkiraka ba, sai dan wata magana mai muhimmanci da muka son mu yi."
Gyara zamansa ya yi akan ledar ƙasa dake shimfiɗe a ɗakin ya na sauraronta.
Innarmu ta cigaba da cewa "Dama na ga kana yawan tahiye-tahiye ka na barin matarka can binni gashi babu kowa kusa da ita, sai su Shamsiyya, ga shi duk su na taron zani-zaka, ƙurciya na cin su, kuma nan an banni shiru, shina nicce me zai hana ka maida Matakka gidan ga?, in yasso gidanka na binni sai ka sa y'an haya, ka ga dannan ma ya hi mata sauƙin zuwa makaranta."
Gyara zama ya yi ya na cewa "Amma Innarmu, miye amfanin gidan da na ke da shi kenan, idan iyalina ba za ta zauna ciki ba?, Kuma nan na ga ya matse ba wani ɗaki da za ta iya zama aciki, ku kanku bai wadace ku ba."
Cikin tsawa Innarmu ta ce "Kama min bakinka, ba ga wancan tsohon ɗakin na babanku ba, tunda yarrasu ɗakin ya ke ruhe, sai a buɗe shi ka ƙara gyarawa kasa Matakka ciki."
Da mamaki a fuskarsa ya ɗago ya na cewa "Amma Innarmu ɗakin fa ƙarami ne kuma....."
Bai samu damar ƙarasawa ba saboda tsawar da ta daka masa ta ce "Ka ga ɗan nema mai shegiyar gardamar tciya? To tashi ka ban wuri hukunci na riga na yanke kahin ka wuce Kano za ta dawo nan umurni ne ba shawara ba, ya rage naka ka bi ko akasin haka."
Ta na gama faɗa ta miƙe ta shige uwar ɗakanta ta bar shi a gun sake da baki.
Shima miƙewa ya yi cike da damuwa ya bar ɗakin, a ransa ya ke mamakin me Innarmu ta ke nufi da hakan? Da farko ta tursasa shi zama birnin Kebbi, yanzu kuma ta na yunƙurin nuna ƙarfin ikonta ta hanyar tursasa shi zama gidan family abinda baya burge shi kwata-kwata.
Jiki a saɓule ya bar gidan.
®®®®®®®®®®®
Dubai
Bayan farkawar Sameer daga bugaggen barcin da ya yi sakamakon kwankwaɗar barasa, ko da ya farka ya dawo hayyacinsa, da ya tuna abinda ya faru kawai sai ya fashe da kukan nadama.
Ya yi kuka sosai tare da Allah wadai da halin su Wisam shi kam tarayya da su bata amfane sa da komai ba, sai jefa shi a halaka da ta yi.
Ya na cikin wannan halin ne Rajbir ya shigo ɗakin, ganin ya farka kuma ya na kuka ya saka ya buɗe shi, cikin harshen turanci ya ke cewa "A'ah! Mutumin ka farka ne? Me ya faru ka ke kuka?"
Cikin zafin rai da ɗaga murya Sameer ya mayar masa da amsa da yaren da su ke amfani da shi idan za su yi magana da juna wato turanci ya ce "Bansaniba, tambayar me kake bayan kuka jefa ni a cikin wannan halin na saɓawa mahaliccina?"
"Oh sam! Wannan fa ba damuwa ba ce shan barasa ai ba laifi bane.."
Dakatar dashi Sam ya yi ta hanyar ɗaga masa hannu ya ce "A addininka hakan ba laifi ba ne, amma a addinina wannan haramun ne, kun cuce ni, daga yanzu na daina yarda da ku, don Allah ku fita rayuwata ku koma masaukinku."
Ya na gama faɗa ya miƙe ya shige toilet ya bar Rajbir nan sake da baki.
Tun daga ranar ya fara share su, ba yanda bai yi su bar masa gidansa ba su ka ƙi, a haka suka lallaɓa shi har su ka shawo kansa ya kuma faɗawa tarkonsu a karo na biyu, tun daga lokacin ya afka cikin baƙin tarkonsu daga lokacin rayuwarsa ta zama ta mashaya,har ta kai da ya fara tunanin Mimie ya ke buɗe bakin kwalba ya tuttula, a haka rayuwarsa ta gurɓace duk silar soyayyar Mimie da ke cunkushe a zuciyarsa.
Har zuwa lokacin kuma ya kasa manta ta ko da ya sha giyar.
®®®®®®®®®®®
Ɓangaren Mommy kuwa ta samu nasarar saka maganin a cikin abincin Saheen ta hanyar Nafisa mai kula da gyaran ɗakinsa, da duk wani abu da ya shafe shi.
Hakan kuwa ta faru ne a lokacin da Mommy ta je gidan Alhaji Salman, kamar yanda ta saba, domin ta mayar da gidan tamkar gidansu.
A lokacin ne ta samu keɓewa da Nafisa su ka haɗa kai, ta bata maganin tare da kuɗi dubu goma ladan aikinta, ita kuwa saboda kwaɗayi ta karɓa ta tafi.
Mommy ba ta bar gidan ba sai da ta tabbatar an saka masa a abinci ya ci.
Tun daga ranar Saheen ya susuce yake jin kansa cikin wani irin yanayi shauƙin soyayya na fizgarsa, shi da kansa ya saka Direbansu ya kai shi gidan su Ruma ba tare da sanin kowa ba, ya je ya furta ya na son ta, da ya ga kamar bata so har kuka ya saka mata.
®®®®®®®®®®®
Bassam ya samu Mimie ya gaya mata hukuncin da mahaifiyarsa ta yanke, jikinta ya yi san yi laƙwas amma bata nuna ba, a haka ta nuna tsantsan farin cikinta, bayan kwana biyu su ka yi parking duk wani abu nasu, su ka koma gidan Innarmu da zama.
Washe garin ranar da suka tare gidan, Bassam ya juya zuwa Kano yayin da ya bar matarsa cikin damuwa da zullumi, haƙiƙa ta na hangowa kanta matsala a zaman gidan saboda yanda mutan gidan su ka fara juya mata baya...
Ga mai buƙata ya tuntuɓeni ta wannan number
08109634202
Follow me on wattpad @ummu inteesar
UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
DA KUMA
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page5️⃣5️⃣↪️5️⃣6️⃣
A haka ta cigaba da haƙuri halayyar mutan gidan da suke cusgunawa rayuwarta a duk kwana duniya,aciki kuwa har da su Sakina da suka manta da tarin Alkhairanta a gare su suka rufe ido suna mata tijara iri-iri.
Damuwa ta taru ta mata yawa ga shi ɗakin da ta tare ƙarami ne, daƙyar uwar ɗakan ta ɗauki gado da walldrop ɗin ta,sai madubi shima daƙyar ya samu mazauni a ɗakin, ɗan filin tsakar ɗakin da ya rage bai wuce inda mutum sai saka Sallaya ya yi Sallah ba, ga shi ba toilet a ciki.
Falon kuwa saboda matsatsinsa daƙyar kujeru ƙwaya uku suka zauna a ciki, sai ƙaramin showglass ɗinta, ɗan filin da ya rage ba zai ishi kwanciyar mutum biyu ba, dole aka bar sauran kayan nata acan wancan gidan da suka taso, haƙiƙa ta na cikin ƙunci sai a lokacin ne ta tuna da auren bada yardar iyayenta aka yi ba, shima wanda ya mata auren don ba yanda ya iya ne, amma ta san ba don ya na so ba.
Kusan ko da yaushe ta na waya da su Mama,yaya Farida da su yaya Kabir da matansu, Baba ne dai idan ta kira sai ya ga dama ya ke ɗagawa, nan ma da sun gaisa ya ke kashe wayar bai damu da tambayar lafiyarta ko yaya zaman su ita da mijin nata ba, don har zuwa lokacin ya na jin zafin abinda ta masa, ga wata mahaukaciyar kunyar Alhaji Salman da ya ke ji tun lokacin da abun ya faru, Mama ce ma ta ɗan sauko ba laifi tun da ita ta na tambayar lafiyarsu kuma ta sake su yi hira.
Haka ma ta na waya da su Daddy Mamie, da su yaya Saheen, watarana su na waya da Daddy ta ke tambayarsa "Daddy wai ni kuwa yaya Sameer fa? Shiru ake jinsa ya shige Dubai ya manta da y'ar ƙanwarsa." Ta ƙarashe da sigar zolaya.
Dariya Daddy ya yi ya ce "Cab! Wai kina nufin bai kira ya taya ki murnar aurenki ba? Na fa tura masa number na ce ya kira ku gaisa."
Shiru ta yi ta na tuna lokacin da suka yi waya da shi ta ƙarshe da irin maganganun da ta gasa masa a lokacin da idonta ya rufe da Soyayyar Bassam, "Tab! Ta ya ma zai kira ni bayan duk wannan abun da na masa?" Ta faɗa a ranta.
Tunawa da ta yi ashe ta na kan waya ne ya sa ts kirkiro murmushi ta ce "Ai kuwa Daddy bai kira ba, ina ga mantawa ya yi turon numbersa na kira shi." Ta faɗa cikin dakiya don ba ta so ya fahimci canjin yanayi daga gare ta.
"Ohk, bye sai anjima, ina da wani aikin da zan yi."
Daga haka ya katse wayar, ko ɗagawa bata yi daga gun ba, saƙonsa ya shigo wayarta.
Nan take ta danna masa kira jiki a saɓule, ta na ji wayar na ring amma bai ɗaga ba sai da ta kuma kira da ya ke can ƙasar har dare ya fara.
Shigowa lokacin ya na zaune a falonsa cikin yanayin damuwa da tunaninta, ko yaya ya rufe idonsa hotonta ya ke gani, lokacin bai jima da gama sallar isha'i ba, ya zauna agun cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa.
Ƙarar wayarsa da ke kusa da shi ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya shiga, ganin new number ne ya saka ya ƙi ɗagawa, sai ga wani kiran ya shigo, lura da ya yi cewa in bai ɗaga ba ba za'a daina kira ba, ga shi kuma number Nigeria ce da alama wani ne daga familynsa hakan ya saka ya ɗaga tare da karawa a kunne.
"Assalamu alaikum." Ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta mai rikita tunani.
Shi kuwa Sameer wata irin super ya yi ya miƙe tsaye tare da ƙara kallon sensor na wayar, tabbas ko ba'a faɗa masa ba, ya san Mimiensa ce ke magana domin ba zai taɓa manta muryarta ba, tunda kullum ya kan ji a mafarki.
Mai da wayar kan kunnensa ya yi ya na faɗar "Baby da gaske kece,Sweet sis, anyah! Ba mafarki na ke ba." Ya faɗa cikin wani rikitaccen yanayi.